19/01/2025
Hajjin bana: IHR ta yaba wa NAHCON bisa canja kamfanin hidimar alhazai a Saudiyya
Kungiya mai zaman kan ta da ke kawo rahotanni kan Hajji da Umrah, IHR, ya yabawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON bisa zabar sabon kamfanin hidimar alhazai a Saudi Arebiya domin gudanar da aikin hajjin 2025.
IHR ta ce matakin zai haifar da gasa mai kyau a tsakanin kamfanonin yi wa alhazai hidima da su rika yin aiyuka masu inganci ga mahajjatan Najeriya.
IHR a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kodinetan ts na ƙasa, Malam Ibrahim Muhammed a birnin Makkah na kasar Saudiyya, ta ce neman inganta aikin Hajji ya kasance babban kalubale ga alhazan Najeriya sakamakon gazawar da aka yi na samar da gamsassun ayyuka.
Saboda haka kungiyar ta yabawa NAHCON boss wannan mataki, inda ta ce zai samar da ingattun hidimomi ga alhazan Nijeriya a Saudiya yayin aikin Hajji.