27/08/2026
Shahararriyar ‘yar jarida kuma mai tasiri a kafafen sada zumunta, Hafsa Musa Abdullahi, wadda aka fi sani da Moofy, ta yi watsi da ra’ayin cewa akwai matan da namiji ba zai iya kai wa matsayin su ba. Ta ce abin da ya fi muhimmanci a gare ta shi ne tsafta da k**ala, ba dukiya ba.
A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Moofy ta yi magana kan mazan da ke cika aika mata saƙon soyayya a DM, suna cewa: “Ina son ki, amma kin fi karfina.”
Ta tambayi ma’anar hakan, tana cewa: “Idan na fi ƙarfinka, me ya sa ka aiko min da saƙo? Babu macen da ta fi ƙarfin kowane namiji — babu ko ɗaya.”
Moofy ta ce ta yi imani da Allah, kuma ba ta yarda cewa mace ta fi namiji daraja ba. A cewarta, aure yana bukatar fahimtar juna.
Ta ce: “Idan kana son mace, ka je gare ta ka ce mata ina sonki kuma ina son in aure ki. Idan mun fahimci juna, sai mu yi aure. Shi ke nan.”
Sai dai ta gargadi duk wani namijin da zai nemi aurenta cewa ba za ta lamunci ya zo mata cikin rashin tsafta ba ko yana wari saboda rashin wanka.
Ta bayyana cewa duk lokacin da wani namiji ya tura mata saƙon neman aure, abin farko da take yi shi ne duba bayanansa da hotunansa domin ganin yadda yake sanya kaya da kuma tsaftarsa.
Ta ce: “Ku manta da ko kayan suna da tsada ko arha — shin mutum yana da tsafta? Akwai wasu maza da za ka kalli hotonsu guda ɗaya kawai ka ce, ‘Ah, wannan mutumin mai tsafta ne. Wannan fa namiji ne na gaske.’”
Moofy ta ce wani lokaci tana fara farin ciki idan ta ga wani ya turo mata saƙon neman aure, tana tunanin watakila ta samu mijin aure, amma daga baya sai ta ji takaici.
Ta ce: “Kamar, kai! Da gaske kake? Kana son ka aure ni amma kana kallon kanka a haka, kana cikin rashin k**ala?”
Mai tasirin ta ce ba ta damu da yawan kuɗin namiji ba, sai dai ta damu da yadda yake gabatar da kansa da kuma ko zai iya kula da ita.
Ta ce: “Ka tabbatar kana da kyau, ɗan’uwa! Ka tabbatar kana da kyau! Ba na damu da kuɗinka sosai ba. Amma ka tabbatar kana da tsafta. Shin za ka iya kula da Moofy?”
Ta kuma ce za ta iya auren talaka, amma gidan da zai kai ta ya k**ata ya kasance ya fi gidan mahaifinta kyau.
Ta ce: “Na fahimci idan kana sona amma ba ka da dukiya. Amma kana da gidan da za ka kai Moofy wanda ya fi gidan mahaifinta? Dole ne ka tabbatar gidan da za ka kai ni ya fi wanda nake zaune a gidan mahaifina yanzu kyau kuma yana da kayan more rayuwa. Ka tabbatar kana da kyau, kana da ƙamshi mai daɗi, kuma kana da kyakkyawan gida.”
Moofy ta ƙarfafa maza da su nemi matan da suke so cikin mutunci, har da mashahuran mata.
Ta ce: “Idan ka ga macen da kake so, ka shiga DM ɗinta cikin mutunci. Idan ta zage ka, ka kare kanka. A cikin DM, babu wanda ya fi wani matsayi.”
Ta ƙara da cewa ita ba ta zagin mutane a DM, amma idan aka raina ta ko aka ci mutuncinta, za ta mayar da martani.
A cewarta, idan namiji ya bayyana mata soyayyarsa cikin gaskiya, za ta iya cewa cikin ladabi: “Yi haƙuri, ba kai ne irin mutumin da nake so ba; tuni ina da wanda nake ƙauna.” Ta ce wannan ya isa, ba tare da wata hayaniya ba.