24/07/2025
Kungiyar Wajamu Rasulillahi Ta Ziyarci Shugaban ta na jihar Bauchi, Malam Shehu Mai Ashafa
BAUCHI, 24 Yuli 2025 – A ci gaba da rangadin tuntuba da ƙarfafa zumunci, kungiyar Waiamu Rasulillahi La-Yata Sha’asu Islamic Organization, ta kai ziyara ta musamman ga shugaban ƙungiyar reshen Jihar Bauchi, Malam Shehu Mai Ashafa.
Tawagar ta kasa ta ƙungiyar, wadda ke gudanar da ziyarce-ziyarcen shugabanninta a yankuna daban-daban na Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, ta isa Bauchi ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025, bayan fara rangadin ne tun Asabar, 19 ga Yuli, 2025.
Malam Shehu Mai Ashafa ya karɓi tawagar da hannu bibbiyu a masallacinsa da ke Unguwar Mukaddas, inda yake koyar da addini da ƙaunar Manzon Allah (SAW).
Ziyarar ta kasance ɓangare ne na shirin ziyarar manyan shugabannin ƙungiyar a biranen:
Nguru
Maiduguri
Potiskum
Gombe
Bauchi
Birnin Kudu
Kano
A cewar jagororin tawagar, tafiyar na da burin ƙarfafa haɗin kai da sada zumunta a tsakanin mambobin ƙungiyar, da kuma ci gaba da yada saƙon Manzon Allah (SAW) cikin lumana, biyayya da tausayi.
Malam Shehu ya bayyana godiyarsa da jin daɗin wannan ziyara, yana mai cewa hakan na ƙara karfin guiwar cigaba da aikace-aikacen ƙungiyar a matakin jiha da ƙasa baki ɗaya.
Kungiyar Waiamu Rasulillahi La-Yata Sha’asu na daga cikin ƙungiyoyin da ke fafutukar gina tarbiyyar al’umma ta hanyar koyar da kaunar Annabi Muhammad (SAW), da ɗorewar al’umma a kan kyawawan dabi’u da zaman lafiya.