Bala wunti social media team

Bala wunti social media team Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bala wunti social media team, Media/News Company, Wunti Street bauchi, Bauchi.

Allah Kara Maka Nasara a Duk Abun da kasa Gaba.
04/04/2026

Allah Kara Maka Nasara a Duk Abun da kasa Gaba.

Maison Al'ummah Da Alheri.Dakta Bala Maijama'a Wunti
28/03/2026

Maison Al'ummah Da Alheri.
Dakta Bala Maijama'a Wunti

BALA WUNTI 💪💪
25/03/2026

BALA WUNTI 💪💪

25/03/2026

Ba'a Bala Rago, Dan Mutanan Wunti Alheri Kayi Gado.
💪💪💪

Dakta Bala Wunti Sakon Bangajiya Hawan Sallah Dakta Bala Wunti na miƙa gaisuwar bangajiya na Hawan Sallah (Hawan Daushe)...
21/03/2026

Dakta Bala Wunti Sakon Bangajiya Hawan Sallah

Dakta Bala Wunti na miƙa gaisuwar bangajiya na Hawan Sallah (Hawan Daushe) ga Mai Martaba Sarkin Bauchi, tare da daukacin Hakimai da Sarakunan Gargajiya na masarautar Bauchi.

Allah Ya maimaita mana wannan rana cikin ƙoshin lafiya da zaman lafiya, Allah Ya ƙara ɗaukaka darajar Mai Martaba, Ya ƙara masa lafiya, hikima da tsawon rai domin ci gaba da jagorantar al’ummarsa cikin adalci da zaman lafiya.

Muna godiya da irin kulawa da jagoranci na gari da Mai Martaba da Hakimansa ke bai wa al’umma, da kuma Kara inganta al'adu gargajiya, Allah Ya saka da alheri, Ya bunƙasa masarautarmu, Ya ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin jama’a.

Allah Ya sa wannan Hawan Sallah ya kasance mai albarka, farin ciki da cigaba ga daukaka darajan al'adun gargajiya da masarautun gargajiya da al’ummar Bauchi.

✍🏽 Bala wunti social media team


Dakta Bala Maijama'a Wunti Yana Mika sakon Barka Da Sallah Yan uwa Musulmi.Dakta Bala Maijama'a Wunti yana mika sakon ta...
19/03/2026

Dakta Bala Maijama'a Wunti Yana Mika sakon Barka Da Sallah Yan uwa Musulmi.

Dakta Bala Maijama'a Wunti yana mika sakon taya murna wa al'ummar Musulmi na Jihar Bauchi, da fadin Najeriya, da ma duniya baki daya.

Dakta Bala Maijama'a Wunti yana Fatah alheri zuwaga al'umah na kammala watan Ramadan, yan uwa Musulmi mu kasance masu kyawawan dabi'un Musulinci da koyi da Annabi Rahama (S A W) da kuma yin amfani da rike darussan da aka koya a watan Ramadan.

Mu kasance masu sada zumunta zuwaga yan uwa namu abokan arziki namu, kuma mu kasance masu tausayi juna tawali'u, girmama juna, da kyautarawa juna.

Allah ya sake maimaita mana cikin koshin lafiya da zaman da koshin lafiya da yalwan arziki, iyaye namu da s**a rasu da yan uwa namu Allah yayi musu Rahama ameen.

Sakon Barka Da Sallah ne Daga Masoyinku Dakta Bala Maijama'a Wunti.

✍🏽 Bala wunti social media team


Jajircecen Matashi Mai Amana Alh Sirajo Caps.Ya kasance mai jajircewa da amana da isar da sakon Dr, Bala Maijama'a Wunti...
18/03/2026

Jajircecen Matashi Mai Amana Alh Sirajo Caps.

Ya kasance mai jajircewa da amana da isar da sakon Dr, Bala Maijama'a Wunti, da sakon amana Bala Wunti Alh, Rabi'u Maijama'a Wunti, cikin aminci da amana lungu da sako.

Alh, Sirajo Caps, yana kara jawowa Dakta Bala Maijama'a Wunti masoya bisa isar da sakon alheri lugu da sako wa al'ummah musamman mabukata.

Al'ummah sai godiya da sa albarka wa Dakta Bala Maijama'a Wunti da Alh, Rabiu Maijama'a Wunti da gidauniyar Wunti Al-khair Foundation, sukeyi bisa sakon alherin, rabon shinkafar da sako yazo garesu wanda Sirajo Caps ya isar musu da wannan sako.

Allah ya kara baka damar rike amana da isar da sako.

✍🏽 Bala wunti social media team


Wunti Al-Khair Foundation Ta Kammala Shirin Ramadan Daura na 2026.Wunti Al-Khair Foundation (WAKF) ta samu nasarar kamma...
15/03/2026

Wunti Al-Khair Foundation Ta Kammala Shirin Ramadan Daura na 2026.

Wunti Al-Khair Foundation (WAKF) ta samu nasarar kammala shirin Ramadan Daura na shekarar 2026, inda aka gudanar da babban bikin rufe shirin tare da halartar manyan baki masu daraja.

Daga cikin bakin da s**a halarta akwai wakilin Sarkin Bauchi, wato Ciroman Bauchi, Lifidin Bauchi, Sheikh Dan’azumi Musa Tafawa Balewa, da kuma Alaramma Sunusi Adamu.

A cikin jawabin bude taron, Abubakar Mohammed Yanmaza ya bayyana nasarar da aka samu a wannan shiri na addini da ilimi, inda ya sake jaddada manufar WAKF a matsayin kungiya mai himma wajen tallafawa al’umma.

Domin murnar kammala shirin Daura da kuma yabawa daliban da s**a nuna jajircewa, kowanne dalibi an ba shi.

Buhun shinkafa, Jakar makaranta ta HP (HP backpack),da kuma kayan Sallah, domin tunkarar bukukuwan Eid.

A madadin Daraktan Shirye-shirye (Director of Programs), Ango Mustapha, jami’in shari’a na WAKF ya gabatar da jawabin rufe taron, inda ya nuna matukar godiya ga dukkan mahalarta tare da sake jaddada kudurin gidauniyar na ci gaba da hidimtawa bil’adama ta hanyar ayyukan alheri masu tasiri.

Allah sakawa gidauniyar Wunti Al-khair Foundation da alheri.

✍🏽 Bala wunti social media team


Barkanku Da Shan Ruwa Mai Martaba Dakta, Rilwanu Sulaiman Adamu da Dakta, Bala Maijama'a Wunti.Allah ya kara muku lafiya...
10/03/2026

Barkanku Da Shan Ruwa Mai Martaba Dakta, Rilwanu Sulaiman Adamu da Dakta, Bala Maijama'a Wunti.

Allah ya kara muku lafiya da nisan kwana Allah kara kare mana daraja mutunci naku, Allah kara muku daukaka da kima da nasara.

Allah ya karbi ibada naku Allah ya karbi addu'o'inku Allah ya kara baku damar cigaba da taimakon talakawa ameen.

Daga: Bala wunti social media team


Barka da shan ruwa ga daukacin al'ummar musulmi Najeriya da Jihar Bauchi, Daga Dakta Bala Wunti.muna rokon Allah ya karb...
07/03/2026

Barka da shan ruwa ga daukacin al'ummar musulmi Najeriya da Jihar Bauchi, Daga Dakta Bala Wunti.

muna rokon Allah ya karbi ibadunmu, a wannan wata mai tsarki na Ramadan, muna rokon Allah ya sa wannan wata ya zama sanadin zaman lafiya hadin kai da ci gaba da tausayi ga juna a tsakaninmu.

Allah ya karbi azumi da addu'o'inmu ya sa mu dace da falalar Ramadan, Allah ya hada al'ummar musulmi da alheri dake cikinta, Allah ya gafarta mana zunubanmu Allah ya sa wannan wata ya zama sanadin da albarka a gare mu baki daya.

Wannan sakone Barka da Shan Ruwa daga masoyin al'ummah Dakta Baka Maijama'a Wunti.

✍🏽 Yusuf Sadeeq Wunti
Bala wunti social media team



#

Masu Hankali Kuyi Adalci wa Dr, Bala Wunti ga lisafi a kasa.👇🏼A cikin shekaru shida da s**a gabata, kasafin kuɗin tarayy...
06/03/2026

Masu Hankali Kuyi Adalci wa Dr, Bala Wunti ga lisafi a kasa.👇🏼

A cikin shekaru shida da s**a gabata, kasafin kuɗin tarayya na Najeriya ya kasance kamar haka: ₦7.44 tiriliyan a 2017, ₦9.12 tiriliyan a 2018, ₦8.92 tiriliyan a 2019, ₦10.59 tiriliyan a 2020, ₦7.99 tiriliyan a 2021, da ₦10.74 tiriliyan a 2022, sannan 2023 ya kai kusan ₦10.49 tiriliyan. Idan aka haɗa su gaba ɗaya, jimillar kasafin kuɗin na shekaru shida ya kai kusan ₦57.3 tiriliyan, da matsakaicin kusan ₦9.88 tiriliyan a kowace shekara.

Jimillar kuɗaɗen shiga na gwamnatin tarayya a wannan lokaci sun tashi daga ₦5.08 tiriliyan a 2017 zuwa ₦10.49 tiriliyan a 2023, yayin da kashe-kashe s**a tashi daga ₦7.44 tiriliyan zuwa ₦21.83 tiriliyan. Ko da an haɗa duk kuɗaɗen shiga da kashe-kashe tare, adadin bai kai ₦210 tiriliyan da ake ambata yanzu ba, don haka lissafi mai sauƙi kaɗai yana buƙatar a yi bayani.

A lokacin da Bala Wunti yake jagorantar National Petroleum Investment Management Services (NAPIMS), sashen da ke kula da saka hannun jari a harkar man fetur ta sama (upstream) da kuma kadarorin haɗin gwiwa na Najeriya, bayanai sun nuna cewa an samu riba kusan ₦9 tiriliyan. Abin lura shi ne cewa Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a (Senate Committee on Public Accounts) wanda yanzu yake ta tambayoyi, a baya ya riga ya amince da yadda sashen ya gudanar da aikinsa da kuma bayanan kuɗinsa a lokacin da yake jagoranci.

Saboda haka ne mutane da dama yanzu suke tambayar wata muhimmiyar tambaya da ta wuce lissafi kawai: Me ya sauya? Idan kwamitin a baya ya amince da yadda aka gudanar da harkokin kuɗi da bayanai a wannan lokaci da ake magana akai, to ‘yan Najeriya suna da haƙƙin sanin dalilin wannan sabon sauyin magana ko matsayi. Kulawa da ayyukan gwamnati dole ne ta kasance mai gaskiya, kuma gaskiya tana buƙatar daidaito.

Saboda haka, yana da adalci kwamitin ya fito ya yi cikakken bayani kan dalilin wannan zargi na yanzu, domin ‘yan Najeriya su fahimci ko matsalolin sun samo asali ne daga sabbin hujjoji, wasu sabbin hanyoyin lissafin kuɗi, ko kuma wani abu dabam. Abin da ya kamata a guje masa shi ne a bar mutane su yi zaton cewa ana amfani da zaman sauraron jama’a ne kawai domin jawo hankalin jama’a ko siyasa, ko kuma jefa inuwa kan wasu kafin a gama bincike.

Allah Kara kare mana maigidanmu Bala Wunti.

✍🏽
Bala wunti social media team


Gara a Sanka Akan Alheri da a Sanka Akan Rowa, Allah Ya Kara Tsare mana Mutunci naka Maigidanmu Dr, Bala Wunti.Bala wunt...
06/03/2026

Gara a Sanka Akan Alheri da a Sanka Akan Rowa, Allah Ya Kara Tsare mana Mutunci naka Maigidanmu Dr, Bala Wunti.

Bala wunti social media team

Address

Wunti Street Bauchi
Bauchi

Telephone

+2348168655949

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bala wunti social media team posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bala wunti social media team:

Shortcuts

Share