19/10/2023
Ministan Abuja Nyesom Wike ya yi magana game da batun zargin rushe babban masallacin Abuja da ake cewa zai yi
Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike ya ba babban sakataren Hukumar bunkasa ci gaban birnin tarayya Abuja, Engr Shehu Ahmed Hadi, wa'adin sa'o'i 24 da ya gaggauta fito da manufar gwamnati game da batun ɗan wurin da za a taba mallakin babban masallacin Abuja, don aikin fadada aikin hanya da kuma diyar da aka ware za a biya sakamakon taɓa filin.
Wike ya fadi hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kwamitin babban masallacin tarayya Abujar, karkashin jagorancin shugaban kwamitin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar, inda Wike ya ƙaryata labarin da wasu s**a fara yadawa na cewa zai rushe masallacin.
"Ina so in fara daga abin da aka gaya man, cewa wai na bada umurnin a rushe masallacin National Mosque Abuja, Ina son ku san cewa a siyasa mutane na amfani da wata kafa yar ƙadan don su yi amfani da ita su ci mutumci abokin adawarsu.
" Sarkin Musulmi na ɗaya daga cikin wadanda nake bala'in ganin girmansa, don haka ba wai ina daukarsa a matsayin ɗan uwa bane, a'a ni ina ma ɗaukarsa a matsayin uba ne.
"Don haka duk abin da ya bukata za a yi a National Mosque, a matsayinsa na shugaba, akodayaushe zan bayar da gudunmawata.
"Kun ce Obasanjo ne ya jagoranci kaddamar da Gidauniyar tara kudin ginin masallacin, babu gwamnatin da ba za taimaki cibiyar addini ta kasa ba, muna da rawar da za mu taka cewa duk wuraren ibada an kula da su" Inji Wike