13/08/2026
HON. IDRIS ISAH YUGUDA: ZABIN MUTANEN KIRKI DA MASU HANKALI NA MAZABAR TARAYYAR BAUCHI
Hon. Idris Isah Yuguda matashi ne mai ilimi, tarbiyya da hangen nesa, wanda ya taso cikin kyawawan dabi'u na hidimtawa al'umma, karamci da sadaukar da kai wajen inganta rayuwar jama'a.
Saboda haka ne ya kasance zabinmu na farko wajen wakiltar al'ummar Mazabar Tarayyar Bauchi.
Kamar yadda wasu mutane ke gado munanan halaye irin su rashin hakuri, rowa, rashin gaskiya da yaudara daga iyayensu ko magabatansu, haka shi kuwa Hon. Idris Isah Yuguda ya gaji kyawawan dabi'u, nagartaccen hali da kishin yi wa jama'a hidima daga mahaifinsa, tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Dr. Malam Isa Yuguda (Matawallen Bauchi).
Daga cikin kyawawan halaye da dabi'un da Allah Ya albarkace shi da su, kuma ya gada daga iyayensa, akwai:
✓ Girmama martabar ɗan Adam da mutunta kowa ba tare da nuna bambanci ba.
✓ Tausayi, karamci da son al'umma da zuciya ɗaya.
✓ Gaskiya, riƙon amana da bayyana gaskiya a dukkan mu'amalolinsa, ba tare da yaudara ko son zuciya ba.
✓ Shirye-shiryen taimakon masu buƙata cikin sauri ba tare da wahalar da su ko sanya musu sharuɗɗa marasa amfani ba.
✓ Girmama manya, tausaya wa marasa galihu da kula da raunana a cikin al'umma.
✓ Ƙwazo, neman ilimi, amfani da hikima da yin tunani mai zurfi kafin yanke hukunci.
✓ Adalci, gaskiya da jin ƙai wajen gudanar da al'amura, musamman idan akwai buƙatar fahimta da tausayi.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin dimbin kyawawan halaye da ɗabi'un da Hon. Idris Isah Yuguda yake da su, waɗanda ya gada tare da bunƙasa su a ƙarƙashin tarbiyyar mahaifinsa, Dr. Malam Isa Yuguda, Matawallen Bauchi.
Babu shakka, shugaba mai irin waɗannan kyawawan halaye ya cancanci a ba shi amanar jagoranci.
Idan aka ba Hon. Idris Isah Yuguda damar wakiltar al'ummar Mazabar Tarayyar Bauchi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, zai jagoranci mutane cikin adalci, gaskiya da kishin ci gaban al'umma, tare da samar da cigaba, haɗin kai da walwalar jama'a.
Muna addu'ar Allah Maɗaukakin S