30/01/2026
*AZUMI YA ƘUSANTO… ME KA SHIRYA MISHI?*
*Allah Maɗaukaki Ya sanar da mu manufar azumi tun kafin ya zo, Ya ce:*
*Yā ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta wa waɗanda s**a gabace ku, domin ku samu taƙawa (tsoron Allah).*
*(Suratul Baqarah: 183)*
*Ma’anar ayar a takaice: 👇*
*1. Allah yana kiran muminai kai tsaye, yana nuna girman umarnin.*
*2. Azumi farilla ne, ba sabon abu ba ne, an wajabta shi ma ga al’ummomin da s**a gaba ce mu.*
*3. Manufar azumi ita ce gina taƙawa wato tsoron Allah, kame kai daga abin da Allah ya hana, da ƙara kusanci da Shi.*
*👉 An wajabta muku azumi ne domin ku samu tsoron Allah (TAQWA).*
*Azumi ba wai barin abinci da ruwa kaɗai ba ne, azumi ibada ce ta gyaran zuciya, halayya da niyya. Wannan ne ya sa Manzon Allah ﷺ ya yi gargaɗi, Ya ce: 👇*
*"Duk wanda bai bar magana ta ƙarya da aikata ta ba, Allah ba Ya buƙatar ya bar abincinsa da shansa.(ma'ana har idan baza ka dena karya ba, ba'a buƙatar azumin ka)" (Sahihul Bukhari)*
*Haka kuma Manzon Allah ﷺ ya ce: 👇*
*"Da yawan masu azumi, rabonsu daga azuminsu yunwa da ƙishirwa ne kaɗai. (ma'ana sun kame da barin ci da Sha, amma* *basu bar aikata zunubai ba)*
*(Ibn Mājah)"*
*👉 Wannan yana nuna cewa azumi ba jiki kaɗai ake gyarawa ba, zuciya ma dole a gyara ta.*
*🔹 Shin mun fara gyaran ibadun mu?*
*🔹 Shin mun fara barin munanan ɗabi’u?*
*🔹 Shin mun gyara niyya da hulɗar mu da Allah da mutane?*
*Domin Manzon Allah ﷺ ya ce:👇*
*"Idan Ramadan ya zo, ƙofofin Aljanna s**an buɗe, ƙofofin wuta s**an rufe, shaidanu kuma a ɗaure.”*
*(Bukhari da Muslim)*
*Wanda ya shirya tun kafin Ramadan, shi ne zai fi cin ribar Ramadan. Amma wanda ya bar shiri har sai watan ya shigo, yawanci yana fita bai samu canji ba.*
*Azumi na ƙusantowa ka shirya zuciyar ka, ka shirya niyyar ka, ka kuma shirya ibadar ka.*
*Allah Ya sanya mu cikin waɗanda Ramadan zai gyara su, ba waɗanda zai zama shaida a kan su ba.*
*Allahumma ballighnā Ramaḍāna wa aʿinnā ʿalā ṣ-ṣiyāmi wal-qiyām.*
_©By Zauren Hikimomin Malaman Sunnah🖋️_