26/09/2025
🌹 Soyayya a Gidan Makwabta 🌹
Amina yarinya ce ‘yar shekara goma sha bakwai, kyakkyawa, mai natsuwa, wacce ake yaba halayenta a unguwar Galambi. Duk lokacin da ta fita kasuwa, ko ta je rijiyar gari, kowa yana ɗaukar ta a matsayin abin koyi.
A gefe guda kuma, akwai Suleiman – saurayi mai shekara ashirin, ɗan makaranta, wanda ke da buri sosai a rayuwa. Duk da cewa ba shi da yawa a rayuwa, yana da zuciya mai tsafta da buri na zama wani a gaba.
Amina da Suleiman makwabta ne. Sun taso suna ganin juna, amma wani lokaci zuciya tana ɓoye sirri da harshe baya iya furtawa. Duk lokacin da Amina ta fito daga gida tana ɗauke da kwanon ruwa, idanun Suleiman ba sa barinta. Kuma idan ta yi masa murmushi, sai zuciyarsa ta buga tamkar karar gangar aure.
Amina ta fara lura cewa Suleiman yana ƙoƙarin yi mata magana, amma kowanne lokaci idan ya zo kusa sai ya kasa. Duk da haka, a zuciyarta ta fara tambayar kanta:
"Me yasa nake jin wani irin sanyi idan idona ya haɗu da nashi?"
A daren ranar, bayan kowa ya kwanta, Suleiman ya zauna a dakin karatunsa yana rubutu a littafi:
"Akwai magana guda tilo da zuciyata take son faɗa mata, amma harshe na ya kasa – Amina, ina sonki."