Kauran Lapai TV

Kauran Lapai TV Kauran lapai TV

10/06/2026
SANARWA TA MUSAMMAN:Muna sanar da al’umma cewa Mai Gidanmu, H.E Alh. Sidi Abdul Bomi (Kauran Lapai, Walin Gulu), ya bayy...
08/04/2026

SANARWA TA MUSAMMAN:

Muna sanar da al’umma cewa Mai Gidanmu, H.E Alh. Sidi Abdul Bomi (Kauran Lapai, Walin Gulu), ya bayyana fitarsa daga jam’iyyar PDP kamar yadda ke kunshe a cikin takarda a hukumance.

Biyo bayan wannan mataki, muna jaddada cikakken goyon bayanmu gare shi, tare da bayyana cewa muna tare da shi a dukkan matakan da zai ɗauka na gaba.

Haka kuma, muna yi masa fatan alheri da nasara a dukkan al’amuransa na gaba.

Daga:
Kauran Lapai TV

SABON SHUGABAN PDP NA KASAAn bayyana cewa bayan hukuncin da kotun tarayya ta yanke na soke babban taron jam’iyyar People...
09/03/2026

SABON SHUGABAN PDP NA KASA

An bayyana cewa bayan hukuncin da kotun tarayya ta yanke na soke babban taron jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar a Ibadan, ana sa ran za a sake gudanar da sabon zaben shugabannin jam’iyyar a matakin kasa.

Rahotanni na nuni da cewa H.E. Sidi Abdul Bomi na daga cikin wadanda ake sa ran za su jagoranci jam’iyyar domin kawo gyare-gyare da farfado da ita.

Ana kuma kira ga ‘yan jam’iyyar da magoya baya da su bada goyon baya tare da yi masa addu’ar fatan alheri.

DR SIDI ABDUL BOMI KAURAN LAPAI WALIN GULU THE ONE AND Only PDP National party chairman ASPIRANT.BY Corm Barr Garba Yusu...
05/02/2026

DR SIDI ABDUL BOMI KAURAN LAPAI WALIN GULU THE ONE AND Only PDP National party chairman ASPIRANT.

BY Corm Barr Garba Yusuf sura Maiduguri DG media

We celebrate a truly exceptional leader whose vision, wisdom, and guidance continue to serve as the foundation of our strength. Your leadership inspires confidence, unity, and excellence. With your continued support, we firmly believe there are no limits to what we can achieve together.

May you be elevated to heights beyond imagination, for you are truly in a league of your own. It's a rare privilege to stand with a gentleman of remarkable integrity, humility, and a genuinely pure heart – one who leads not just with authority, but with compassion and purpose.

Dr. Sidi Abdul, Bomi Kaura, NAP, PDP National Party Chairman aspirant, your unwavering commitment to growth, innovation, and people development does not go unnoticed. We're grateful for your mentorship, inspired by your example, and proud to walk this journey under your leadership. We appreciate you today and always. 🙏

"IDAN WANI ABU BAI FARU BA, TO WANI ABU MA BAZAI FARU BA – INSHA ALLAHU. Hakika komai yana tafiya ne da izinin Allah. Ab...
07/01/2026

"IDAN WANI ABU BAI FARU BA, TO WANI ABU MA BAZAI FARU BA – INSHA ALLAHU.


Hakika komai yana tafiya ne da izinin Allah. Abin da bai samu ba, wata kila Allah na boye alheri ne ko kuma yana jiran lokacin da ya fi dacewa. Muna fatan alheri a dukkan lamurran ka H.E SIDI ABDUL BOMI ( KAURAN LAPAI )


H.E DR. SIDI ABDUL BOMI YA ZIYARCI HON. OBETH YAKOI KANGO A MINNA, DOMIN TAYA SU MURNAR BIKIN KIRSIMETI.Mai girma Dan Ta...
25/12/2025

H.E DR. SIDI ABDUL BOMI YA ZIYARCI HON. OBETH YAKOI KANGO A MINNA, DOMIN TAYA SU MURNAR BIKIN KIRSIMETI.

Mai girma Dan Takarar Shagaban Jam'iyyar PDP na kasa, Dr. Sidi Abdul Bomi (Kauran Lapai, Walin Gulu) ya kai ziyarar girmamawa ga Hon. Obeth Yakoi Kango a gidansa da ke Minna, Jihar Neja, domin taya shi murnar bikin Kirsimeti.

Hon. Obeth Kango tsohon ɗan majalisar dokoki ne na jihar Neja (Muya Constituency), tsohon shugaban ƙaramar hukumar Muya, da kuma tsohon kwamishina a jihar Neja.

Ziyarar na nuna alamar ɗorewar zumunta da mutunta juna tsakanin shugabanni da al’umma.

Hotunan Daga Maiyaki I Jubrin

By
Kauran Lapai Tv ✍️
25-12-25

MAI GIRMA DR. SIDI ABDUL BOMI, YA DAMAR HALARTAR TARON ADDU'A NA KWANA UKU GA MARIGAYI HAJIYA KHADIJA ALIYUMai girma dan...
22/12/2025

MAI GIRMA DR. SIDI ABDUL BOMI, YA DAMAR HALARTAR TARON ADDU'A NA KWANA UKU GA MARIGAYI HAJIYA KHADIJA ALIYU

Mai girma dan takardar shugaban Jam'iyyar PDP na kasa Dr. Sidi Abdul Bomi, (Kauran Lapai Walin Gulu) ya halarci taron addu’a na kwanaki uku domin roƙon gafara ga rai da ruhin marigayiya Hajiya Khadija Aliyu, mahaifiya ga Dr. Dantala Aliyu.

Allah Ya jikan ta, Ya sa Aljanna Firdausi ta kasance makomarta.

Hotunan Daga Maiyaki I Jinrin

By
Kauran Lapai Tv ✍️
22-12-2025

H.E SIDI ABDUL BOMI, YA HALARCI TARON BIKIN AUREN 'YAR HON. ABRAHAMS KWAGHNGU:  Mai Girma Dan Takardar shugaban Jam'iyya...
13/12/2025

H.E SIDI ABDUL BOMI, YA HALARCI TARON BIKIN AUREN 'YAR HON. ABRAHAMS KWAGHNGU:

Mai Girma Dan Takardar shugaban Jam'iyyar PDP na kasa H.E Sidi Abdul Bomi, (Kauran Lapai, Walin Gulu), ya halarci liyafar bikin aure na 'yar tsohon Mataimakin Musamman na Gwamnan Jihar Benue, Hon. Abrahams Kwaghngu.

An gudanar da taron ne a Nnam Hall and Complex, lamba 7, Orita Bende Street, kusa da Kashim Ibrahim Road, Old GRA, Makurdi, Jihar Benue.

Kauran Lapai ya bayyana farin cikinsa da samun gayyata, tare da mika sakon fatan alheri ga ma'auratan, yana addu’ar Allah Ya basu zaman lafiya, soyayya da zuri’a ta gari.

Taron ya samu halartar manyan baki da dama daga sassa daban-daban na ƙasa.

Hotunan Daga Maiyaki I Jibrin

Daga
Kauran Lapai Tv ✍️
13-12-2025

Address

Bauchi State, Darazo Lga, Kari
Bauchi
001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kauran Lapai TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share