Mu Farka Reporters

Mu Farka Reporters Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mu Farka Reporters, Media/News Company, Jama'are Local Government, Bauchi.

Shugaba Tinubu ba ya da wani ƙuduri na canza sunan Nijeriya ko soke Shari’ar Musulunci - Fadar Shugaban NijeriyaFadar Sh...
21/05/2026

Shugaba Tinubu ba ya da wani ƙuduri na canza sunan Nijeriya ko soke Shari’ar Musulunci - Fadar Shugaban Nijeriya

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin sauya sunan Nijeriya zuwa “United States of Nigeria” tare da soke dokar Shari’ar Musulunci a Arewacin ƙasar ta hanyar yin gyaran kundin tsarin mulki.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Alhamis, ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da yaudara da aka ƙirƙira domin tayar da hankali da haddasa rikici gabanin babban zaɓen ƙasa.

Bayo Onanuga ya ce babu wani shiri daga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na yin gyaran kundin tsarin mulki domin canza sunan Nijeriya ko kuma soke dokar Shari’a a yankin Arewa, kamar yadda ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Credit:

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.ALHAMDULILLAHALHAMDULILLAHALHAMDULILLAHGodiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin...
21/05/2026

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH

Godiya ta tabbata ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya dawo mana da babban Malaminmu,
Sheikh Abdurrazzaq Yahaya Haifan Hafizahullah, gida Najeriya bayan tafiyarsa ƙasa mai tsarki tun ƙarshen azumi.

Alhamdulillah, Mallam ya dawo gida da rai da lafiya.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara masa lafiya mai albarka, Ya ƙarfafa masa jiki, Ya ƙara masa istiqama a kan addini, kuma Ya ci gaba da amfanar da al’umma da iliminsa.

https://chat.whatsapp.com/E6FluaJeA5LIwh3zOaMReY

E-signed:
Dandalin Sheikh Abdurrazzaq Yahaya Haifan.

RAHOTONNIProfessor Isa Ali Ibrahim Pantami ya jajantawa mutanen da iftila'in hatsari mota ya rutsa da su a unguwar Mile ...
21/05/2026

RAHOTONNI

Professor Isa Ali Ibrahim Pantami ya jajantawa mutanen da iftila'in hatsari mota ya rutsa da su a unguwar Mile 3 a jahar Gombe, Prof yayi kira ga matuka ababen hawa musamman manyan motoci da su kula yayin tuki da kuma bin ka'idojin tuki din.

Daga karshe yayi addu'ar Allah ya gafartawa wanda s**a rasu sakamakon hadarin, wanda s**a ji rauni ALLAH ya basu lafia.

MUFARAKA REPORTER'
26/05/2026

21/05/2026

RAHOTONNI

Ansamu hatsaniya yayin gudanar da zaben fitar da goni na dan takarar Majalisar Jahar Lagos a mazabar Kosofe.

MUFARAKA REPORTER'S

Sakon Dantakarar Majalisar Jahar Bauchi na Jama'are Constituency a jamiyyar APMHon. Sani Bello Hanafari Ya Yi Kira ga Al...
21/05/2026

Sakon Dantakarar Majalisar Jahar Bauchi na Jama'are Constituency a jamiyyar APM

Hon. Sani Bello Hanafari Ya Yi Kira ga Al’ummar Jama’are da Matasa Kan Zaman Lafiya da Zaɓe Nagari

Hon. Sani Bello Hanafari ya aike da saƙo ga al’ummar ƙaramar hukumar Jama’are, musamman matasa, inda ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da bin doka bayan kammala rajistar zaɓe.

Ya bukaci jama’a da su jira lokacin zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, tare da fitowa domin kaɗa ƙuri’arsu cikin zaman lafiya da bin doka.

Hon. Sani Bello Hanafari ya kuma yi kira ga magoya baya da al’umma su mara wa jam’iyyar APM mai alamar rogo baya ta hanyar halal da lumana, yana mai gargadin matasa da su guji shan ƙwaya, karɓar kuɗi ko kyaututtuka domin sayar da ƙuri’arsu.

Haka zalika, ya ja kunnen matasa da su nisanci duk wani ɗan siyasa ko mutum da ke amfani da ƙwayoyi, makamai ko tayar da rikici domin haddasa tashin hankali a cikin al’umma.

A ƙarshe, ya yi kira ga jama’ar Jama’are da su haɗa kai wajen gina al’umma mai zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba domin kyakkyawar makomar Jama’are da Jihar Bauchi baki ɗaya.

"Allah Ya bamu zaman lafiya a Najeriya, Jihar Bauchi da ƙaramar hukumar Jama’are." 🤲




— MUFARKA REPORTER'S
21/05/2026

MUHIMMANCIN ZAƁEN NAGARI DA SIYASA MAI TSAFTA A JIHAR BAUCHISiyasa hanya ce ta zaɓar shugabanni da tsara makomar al’umma...
21/05/2026

MUHIMMANCIN ZAƁEN NAGARI DA SIYASA MAI TSAFTA A JIHAR BAUCHI

Siyasa hanya ce ta zaɓar shugabanni da tsara makomar al’umma. Saboda haka, wajibi ne al’umma su fahimci cewa zaɓe ba wasa ba ne, amanar da za ta iya gina ko rusa al’umma ce. Tarihin siyasa a Bauchi ya nuna muhimmancin wayewar kai da ‘yancin zaɓin jama’a.

Zaɓen nagari, jajirtacce, mai kishin al’umma kuma mai son cigaban jama’a yana da matuƙar muhimmanci. Shugaba nagari shi ne wanda gaskiya, adalci da tsoron Allah s**a fi masa muhimmanci sama da son rai ko anfani na kai. Irin wannan shugabanci ne ke kawo ci gaba a fannoni kamar ilimi, lafiya, hanyoyi, tsaro da bunƙasar tattalin arziki.

Al’umma su guji zaɓen mutum saboda kuɗi, jam’iyya ko son zuciya kawai. A duba halayya, gaskiya, aiki da kishin jama’a. Masu wayar da kai a Bauchi sun dade suna kira ga jama’a su guji siyasar kuɗi tare da fifita abin da zai amfani al’umma.

Haka kuma, siyasa mai tsafta ita ce ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai. Siyasa ba ta kamata ta zama hanyar cin mutunci, karya, yaɗa jita-jita, yarfe ko haddasa rikici ba. Bambancin ra’ayi ba yana nufin gaba ko ƙiyayya ba ne. Mutane na iya bambanta a jam’iyya ko ɗan takara amma su ci gaba da zama ‘yan’uwa da maƙwabta masu mutunta juna.

Abin takaici, rikice-rikicen siyasa da amfani da matasa wajen tashin hankali sun jawo illa ga ci gaban al’umma a wurare da dama, ciki har da Bauchi. Bincike ya nuna cewa siyasar tashin hankali da amfani da ‘yan daba na cutar da dimokuraɗiyya da zaman lafiya.

Saboda haka, lokaci ya yi da ‘yan siyasa, magoya baya da matasa za su rungumi siyasa mai tsafta siyasar hujja, mutunci da manufofin cigaba. A yi takara da gaskiya, a yi yaƙin neman zaɓe da ladabi, kuma a karɓi sakamakon zaɓe cikin lumana.

Jihar Bauchi na buƙatar shugabanni masu hangen nesa da jama’a masu zaɓen gaskiya. Cigaban Bauchi ba zai samu da hayaniya, cin mutunci da rikici ba; zai samu ne da haɗin kai, adalci da zaɓen shugabanni nagari masu kishin jama’a.

Kuri’a amanar al’umma ce, siyasa kuma hidima ce ba filin gaba ko cin mutunci ba.



10/12/2024

Arewa: Ga dukiya ga bakar fatara da talauci👇

Hira da Kwararren masani akan ma'adinai na karkashin kasa Tareda Kwararren Dan Jarida Nasiru Adamu El-hikaya

Kwalejin ilimi na Gomnatin tarayya dake Jama'are a Jihar Bauchi ta fara daukar sabbin dalibai na shekaran karatu 2024/20...
02/12/2024

Kwalejin ilimi na Gomnatin tarayya dake Jama'are a Jihar Bauchi ta fara daukar sabbin dalibai na shekaran karatu 2024/2025

Ga masu sha'awa ga adireshinsu na yanar gizo👇
https://fcejamaare.edu.ng/

22/11/2024

Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano hadin guywa da Qatar Nigeria Charity Foundation suna gayyatar dukkan al'ummah musamman marasa Lafiyan da suke fama da irin wadannan cututtuka cewar suzo za'ayi musu aiki kyauta ba tareda ko sisin kobo ba kunna video domin ganin lambar da zaka tuntuba.

10/11/2024

Nasiha Mai Ratsa zuciya daga Malam Sunusi Ibn Sanda 🇳🇪

Address

Jama'are Local Government
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mu Farka Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share