
12/09/2025
Marigayi Hassan Sarkin Dogarai...
Takaitaccen Tarihin Marigayi Hassan Sarkin Dogarai Shahararren Dogarin Sarkin a Tarihin Najeriya na Wancan Zamani
An haifi Hassan Adamu a garin Kano a shekarar 1925, wanda aka fi sani da Hassan Sarkin Dogarai, shi ne Sarkin Dogarai na uku a zamanin Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.
Ana kiran sa da suna “Bishiya” saboda tsayin sa, Girman jikin sa, karfi, da kuma kallo mai ban tsoro, wanda hakan ya sanya ya jagoranci rundunar Dogarai masu rawani da bulalai a kan dawakai.
Marigayi Alhaji Hassan Adamu ya samu wannan mukami ne a shekarar 1990, lokacin da Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya naɗa shi a matsayin Sarkin Dogarai.
Kafin naɗin Hassan, Sarki Ado Bayero ya naɗa wasu mutum biyu a wannan mukami Na Sarkin Dogarai, wato Marigayi Sarkin Dogarai Dan Wudil, da kuma Marigayi Sarkin Dogarai Adamu.
Amma banbancin su dashi shi ne, Hassan bai fito daga gidan sarauta ba.
A hakikanin gaskiya ma shi asalin sa Direba ne, daga bisani ya zama bawa ga Galadiman Kano, Marigayi Alhaji Tijjani Hashim.
Tijjani Hashim ya fara naɗa Hassan a matsayin Shamaki, kuma wannan ne ya bashi damar fara shiga fada da mukami a gidan sarauta.
A shekarar 1990, bayan rasuwar Sarkin Dogarai na lokacin, Galadiman Kano Tijjani Hashim ya bukaci Sarki Ado Bayero da ya naɗa Hassan a matsayin Sarkin Dogarai, kuma Sarki ya amince.
Hassan ya shahara sosai wajen jarumtaka, ƙarfi da kuma Aminci marar misaltuwa ga Marigayi Sarkin Kano Ado Bayero
Shahararren mawakin Hausa Alhaji Mamman Shata Katsina, ya kwarzanta Hassan da wasu kirari masu ratsa zukatan jaruman maza a cikin wata waƙarsa daya rera masa a cikin shekarun 90s, mai suna "Hassan Sarkin Dogarai", wadda ta ƙara masa suna a ko’ina cikin Kasar nan.
Alhaji Hassan ya rasu a shekarar 2007, kuma iyalansa sun koma gidansa da ke unguwar Sagagi a Kano, inda s**a ci gaba da rayuwar su.
Allah Ya jikansa da rahama, Ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makomar sa. Ameen
~Arewajiyadayau