26/07/2025
TAKARDAR GAYYATA A TAQAICE
Domin Gudanar da DAURAR ILIMI GA DALIBAI A LOKACIN HUTUN MAKRANTAR BOKO
Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh,
Muna miƙa gaisuwar addini tare da fatan alheri gare ku shugabannin makarantu, malamai da duk masu ruwa da tsaki a fagen ilimin addinin Musulunci.
A cikin al’adar da aka saba a kowane lokaci na hutu, muna shirya Daurar Ilimi ga dalibai domin tsare su da kula da tarbiyyarsu daga barna da shagala da duniyar zamani. Wannan Daurah zata ƙunshi karatun Qur'ani, Hadisi, Fiqhu, Tarbiyyah da Hanyoyin Kyautata Halaye.
Ga bayanan Daurar kamar haka:
📍 Wurin Daurar:
IBADURRAHMAN LITTAHFIZIL QUR'AN WADDARASATUL ISLAMIYYA,
Unguwan Kur Railway, Bauchi.
📆 Ranar Farawa:
Litinin, 11 ga watan August, 2025
🕘 Lokaci:
Daga 9:00 AM zuwa 11:00 AM kowacce rana daga Litinin zuwa Alhamis, na tsawon sati biyu (2).
Manufa:
Don karfafa gina tarbiyyar dalibai da kuma kula da lafuzzan addini da halayensu a lokacin da ba sa zuwa makarantar boko.
Muna gayyatar ku da ku kasance cikin wannan aiki na alheri da hadin gwiwa domin samun cikar nasara. Allah ya saka da alheri, ya kuma saka da lada.
Wassalam.
Masu Shirya Daurah:
IMAM IBRAHIM IDRIS BAUCHI FOUNDATION
Lambar Tuntuɓa: 08061636305