
29/06/2025
GWAMNAN JIHAR BAUCHI SANATA BALA MUHAMMAD YA TALLAFAWA AL'UMMAR ƘARAMAR HUKUMAR DASS DA IFTILA'IN RUWA DA ISKA YA RABA SU DA MUJALLANSU DA NAIRA MILIYON 200.
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya kai ziyarar jaje wa Al'ummar yankin ƙaramar hukumar Dass da Iftila'in ruwa da iska ya rabasu da gidajensu a kwanakin baya.
Da yake jawabi a fadar Mai martaba Sarkin Dass Gwamna Bala Muhammad ya nuna Alhininsa bisa jarabawar da ta shafesu na rasa gidaje tare da Addu'ar Allah ya Mayar musu da abinda s**a rasa, sai ya bukaci da su mayar da Al'amarin zuwa ga Ubangiji.
Gwamnan yace lokacin da abin ya faru ya umurci hukumar bada Agajin gaggawa ta jiha ta yi kididdigar Asarar da akayi, sai ya bada tallafin kudi na Naira Miliyon 100, da kuma kayan aikin gini na Naira Miliyon 100 wanda in aka haɗa shine Naira Miliyon 200.
Sai yayi fatar za'a raba kuɗin da kayan Tallafin da aka samu bisa Adalci, yana mai cewa Masallatai da chochi chochi da Iftila'in ya shafa kuma Ma'aikatar kula da harkokin ƙananan hukumomi da Masarautu zasu gyara.
Cikin Jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Dass Hon Muhammad Abubakar Jibo ya bayyana irin matakai da ƙaramar hukumar ta dauka tun lokacin da Iftila'in ya faru, sai yayi godiya wa Gwamnan da Muƙarrabanshi bisa ziyarar jajen da kuma Tallafin da ya bayar.
Shima cikin jawabinsa Mai martaba Sarkin Dass Alh Usman Bilyaminu Othman yayi godiya ne bisa nuna damuwa da yake yi da duk wasu Al'amuran da s**a shafi ƙaramar hukumar, tare da bashi tabbacin cigaba da samun goyon bayansu a ko da yaushe.