13/08/2025
Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Mai Girma Rt. Hon. Muhammad Auwal Jatau (Madugun Katagum), ya wakilci Gwamnan Jihar Bauchi, Mai Girma Sanata Bala Muhammad (Sarkin Yakin Daular Usmaniyya) Abdulkadir, a taron ƙungiyar masu kamfanoni na ƙasa karo na 40, wanda ya gudana a Bauchi.
Taron, wanda ya tattaro shugabannin masana’antu, masu kamfanoni, da jami’an gwamnati daga sassa daban-daban na ƙasar, ya mayar da hankali kan haɓaka masana’antu, ƙarfafa haɗin gwiwar gwamnati da ’yan kasuwa, da samar da yanayi mai kyau don zuba jari a Najeriya.
A jawabin da ya gabatar a madadin Gwamnan, Mataimakin Gwamnan ya yaba da ƙoƙarin ƙungiyar wajen taka muhimmiyar rawa a ci gaban tattalin arzikin ƙasa, tare da tabbatar da cewa gwamnatin Jihar Bauchi za ta ci gaba da samar da ingantattun manufofi da tallafi ga masana’antu da ’yan kasuwa.
Ya ce Jihar Bauchi na da albarkatu masu yawa da za su iya jawo hannun jari daga cikin gida da waje, kuma gwamnati tana ɗaukar matakai don inganta samar da wutar lantarki, hanyoyi, da tsaro domin bunƙasa harkokin kasuwanci.
Taron ya ƙare da tattaunawa tsakanin mahalarta kan sabbin hanyoyin ƙarfafa masana’antu, haɗin kai, da kirkire-kirkire a fannin kasuwanci.