
01/07/2025
TSARABAR SAFIYA🌸
MANZON ALLAH💞{ﷺ}💞YACE: YIN AZUMIN RANAR ASHURA, NA YI TSAMMANIN WAJEN ALLAH YA GAFARTA ZUNUBAN SHEKARAN DA YA GABATA.🥀🌺
[QARIN HASKE]
WANNAN HADITH DIN YANA KARANTAR DA MU HALACCIN YIN AZUMIN RANAR ASHURA
YAYIN DA AKA SHIGA SABUWAR SHEKARAR
MUSULUNCI WATAU NA(WATAN MUHARRAM)
IDAN YA KAI KWANA TARA IZUWA GOMA GA WATAN DIN, DON YA KASANCE KOWANI RANA
DAGA CIKINSU 9 DA 10 ANA AZUMTAR SU.🌺
WANDA AKE YI RANAR TARA GA WATA SHI NE
AKE KIRA DA TASU'AH, WANDA AKE YI RANAR
GOMA GA WATA SHINE AKE KIRA DA ASHURA,
ASHURA SHI NE WANDA ANNABI YA LOKACIN YANA DA RAI, AMMAH TASU'AH YA AMBATA CEWA IDAN ALLAH YA KAI RAYUWARSA ZUWA
SHEKARA TA GABA ZAI AZUMCE TA, DOMIN
YA SABAMA YAHUDAWA DON SUN KASANCE SUNA AZUMTAR 9 GA (WATA MUHARRAM).🌺
SABODA HAKA YAKU ƳAN'UWANA MUSULMAI MUSAMMAN MAZA DA MATA MU KASANCE MUN AZUMCI WADANNAN RANAKUN DOMIN SAMUN DACEWA DA GAFARAR ALLAH {SWT}.
TARE DA CEWA BA WAJIBI BA NE HAKAN DIN
SAI DAI ITA SUNNAH CE MAI QARFI SOSAI.🌺
ALLAH YA DATAR DA MU DA FALALAR SA.🤲