17/08/2026
*Zaɓen Ƙananan Hukumomi Ya Gudana Cikin Nasara A Alkaleri - Gwamna Bala Da Shugabar BASIEC Sun Bayyana Gamsuwa*
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi, BASIEC, ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi 20 na jihar tare da kansilolinsu a yau Litinin, 17 ga watan Agusta, 2026.
A ƙaramar hukumar Alkaleri, zaɓen ya gudana yadda aka tsara. An fara kada kuri'a da misalin ƙarfe 8:30 na safe a rumfar zaɓe mai lamba 008 dake Yelwan Duguri, tare da sauran rumfunan zaɓe a fadin ƙaramar hukumar.
Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, tare da uwargidansa Hajiya Dr. A'isha Bala Mohammed, sun kaɗa kuri'arsu a rumfar su.
Bayan kaɗa kuri'ar, gwamnan ya bayyana gamsuwarsa da yadda zaɓen ke gudana cikin tsari da lumana. Ya gode wa Allah bisa damar da ya ba shi na cika alƙawarin da ya yi na gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar har sau uku, tare da bai wa shugabannin damar gudanar da ƙananan hukumominsu ba tare da tsangwama ba.
Shugabar Hukumar BASIEC, Hajiya Jummai Salamatu Abubakar, tare da tawagarta, sun zagaya wasu rumfunan zaɓe domin duba yadda ake gudanar da aikin.
Bayan zagayen, Hajiya Jummai ta ce ta gamsu da yadda al'umma s**a fito don kada kuri'arsu cikin nutsuwa.
_"Tun daga Bauchi har zuwa Yelwan Duguri na zagaya rumfunan zaɓe daban-daban. Na ga jama'a sun fito kuma ana gudanar da zaɓen bisa ka'ida,"_ in ji ta.
Wasu daga cikin masu kada kuri'a da muka tattauna da su sun bayyana gamsuwarsu da tsarin zaɓen. Sun yaba da cewa ma'aikatan zaɓe sun fito a kan lokaci kuma har yanzu ba a samu wata matsala ba.