11/08/2025
LABARIN CIN AMANA: Wannan matashi ne karami, akwai wata budurwa da s**a san juna sosai, tana kai masa gyaran waya
Wani lokaci ta kawo masa gyaran waya, sai ya shiga cikin guraren da take ajiyar abubuwa na sirri, sai ya ci karo da wani bidiyo na tsiraici da tayi da saurayinta wanda bai dace ba, sai ya tura zuwa wayansa
Sai yaron ya sayi sabbin layukan waya, ya sayi sabuwar waya, sai ya yiwa budurwan message ta WhatsApp ya tura mata bidiyonta, ya bukaci ta tura masa kudade masu nauyi imba haka ba zai yada bidiyonta a duniya
Sai ya tura mata wallet address na crypto domin ta tura masa daloli ta gurin, wato yayi amfani da crypto domin ya kauce wa bincike, sannan layin waya da ita kanta wayar sabbi ya saya duk don ya kaucewa hanyoyin da za'a bi a ganoshi
An tuntubeni akan na taimaka da bincike domin gano yaron, na karbi lambar wayansa nayi analysis babu information, idan na duba location sai ya kadani can yankin Inyamurai, wato yaron ya san cyber security sosai, domin na yaba da kwarewarsa
Amma a karshe sai da na hada da human intelligence na kure duk wayonsa da dabarunsa, aka je aka kamashi a shagonsa aka kawoshi ofishin 'yan sanda na garin, a karshe dai darane ta ci gida, case din ya kare
Jama'a sai a cigaba da kula da kiyayewa, sannan a guji daukar hoto da bidiyo na tsiraci, sannan wanda ya san yana ajiyar bidiyo na tsiraicinsa a wayarsa idan zai kai gyara ya tabbata ya goge su, saboda cin amana a wannan rayuwa tayi yawa, wanda ka yadda dashi shine zai ci amanarka
Allah Ya tsare mana imaninmu, Ya karemu daga sharrin maciya amana.
Me zaku Iya cewa?
kuyi following ko Like na Madubin-Arewa-TV