Dariqah TV

Dariqah TV Domin samun karatun malaman addini Musamman Abunda Yashafi Addini da Rayuwa ku kasance tare damu Ku kasance da kafar Darika TV
(1)

Domin samun karatun malaman Darika Tafsir, wa'azozi tarihin Darikun sufaye.

11/10/2026

Malam Abduljabbar bai zagi Annabi Muhammad ﷺ ba da wannan nake bauta wa Allah kuma babu wadda ya isa ya hanabi fada.

10/10/2026

Yakamata duk wani limami ya zama yanada sana'a

~ Imam Sheikh Muhammad Nasir Adam.

10/10/2026

Allahu Akbar jiya ancire tutar maulidin Annabi Muhammadu a garin Kano na Shekarar 2026.

Allah ka Mai maita mana Albarkan Annabi Muhammadu ﷺ.




゚

LABARI CIKIN HOTUNA:An gudanar da Muzaharar Mauludin Annabi Muhammadu ﷺ Ya Gudana A Karamar Hukumar Kudan Dake Jahar Kad...
10/10/2026

LABARI CIKIN HOTUNA:

An gudanar da Muzaharar Mauludin Annabi Muhammadu ﷺ Ya Gudana A Karamar Hukumar Kudan Dake Jahar Kaduna .

Muzaharar wanda yan'uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) na Da'irar Kudan s**a gabatar yau Asabar 28 ga watan Rabi'ul Thani, wanda ya yi daidai da 10/10/2026 ta gudana cikin salo da tsari.

An fara Muzaharar ne da Misalin ƙarfe 10 na safe inda ta shafe fiye da awanni uku tana tafiya cikin tsari da natsuwa. masu gabatar da wannan muzaharar wanda s**a haɗa maza da mata, yara da manya, sun fito cikin ado na musamman da bayyana irin farin cikin da suke yi da wannan muhimmiyar rana da suke biki domin samuwar ma'aikin Allah Annabin Rahama Muhammad ɗan Sayyadi Abdullahi da Sayyida Aminatu. Daga kasa wasu daga cikin kyawawan hotunan yanda Muzaharar ta gudana ne.

©️ Media Forum — Zaria Team
28th Rabi'ul Thani 1448
10th October 2026

10/10/2026

Kidsar wata Mata da wani Mutum tare da Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

A yammacin ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, an sauke tutar Maulidin Annabi Muhammad ﷺ a Cibiyar Qadiriyya Kabara.An ɗaga...
10/10/2026

A yammacin ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, an sauke tutar Maulidin Annabi Muhammad ﷺ a Cibiyar Qadiriyya Kabara.

An ɗaga wannan tuta ne a ranar 1 ga watan Rabi’ul Awwal, shekara ta 1448 bayan Hijira (2026), sannan aka sauke ta a yau, 29 ga watan Rabi’ul Thani, shekara ta 1448 bayan Hijira (9 ga Oktoba, 2026).

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya azurta mu da albarkoki ta hanyar ƙaunataccen jagoranmu, Annabi Muhammad ﷺ, kuma Ya ba mu damar sake ganin wannan gagarumin al’amari a wata shekara mai zuwa.

Albarkan Annabi Muhammad ﷺ.

10/10/2026

Shi Aljanna inda yafi komai dadi ba tsufa ba mutuwa🥰.





゚

ALLAHU AKBAR 😭.Yanda aka gudanar da sallar jana'izar marigayi Imam khalifa Buhari Dan-iya Lafiya Shugaban ZAKIRAI na Nig...
10/10/2026

ALLAHU AKBAR 😭.

Yanda aka gudanar da sallar jana'izar marigayi Imam khalifa Buhari Dan-iya Lafiya
Shugaban ZAKIRAI na Nigeria.😭😭😭

Wanda aka gudanar a Fadar mai martaba Sarkin Lafian bare bari, a jihar Nasarawa.

Muna addu'a Allah ya jikashi da rahama.

10/10/2026

Bincike na na Degree da masters Akan Diwanin Shehu Ibrahim Inyass R.T.A yana daga abun ke saka ni farin ciki.
✍️ Syd Ahmad Mukaddam

Juma'at kareem!!!عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: إِنَّ الْعَبْدَ لَيَتَك...
09/10/2026

Juma'at kareem!!!

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ، عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: إِنَّ الْعَبْدَ لَيَتَكَلَّمُ بِالْكَلِمَةِ مِنْ رِضْوَانِ اللَّهِ، لَا يُلْقِي لَهَا بَالًا، يَرْفَعُهُ اللَّهُ بِهَا دَرَجَاتٍ، وَإِنَّ الْعَبْدَ لَيَتَكَلَّمُ بِالْكَلِمَةِ مِنْ سَخَطِ اللَّهِ، لَا يُلْقِي لَهَا بَالًا، يَهْوِي بِهَا فِي جَهَنَّم.

Manson Allah SAW yace: "Lallai bawa yana iya furta wata kalma wadda Allah ya yarda da ita, alhali shi bai damu da ita ba, sai Allah Ya ɗaukaka shi sabida ita zuwa wasu darajoji. Haka kuma, lallai bawa yana iya furta wata kalma wadda Allah yake fushi da ita, alhali bai damu da ita ba, sai ta jefa shi cikin Jahannama".

Yaku yan uwa muyi kokari mukiyaye Harsunanmu

Address

Ahamadu Bello Way Wunti Street Bauchi
Bauchi
740001

Telephone

+2348160886230

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dariqah TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dariqah TV:

Shortcuts

Share