04/10/2026
Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Ƙaddamar da Motocin CNG 30 da Keke Napep Mai Amfani da Lantarki 200 a Katsina
Mataimakin Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Kashim Shettima, GCON, a ranar Lahadi ya ƙaddamar da motocin sufuri masu amfani da fasahar CNG guda 30 da kekuna masu kafa uku kuma masu amfani da wutar lantarki guda 200 a Jihar Katsina, a wani mataki na Gwamnatin Jihar na zamanantar da harkokin sufuri, inganta zirga-zirga da kuma saukakawa mutanen jihar Katsina.
Manyan Motocin guda 30, waɗanda ke amfani da wutar lantarki, dizal da kuma iskar Compressed Natural Gas (CNG), za su yi aiki a Katsina, Daura da Funtua, tare da babbar tashar sufuri da cibiyar gyaran motoci a Katsina da ƙananan tashoshi a Daura da Funtua. Haka kuma, Gwamnatin Jihar na samar da tashoshin motoci na zamani guda 40, waɗanda ke ɗauke da internet da na’urorin solar inverter domin ƙara wa fasinjoji sauƙi da jin daɗi.
Kekunan hawa masu amfani da wutar lantarki guda 200 da aka ƙaddamar, wani ɓangare ne na babban shirin Gwamnatin Jihar na samar da kekunan Keke guda 500. Shirin zai samar da damammaki ga masu sana’ar sufuri, matasa, masu gyaran ababen hawa da sauran ‘yan kasuwa a fannin sufuri na zamani.
Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana shirin a matsayin “Daga Sauyin Makamashi zuwa Sauyin Tattalin Arziki”, yana mai cewa manufar ba wai kawai sauya fasahar motocin sufuri ba ce, illa gina ingantaccen tsarin sufuri na zamani da zai tallafa wa harkokin tattalin arziki, samar da ayyukan yi da bunƙasa sana’o’i.
Gwamna Radda ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, bisa goyon bayan da suke bai wa Jihar Katsina, tare da sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa, ƙarƙashin manufar Building Your Future Agenda, na samar da ababen more rayuwa da ayyukan gwamnati na zamani waɗanda za su inganta rayuwar al’umma.
MS Ingawa
SSA, Media & Strategy
Katsina State Government
October 4, 2026.