30/09/2025
Gwamnatin taraiya za ta fara karbar haraji daga hannun mata masu zaman kansu
Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan manufofin kuɗi da gyaran dokokin haraji, ya ce kudaden da masu yin karuwanci ke samu za a rika cire musu haraji daga cikin da a ƙarƙashin sabon tsarin.
Oyedele ya yi wannan bayani ne a wani faifen bidiyo da ya wallafa a shafin X a jiya Litinin, inda ya kawo misalan hanyoyin samun kuɗin da ake sanya wa haraji.
Masanin harajin ya bayyana cewa sabbin dokokin ba sa bambanta tsakanin hanyar halal ko ta haram wajen samun kuɗi ba — abin da suke dubawa kawai shi ne ko kuɗin ya fito daga sayar da kaya ko kuma wani aiki da aka yi a ka biya.
“Ga wani misali mai tsanani… idan wani mutum yana yin dadiro, suna neman maza su kwanta da su. Ka sani wannan aiki ne, za a ɗauki haraji a kai,” in ji shi.
“Abu ɗaya game da dokar haraji, ba ta bambanta ko abin da kake yi halal ne ko ba halal ba, ma ba ta tambayarka hakan ba.
“Abin da take tambaya shi ne, shin kana samun kuɗi? Shin ka samu kuɗin ne ta hanyar aikin da kayi ko sayar da kaya? Idan haka ne, sai ka biya haraji.”
A gefe guda kuma, Oyedele ya ce kuɗaɗen kulawa da ake aika wa ‘yan uwa, abokai ko ma baƙi ba a ɗauke su a matsayin abin da ake ciro haraji akai, domin ana ɗaukar su kyauta ce.
“Ka samu wani adadin kuɗi sannan ka aika wa ɗan uwanka, ɗan’uwanka ko ma wani baƙo kuɗi don kulawa, ba kome ba ne. Idan kuɗin da kake aikawa kyauta ne, ba don sun yi maka wani aiki ba, to wannan kyauta ce. Muna kiran shi mu’amala ba ta musayar abu. Wannan ba abin da za a harhaɗa da haraji ba ne,” in ji Oyedele.