13/12/2025
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun dakile wani hadin gwiwar hari da ‘yan ta’addar ISWAP s**a kai a wani sansanin soji na gaba (FOB) da ke Mairari a Jihar Borno, inda s**a kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan.
Rahotanni sun bayyana cewa harin ya faru ne a daren Jumma’a, 12 ga watan Disamba, ns shekarar 2025, zuwa safiyar Asabar, 13 ga watan Disamba, na shekarar 2025. Sojojin sun gano yunkurin ‘yan ta’addan na kutsawa cikin sansanin ne ta hanyar amfani da motoci biyu da aka dasa bama-bamai, amma aka gano su cikin gaggawa tare da lalata su kafin su kai ga cimma manufarsu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar, ya ce an dakile harin ne ta hanyar hadin gwiwar sojojin kasa da na sama, lamarin da ya yi matukar rage karfin ayyukan ISWAP a yankin.
Ya ce hotunan kyamarori da kuma binciken da aka gudanar a filin daga sun tabbatar da cewa da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun mutu, yayin da wasu s**a jikkata, inda ragowar s**a tsere dauke da gawarwaki da wadanda s**a jikkata.
Bayan dakile harin, sojojin Sashi na Uku na Operation Hadin Kai, tare da hadin gwiwar Rukunin Daukar Matakin Gaggawa, ‘yan sanda na musamman, da kuma rundunar Civilian Joint Task Force, sun gudanar da bincike mai zurfi a yankin.
A yayin aikin, an gano gawar ‘yan ta’adda da dama tare da kwace makamai da kayan aiki da s**a hada da bindigogi kirar AK-47, alburusai, gurneti, babura, kayan sadarwa, kayan yaki, kayayyakin jinya da sauran kayan da ke nuna shirin kai hare-hare na dogon lokaci.
Laftanar Kanal Sani Uba ya kara da cewa lalata motocin bama-baman biyu ya jawo barna a wasu sassan hanya, amma ba a samu kutsawa cikin sansanin soji ba, abin da ke nuna shiri da jajircewar sojojin.
Ya tabbatar da cewa sojoji na ci gaba da zagaye da sintiri mai tsanani a yankin domin hana duk wani sabon hari, tare da kwantar wa al’ummar yankin hankali kan ci gaba da tsaro.
A karshe, rundunar ta jaddada kudirinta na kakkabe dukkan ‘yan ta’adda da kuma dawo da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa Maso Gabas, tana mai cewa wannan nasara ta nuna kwarewa da jajircewar jami’an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.