Radio and TV LYB

Radio and TV LYB Radio LYB na Watsa Shirye-Shirye Akan https://radiolyb.com.ng/ na Tsawon Sa’o’i 24 a Duk Rana.

Sarkin Kano, Sanusi ll, ya ce cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafita ga ƙasar duba da yanayin ...
15/09/2025

Sarkin Kano, Sanusi ll, ya ce cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafita ga ƙasar duba da yanayin ƙaƙaniƙayi da ta samu kanta na taɓarɓarewar tattalin arziki.

Sai dai basaraken ya nuna damuwa kan yawan ciwo bashi da gwamnatin ke yi da kuma yadda take facaka da kuɗaɗen, wanda ya yi gargaɗin cewa hakan na iya jefa Nijeriya cikin matsalar tattalin arziƙi na tsawon shekaru.

15/09/2025
KAI TSAYE DAGA WAJEN SALLAN JANA'IZAR LIMAMIN KOBI UBANGIJI ALLAH YAJI KANSA YAYI MASA RAHAMA AMEEN
14/09/2025

KAI TSAYE DAGA WAJEN SALLAN JANA'IZAR LIMAMIN KOBI UBANGIJI ALLAH YAJI KANSA YAYI MASA RAHAMA AMEEN

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa cire t...
14/09/2025

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi a matsayin “gagarumin aikin kishin ƙasa,” ba tare da tunani irin na ɗan siyasa da yake tunanin zaɓe na gaba ba.

Gbajabiamila ya jaddada cewa tun daga ranar farko da Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta guje wa manyan sauye-sauye masu wahala da za su kawo ci gaba a ƙasa ba.

13/09/2025

Hon. Adamu Dako..........................

Shugaban Rundunar Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yi kira kan ci gaba da yin haɗin gwiwa a tsakani...
13/09/2025

Shugaban Rundunar Sojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Bala Abubakar, ya yi kira kan ci gaba da yin haɗin gwiwa a tsakanin hukumomin tsaron Nijeriya, yana mai jaddada cewa; tsaron ƙasa aiki ne na haɗin gwiwa da ke buƙatar haɗin kai.

Air Marshal Abubakar, ya shaida wa shugabanni da wakilan ƴan ’uwan jami’an tsaro da s**a halarci taron cewa; halartar tasu na da matuƙar muhimmanci, ”sanin kowa ne cewa; tsaron ƙasa aiki ne na kowa da kowa da ke buƙatar haɗin gwiwa.” Ya bayyana cewa, barazanar da ke kunno kai da s**a haɗa da ta’addanci, satar mutane da sauran laifukan da s**a shafi intanet, “abubuwa ne da s**a ci garo da shari’a”, don haka; akwai buƙatar haɗin kan ɓangarorin tsaro daban-daban.

Da yake nuna irin muhimmiyar rawar da ɓangaren sojin sama ke takawa, ya bayyana su a matsayin masu bin dokoki da kula da horo fannin nasu, waɗanda kuma ayyukansu ke da matuƙar nuhimmanci tare da kuma da samun nasarori.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Shugaban Hukumar Air Vice Marshal (AVM) Idi Sani, ya jaddada muhimmancin rawar da shugaban yake takawa wajen tabbatar da ɗa’a, ladabtarwa, aiwatar da dokoki da kuma samar da ayyuka ga hukumar sojin saman.

A nasa jawabin Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, wanda sakataren gwamnatin jihar Architect Samuel Jatau, ya wakilce shi; ya yaba wa rundunar sojojin saman Nijeriya da sauran hukumomin tsaro a jihar, bisa namijin ƙoƙarin da suke yin a wanzar da zaman lafiya a faɗin jihar ta Filato.

A nasa jawabin, Air Marshal, AVM JA Usman, ya yaba wa hafsan hafsoshin sojin saman bisa jajircewarsa da kuma sadaukarwa wajen ciyar da harkokin sojin sama da sauran ma’aikata gaba. ya yi nuni da cewa, taron ya sabunta ƙudirin hukumar na yin amfani da fasahar zamani, ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙara ƙarfin gudanar da ayyuka yadda ya kamata.

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga rana...
13/09/2025

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga ranar Litinin, 15 ga Satumba.Kazalika, kamfanin ya rage farashin man fetur ga masu gidajen mai zuwa N820 kan lita ɗaya, inda gidajen man jihohin Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya za su sayar da shi kan N841.Sai kuma Abuja da Rivers da Delta da Edo da Kwara za su sayar kan N851. Ta ce daga baya shirin zai karaɗe sauran jihohin ƙasar.Kamfanin ya ce an yi wannan tsarin ne domin rage farashin rarraba man da kuma sauƙaƙa farashin a tashoshi, da kuma rage matsin tattalin arziki.Haka nan, ana sa ran tsarin zai amfani ƙananan masana’antu sama da miliyan 42 ta hanyar rage farashin makamashi da inganta ribarsu, in ji matatar.

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta jaddada cikakken goyon bayanta na samar da ƴan sandan jihohi a wani ɓangare n...
12/09/2025

Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta jaddada cikakken goyon bayanta na samar da ƴan sandan jihohi a wani ɓangare na ƙoƙarin magance matsalar rashin tsaro a yankin da ma faɗin ƙasar baki ɗaya. Wannan tabbaci ya zo ne bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sabunta ƙudirinsa na tabbatar da samar da rundunar ƴan sandan jihohi.
Isma’ila Uba Misilli, babban daraktan hulɗa da manema labarai na Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa tuni gwamnonin s**a ɗauki matsaya kan wannan al’amari. A cewarsa, kafa ƴan sandan jihohi na daga cikin matakan sake fasalin tsarin tsaro na Nijeriya domin magance matsalolin da s**a addabi al’umma.
Ƙungiyoyin al’adun gargajiya guda uku na Arewa da Kudancin Nijeriya sun buƙaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta ɗaukar matakan da s**a dace wajen samar da rundunar. Babbar ƙungiyar Arewa, wato Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta ce wajibi ne samar da ƴan sandan jihohi ya bi dukkannin sharuddan da kundin tsarin mulki ya tanada, tare da gargadin cewa kada gwamnonin su yi amfani da su wajen yaƙi da abokan adawa.
Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na ACF, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya bayyana cewa har yanzu ƙungiyar ba ta ɗauki matsaya a hukumance ba, amma wajibi ne a bi dukkan matakan da doka ta shimfiɗa. Ya nuna damuwa kan yiwuwar amfani da rundunar wajen muzgunawa abokan adawa da masu s**a.

A nasa ɓangaren, tsohon Sanata daga Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa masu rajin kafa ƴan sandan jihohi dole ne su fahimci ƙalubalen da ke gaba. A cewarsa, “Waɗanda suke so tare da fatan ganin an kafa ƴan sandan jihohi, suke kuma s**ar ƴan sandan tarayya, ina yi muku fatan abin da kuke yi wa kanku fata. Yayin da shugaban ƙasa a ƙarshe ya amince da ƴan sandan jihohi, za ku gane banbanci tsakanin rundunar tarayya da ta jihohi.”

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da s**a shafi auren jinsi da dangoginsa.Gwamn...
12/09/2025

Gwamnatin jihar Kano ta buƙaci majalisar dokokin jihar ta haramta abubuwan da s**a shafi auren jinsi da dangoginsa.

Gwamnatin ta ɗauki matakin ne bayan taron majalisar zartaswar jihar da aka gudanar ranar Laraba.

Cikin ƙunshin ƙudurorin da majalisar zartaswar ta aike wa majalisar dokokin - wanda kwamishinan ƙasa da safiyo, Abduljabbar Mohammed Umar ya sanya wa hannu, ta buƙaci da majalisar ta amince da dokar da za ta haramta duk wani abu da ya shafi auren jinsi a a faɗin jihar.

Jihar Kano da ke arewacin Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke amfani da shari'ar addinin musulunci - wadda a dokokinta s**a haramta auren jinsi, tare da tanadar hukunci mai tsanani ga wanda ya aikata.

Al’umar K**i ta yi barazanar ƙauracewa zaɓen 2027Al’umar K**i da ke cikin Karamar Hukumar Bauchi ta bayyana barazanar ƙa...
12/09/2025

Al’umar K**i ta yi barazanar ƙauracewa zaɓen 2027

Al’umar K**i da ke cikin Karamar Hukumar Bauchi ta bayyana barazanar ƙauracewa zaɓen shekarar 2027 muddin zaɓaɓɓun shugabanni ba su cika alkawurran samar da ababen more rayuwa da kuma shawo kan matsalolin da s**a addabi yankin ba.

Wannan matsaya ta fito fili ne a yayin wani taron manema labarai da wakilin Radio LYB ya halarta, inda gamaiyar matasan yankin ta bayyana takaicinsu kan yadda matsalolin da s**a daɗe suna korafi akansu s**a ki samun mafita.

A cewar Malam Sharp Sharp, tun daga jamhuriya ta farko har zuwa yanzu, al’ummar K**i na ci gaba da fuskantar matsalar rashin ingantacciyar hanya.

Ya bayyana cewa wannan matsala tana jefa manoma cikin mawuyacin hali, inda ake samun tsaiko wajen fitar da amfanin gona daga ƙauye zuwa kasuwanni.

A nasa bangaren, Tajuddeen Aliyu ya yi ƙarin haske kan matsalar rashin kayan aiki da magunguna a cibiyar kiwon lafiya ta yankin, wacce ya bayyana a matsayin gurbatacciya da ta gaza cika maƙasudin samar da kulawa ga jama’a.

Matasan K**i sun jaddada cewa lokaci ya yi da zaɓaɓɓu za su dauki matakai masu ma’ana wajen inganta rayuwar jama’a, domin kuwa rashin yin hakan na iya janyo su kauracewa zaɓe a shekara ta 2027.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarni ga wani kwamitin gwamnatin tarayya da ya aiwatar da gaggawar matakai domin...
11/09/2025

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarni ga wani kwamitin gwamnatin tarayya da ya aiwatar da gaggawar matakai domin sake karya farashin kayan abinci a faɗin ƙasar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Jiha na harkokin noma da tsaron abinci, Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron a Abuja.

Ya ce wannan umarni ya fi mayar da hankali ne wajen tabbatar da samun kariya da sauƙin jigilar kayan gona.

“Shugaban ƙasa ya bayar da cikakken umarni tare da kafa wani kwamiti da ke kula da yadda za a samar da kariya da kuma sauƙaƙa jigilar kayan abinci da kayayyakin gona a manyan hanyoyinmu” in ji Abdullahi.

Ministan ya ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin hangen nesan Tinubu na cimma cikakken ikon cin gashin kai a fannin abinci.

Ya ce gwamnati na shirin ƙaddamar da wani tsari mai suna “Farmer Soil Health Scheme” domin ƙara yawan amfanin gona, tare da sabunta tsarin haɗin kan manoma domin haɗa albarkatu da kuma ƙarfafa manoman karkara.

“Shugaban ƙasa ya nuna matuƙar sha’awa a tsarin haɗin kan manoma a matsayin wata muhimmiyar hanya ta tara albarkatu da samar da ayyukan tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar mambobinsa,” in ji Abdullahi.

Address

No 3 Atiku Abubakar Road
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Radio and TV LYB posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Radio and TV LYB:

Share