12/10/2025
"Dr Bala Wunti Ka Amsa Kiran Mu Kayi Takarar Gwamnan Bauchi" - Sako Daga Karamar Hukumar Ningi
An gudanar da gagarumin taro a garin Ningi domin kiran Dr. Bala Wunti, da ya tsaya takarar Gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
Taron, wanda Ko’odinetan Bala Wunti na ƙaramar hukumar Alhaji Bala Somebody, ya shirya ya gudana ne a M.U.K dake Ningi ranar Juma’a.
Alh Bala ya bayyana cewa manufar taron shine haɗa kai da jawo hankalin al’umma domin su mara baya ga Dr. Bala Wunti wajen samun nasarar tsayawa takarar gwamna a 2027.
A jawabinsa, Sa’in Tiffi, ɗaya daga cikin jagororin tafiyar Bala Wunti a ƙaramar hukumar Ningi, ya yi karin bayani kan dalilan da s**a sa s**a kuduri aniyar ganin an samu shugaba nagari da kwarewa a tafiyar da al’amuran jihar.
Haka zalika, wakilan Dr. Bala Wunti daga fadar jiha sun halarci taron, inda Alhaji Abba M. Inuwa ya gabatar da jawabi a madadin tawagar, yana mai yabawa da yadda jama’ar Ningi ke nuna cikakken goyon baya da kauna ga Dr. Bala Wunti.
Taron ya sami halartar bangarori daban-daban na al’umma, ciki har da kungiyoyin matasa da na mata.
Abubakar M. Abubakar ya gabatar da jawabi a madadin matasa, inda ya jaddada cewa matasa na da rawar gani wajen tabbatar da nasarar wannan tafiya.
Haka kuma, Hajiya Zulai Mamuda daga bangaren mata ta yi jawabi, tana mai cewa mata za su kasance a sahun gaba wajen tallafawa wannan tafiya mai albarka.
Manufar taron gaba ɗaya ita ce tabbatar da cewa ƙaramar hukumar Ningi ta tsaya tsayin daka wajen bayar da gudunmawa ga jam’iyyar APC, tare da tabbatar da turbar shugabanci mai inganci da dorewa a jihar Bauchi.
Oga Habu Umar Umb Bauchi Bala Wunti Youths Movement Bauchi