Online Sunnah Da'awah

Online Sunnah Da'awah ~ Domin YAƊA Karatuttukan Malaman Sunnah ~

  💥🔥@topfansnOnline Sunnah Da'awah
14/09/2024

💥🔥

@topfansnOnline Sunnah Da'awah

09/09/2024

"Kaji tsaron Allah, kaji tsaron mai tsaron Allah, kaji tsaron mai rokon Allah kuma kaji tsaron wanda zai barka da Allah".

@

 .Ka taɓa ganin liman ya shuka Tabar Wiwi kuma sabida Allah na son sa, ya fito masa da Shinkafa a Gonarsa?Ka taɓa ganin ...
25/08/2024

.

Ka taɓa ganin liman ya shuka Tabar Wiwi kuma sabida Allah na son sa, ya fito masa da Shinkafa a Gonarsa?

Ka taɓa ganin mutumin banza ya Shuka Shinkafa saboda Allah baya son sa, ya fito masa da Tabar Wiwi a Gonarsa?

A'a ba haka ba ne, abinda ka shuka shine zai fito maka a Gonarka, kuma shi zaka girba in ka shuka tabar Wiwi saboda Allah na son ka, ba zai fito ma da shinkafa ba, Wiwi ce zata fito.

Ubangiji ya Allah yasa mu dace da Ayyuka nagari.🙏

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Hafizahullah
✍️

@ ⊕OOnline Sunnah Da'awah

Idan kika auri namijin da ya ɗauke ki tamkar abokiyar sa, bazai boye miki komai nasa ba. Idan kika auri mijin da ya ɗauk...
24/08/2024

Idan kika auri namijin da ya ɗauke ki tamkar abokiyar sa, bazai boye miki komai nasa ba.

Idan kika auri mijin da ya ɗauke ki kamar kanwarsa. Ba zai so ya ga bacin ranki ba.

Idan kika auri namijin da ya ɗauke ki tamkar 'yar sa, xai yi hakuri da ke.

Idan kika auri namijin da ya dauke ki a matsayin mace, xai ta mutunta ki.

Idan kika auri namiji sabo da kudinsa, kinsan sauran ...........


Online Sunnah Da'awah

Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, FCIIS, FBCS, FNCS, meets the Governor of Yobe State, His Excellency Alhaj...
23/08/2024

Professor Isa Ali Ibrahim (Pantami), CON, PhD, FCIIS, FBCS, FNCS, meets the Governor of Yobe State, His Excellency Alhaji Mai Mala Buni, CON today

Cybersecurity Award!Professor Isa Ali Pantami Hafizahullah
21/08/2024

Cybersecurity Award!
Professor Isa Ali Pantami Hafizahullah

YADDA AKE YIN TAIMAMA DARASI NA (08). Ita dai taimama ana yinta ne da kasa mai tsarki, ko duwatsu, ko rairayi, da sauran...
20/08/2024

YADDA AKE YIN TAIMAMA DARASI NA (08).

Ita dai taimama ana yinta ne da kasa mai tsarki, ko duwatsu, ko rairayi, da sauransu.

*_Da farko idan mutum zai yi taimama zai yi niyyar halatta sallah. Daga abinda kari yake hanawa, sannan sai ya bugi kasa da tafukansa biyu idan wani abu daga turbaya ya makale sai ya kakkabe, sannan sai ya shafi fuskarsa gaba dayanta tun daga sama har kasa._*

*_Sannan sai ya sake bugar kasa karo na biyu ya sanya 'yan yatsun hannunsa na hagu a bayan 'yan yatsun hannunsan a dama. Sai ya taho yana shafawa a hankali har yazo guiwar hannu, sannan sai ya juyo da tafin hannunsa na hagun birbishin hannunsa na dama yana shafawa har yazo kan 'yan yatsu, sannan shima hannun hagu yai masa kamar yadda yai wan a dama._*

*_Idan ya akasta ya fara shafar hannun hagu sannan na dama ya isar masa, matukar dai ya game ko'ina da shafar._*

•✍️
Mohammed Tasi'u Abubakar



Online Sunnah Da'awah

BAN BANCIN ILIMI DA KUDI.Ilimi shi yake tsaronka, kudi kuma kai kake tsaron su, ilimi yana tsareka daga fadawa cikin hal...
19/08/2024

BAN BANCIN ILIMI DA KUDI.

Ilimi shi yake tsaronka, kudi kuma kai kake tsaron su, ilimi yana tsareka daga fadawa cikin halaka, ilmi yakan mayar da kai sarki, kudi kuma su mayar da kai bawa.

Mallam Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum
~ H a f i z a h u l l a h.



Online Sunnah Da'awah

18/08/2024

Professor Isa Ali Pantami Hafizahullah

HUKUNCIN TAIMAMA DARASI NA (07)...Allah madaukakin Sarki yana cewa:"وإن كنتم جنبا أو على سفر ولم تجدوا ماءا فتيمموا صعيد...
18/08/2024

HUKUNCIN TAIMAMA DARASI NA (07)...
Allah madaukakin Sarki yana cewa:
"وإن كنتم جنبا أو على سفر ولم تجدوا ماءا فتيمموا صعيدا طيبا وامسحوا بوجوهكم وأيديكم" الآية. (المائدة: 6).
“Wa’in kuntum junuban au ala safarin walam tajiduu maa’an fatayammamu sa’idan dayyiban wamsahuu biwujuuhikum wa’aydeekum…” (Al-Ma’ida:6)
Ma'ana: Idan kun kasance a halin Janaba, ko kuna halin tafiya baku sami ruwa ba, to kuyi taimama da kasa mai tsarki ku shafi fuskokinku da hannayenku". (Surar Ma'ida Aya:6).
Taimama tana wajaba saboda rashin ruwa a halin tafiya. Haka ma tana wajaba idan ya zama akwai ruwan amma ba za’a iya tabashi ba saboda rashin lafiya.

Idan matafiyi ya tabbatar zai sami ruwa a gaba, to ya jinkirta sallah zuwa karshen lokaci, amma idan ya sakankance ba zai samu ruwa ba, to yai taimamarsa tun a farkon lokacin yai sallah, wanda kuma yake zaton zai samu ko ba zai samu ba, to yayi taimamar a tsakiyar lokaci.

Wanda yai taimama a cikin wadanda za'a ambata idan ya sami ruwa to ga hukuncinsa kamar haka:

1- Mara lafiya wanda bai sami wanda zai debo masa ruwa ba, har yai taimama yai sallah, idan ya sami ruwa lokaci bai fitaba, an so yayi alwala ya sake sallah.

2- Mai tsoron zakoki = Idan yaje inda ruwan yake akwai namun daji ko 'yan fashi to daga baya sai wannan tsoron ya kau. Idan ya je ya debi ruwan kuma lokaci bai fitaba, shima an so yayi alwala yai sallah.

3- Matafiyi, wanda yake zaton ba zai sami ruwa a farkon lokaci ba, sai a karshe shima idan yai taimamar kuma sai ya samu a tsakiyar lokaci anso ya sake.

Ba'a sallar farilla biyu da taimama guda daya, sai dai kowace sallar farilla ai mata taimamarta daban.

•✍️
Mohammed Tasi'u Abubakar



Online Sunnah Da'awah

Address

Bauchi

Telephone

+2348169202921

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Online Sunnah Da'awah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Online Sunnah Da'awah:

Share