21/09/2025
Jami’ar European American University ta karyata wani bikin murnar kammala karatu da aka ce an gudanar da shi a NICON Luxury Hotel, Abuja, inda aka yi ikirarin ba wa wasu fitattun mutane shaidar girmamawa na PhD ciki har da mawaki Dauda Kahutu Rarara.
A wata sanarwa da shugaban jami’ar, John Kersey, ya fitar, ya bayyana cewa ba su amince da wannan taro ba, kuma an shirya shi ne ta hanyar yaudara, ba tare da sanin jami’ar ko yardarta ba.
“Mutanen da s**a shirya wannan biki sun yi amfani da sunan jami’ar ne wajen yaudarar jama’a da kuma karɓar kuɗi ba tare da wata hurumi daga gare mu ba,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa jami’ar ba ta taba ba da shaidar PhD ko girmamawa ga Dauda Kahutu Rarara, Alhaji Ahmed Saleh jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa da Tarela Boroh ba. Haka zalika, duk masu digiri daga jami’ar suna cikin jerin Register of Graduates a shafin intanet na jami’ar, kuma waɗannan ba su cikin sahihan daliban da aka girmama.
Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa Musari Audu Isyaku, wanda aka ce shi ne wakilin Arewa maso Yamma, ba shi da wani izini daga gare ta. Hakazalika, Idris Aliyu, wanda aka ce ya wakilci shugaban jami’ar a wajen bikin, ba shi da wani matsayi a hukumar jami’ar, kuma ba shi da ikon wakiltar shugabanta. An tabbatar cewa a shekarar 2024 aka ba shi mukamin Fellowship da matsayin farfesa a fannin Financial Management, amma yanzu haka an soke mukamin saboda hannunsa cikin wannan zamba.
Jami’ar ta kuma tunatar da cewa a watan Afrilu na wannan shekara ta fitar da sanarwa game da tsohuwar shugabar jami’ar, Dr. Mrs. Josephine Egbuta, wadda aka kora daga mukaminta saboda laifuka, tana mai cewa yanzu haka ba ta da ikon wakiltar jami’ar. Shugaban jami’ar na yanzu shi ne Professor Luca Scotto di Tella de’ Douglas di Castel di Ripa.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’ar ba ta da alaka da Dominica ko Panama k**ar yadda aka wallafa, inda ta jaddada cewa yanzu haka tana aiki ne a matsayin gidauniyar ilimi mai zaman kanta a Faransa, tare da riƙe Royal Charter daga Bunyoro-Kitara Kingdom a Uganda.
Jami’ar ta ce za ta shigar da ƙara a gaban hukumomin Najeriya domin dakile irin wannan yaudara ta buga takardun jami’a na ƙarya, tare da tabbatar da cewa wadanda ke da hannu za su fuskanci hukunci na doka.