16/07/2026
Wata Kaza Ta Tsinci Kanta A Komar Jami'an Bijilanti Bayan K**a Ta Da Laifin Tone Amfanin Gonar Wani Manomi A Kano
Wata kaza ta faɗa komar jami'an bijilanti a garin Ɗorawar Sallau dake ƙaramar hukumar Garun Mallam a jihar Kano bayan k**a ta da laifin shiga gonar wani manomi ta tone masa amfanin gona.
Kazar wadda darajar ta bai wuce naira dubu huɗu ba, ana zarginta da yin ɓarnar amfanin gona na dubban kuɗaɗe, inda bayan an hango tana yin ɓarnar aka yi tara-tara aka k**a ta.
Daga ƙarshe dai mamallakin kazar, Abdullahi Yalo Ɗan K**asho sun sulhunta da mai gonar, wato Sallau Mai Iri, inda kuma aka ja masa kunne da ya dinga saka ido a kan kazar tasa.
Al'ummar garin na Ɗorawar Sallau suna fama da dabbobin dake ɓarnatar musu da amfanin gona, inda ko a kwanakin baya ma an cika hannu da wani zoma bayan ya yi ɓarna a wata gona.
Me zakuce?