Jamil Idris

Jamil Idris Alhamdullilah For Everything
(1)

Google ta ƙaddamar da wani sabon app mai zaman kansa a yau da ake kira Google Password Manager a cikin Google Play Store...
23/08/2025

Google ta ƙaddamar da wani sabon app mai zaman kansa a yau da ake kira Google Password Manager a cikin Google Play Store, domin bai wa masu amfani hanya mafi sauri da tsaro wajen sarrafa kalmomin sirri a wayoyinsu.

🔐 Muhimman abubuwan app ɗin:

Sauƙin shiga kai tsaye zuwa kalmomin sirri da aka ajiye ba tare da shiga system settings ko Chrome ba.

Interface mai sauƙi da sauri wanda zai baka damar duba, gyara ko share passwords cikin sauƙi.

Gargadi idan kalmar sirri ta yi rauni ko kuma aka taba satar ta.

Tsaro na musamman (advanced local encryption) da yake kare bayananka har ma daga Google kanta.

Taimakon biometric lock (yatsa ko fuska) don ƙara tsaro wajen buɗe app ɗin.

🎯 Me yasa wannan app ɗin ya zama mai muhimmanci ❓

Wannan app ya zo a matsayin mataki na ƙara kare sirri da kuma sauƙaƙe sarrafa kalmomin sirri, musamman ga masu amfani da ayyukan Google a rayuwar yau da kullum.

📱 YADDA ZAKA MAGANCE DUK WATA MATSALA A LAYINKA 👇🔹 Idan wani yana bibiyar kira ko kira baya shigowa, ka gwada waɗannan U...
19/08/2025

📱 YADDA ZAKA MAGANCE DUK WATA MATSALA A LAYINKA 👇

🔹 Idan wani yana bibiyar kira ko kira baya shigowa, ka gwada waɗannan USSD codes

✅ Dubawa idan wani yana bibiyar kiranka: * #21 #

✅ Kashewa daga duk wata bibiyar kiranka da ake: # #004 #

✅ Dubawa / kashe Call Waiting: *43 # | #43 #

✅ Boye lambar ka: *31 #

✅ Bayyana lambar ka: #31 #

⚡ Idan matsala ta ci gaba: ka kunna “Airplane mode” ka kashe, ko kuma ka kira Customer Care na layinka.

Allah Ya tsare mu daga duk wata matsala 🙏

Rabiu A. Abubakar

19/08/2025

MTN USER'S DATA 2Gb 500 14days

*312*65*4 #

🚫 IDAN KANADA MATSALAR KIRA A LAYIN KA 👇Idan Kanada matsalar kira a layinka ko kana kira baya shiga ko idan aka kiraka b...
18/08/2025

🚫 IDAN KANADA MATSALAR KIRA A LAYIN KA 👇

Idan Kanada matsalar kira a layinka ko kana kira baya shiga ko idan aka kiraka baya shigowa ga wasu code da zakai Amfani dasu Insha Allahu zaka magance wannan matsalar

#002 #

# #002 #

# #21 #

Rabiu A. Abubakar

📌 Yadda Ake Linking NIN da Airtel SIM ✅1️⃣ Ta USSD Code👉 Danna *996 #👉 Zaɓi "Link NIN"👉 Shigar da 11-digit NIN ɗinka (mi...
18/08/2025

📌 Yadda Ake Linking NIN da Airtel SIM ✅

1️⃣ Ta USSD Code

👉 Danna *996 #
👉 Zaɓi "Link NIN"
👉 Shigar da 11-digit NIN ɗinka (misali: 12345678901)

👉 Jira ka samu confirmation message daga Airtel

2️⃣ Ta SMS

Rubuta:

UpdateNIN NINnumber FirstName LastName

(misali: UpdateNIN 12345678901 Rabiu Abubakar)

👉 Aika zuwa 121

👉 Za ka samu sakon tabbatarwa

3️⃣ Ta Online (Airtel NIN Portal)

👉 Je Airtel NIN Portal
👉 Shigar da Airtel number ɗinka
👉 Shigar da NIN ɗinka
👉 Aika kuma jira sakon tabbatarwa

---

4️⃣ Ta Airtel Service Center

👉 Ka kai NIN slip + SIM card ɗinka Airtel office
👉 Za su haɗa maka nan take

✅ Idan ka gama, zaka iya sake duba status da:
👉 *996 #

📢 Ka tura wannan ga wasu masu amfani da AIRTEL

Rabiu A. Abubakar

📱YADDA ZAKA ƘARAWA NETWORK ƊIN WAYARKA GUDU 👇Ka danna *3370 # network ɗin Wayarka zai ƙara sauri sosai fiye yadda kake t...
18/08/2025

📱YADDA ZAKA ƘARAWA NETWORK ƊIN WAYARKA GUDU 👇

Ka danna *3370 # network ɗin Wayarka zai ƙara sauri sosai fiye yadda kake tunani

Saidai yana jan chaji sosai idan kagama amfani zaka iya cirewa saika sa #3370 # shikenan Duk sanda kake son saurin network zaka iya amfani dashi. 🚫

NOTE Saidai ba kowace waya ce takeyi ba 🙏

Rabiu A. Abubakar ✍️

📶❌ Kana fama da raunin network a wayarka?Yau zan nuna maka code da zaka duba ƙarfin network ɗinka kai tsaye a wayar ka! ...
18/08/2025

📶❌ Kana fama da raunin network a wayarka?

Yau zan nuna maka code da zaka duba ƙarfin network ɗinka kai tsaye a wayar ka! 🔥

📱 Android:
👉 Danna: * #* #4636 #* #*
👉 Zaɓi Phone Information ka ga Signal Strength (dBm)

🍏 iPhone:
👉 Danna: *3001 #12345 #* sannan ka kira.
👉 Za ka shiga Field Test Mode ka ga RSRP (dBm)

📊 Ma’anar dBm:

🔵 -50 ~ -70 dBm = Ƙarfi sosai

🟢 -71 ~ -90 dBm = Kyau

🟡 -91 ~ -100 dBm = Matsakaici

🔴 -101 ~ -120 dBm = Rauni

👉 Ka gwada yanzu, ka faɗa mana ƙarfin network ɗinka a comments! 💬

Anjima zan kawo muku yadda zaku ƙarawa network ɗin Wayarka gudu

Rabiu A. Abubakar

📢 GAGARUMIN WA’AZIN WALIMA A MARADI – JAMHURIYAR NIJAR! 🇳🇪🗓 Rana: Asabar, 02 ga Agusta, 2025📍 Wuri: Birnin Maradi, Jamhu...
31/07/2025

📢 GAGARUMIN WA’AZIN WALIMA A MARADI – JAMHURIYAR NIJAR! 🇳🇪

🗓 Rana: Asabar, 02 ga Agusta, 2025
📍 Wuri: Birnin Maradi, Jamhuriyar Nijar

Ana gayyatar al’umma baki ɗaya zuwa babban taron Walima mai albarka, inda za a gabatar da wa’azi mai cike da hikima, ilimi da faɗakarwa daga manyan malamai na Ahlus-Sunnah.

Masu Halarta Daga Cikin Fitattun Malamai:

🕌 Sheikh Dr Muhammad Kabiru Haruna Gombe

🕌 Sheikh Mukhtar Abubakar Zinder

🕌 Sheikh Dr Ibrahim Rijiyar Lemu

🕌 Sheikh Abdulbasir Unguwar Maikawo

🕌 Sheikh Dahiru Yahaya Maradi

🕌 Alaramma Nasiru Salihu Gwandu

🕌 Da sauran zababbun malamai da alarammomi.

📌 Abin jira ya zo kusa! Kada a ba ka labari – ka zamo cikin waɗanda s**a halarta, s**a amfana, kuma s**a ɗora wa kansu hanyar samun ƙarin ilimi da tsoron Allah.

🕊️ "Wani lokaci taro guda na iya canza rayuwa gaba ɗaya."

🤲 Allah ya ba da ikon halarta cikin lafiya da amfāni. Ameen.
Copied

🌙 TSAYA KA GYARA SALLAH KA — CIKAKKEN BAYANI AKAN SALLAH DAGA TSHARKI HAR ZUWA KARSHENTANa rubuta wannan domin Musulmi y...
25/07/2025

🌙 TSAYA KA GYARA SALLAH KA — CIKAKKEN BAYANI AKAN SALLAH DAGA TSHARKI HAR ZUWA KARSHENTA

Na rubuta wannan domin Musulmi ya fahimci ibadarsa, kuma kada mu zama 'yan Sallah amma ba 'yan Aljanna ba.

---

🔹 1. MA'ANAR SALLAH & MUHIMMANCINTA

Sallah tana nufin: "ƙusanci da Allah ta hanyar karatu, sujuda da ruku'u."

🕌 Sallah itace ginshiƙi na biyu bayan Shahada. Idan ta rushe, sai addini ya rushe.

Dalili daga Al-Qur’ani:

> وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ إِنَّ ٱلصَّلَوٰةَ تَنْهَىٰ عَنِ ٱلْفَحْشَآءِ وَٱلْمُنكَرِ ۗ
(Al-‘Ankabūt: 45)
Fassara: Ka tsayar da Sallah, domin Sallah tana hana alfasha da mummunan aiki.

📝 Idan kana yin Sallah amma kana shaye-shaye, zina, ko zamba, ka duba ko Sallah ɗinka na da inganci.

---

🔹 2. TSARKI (طَهَارَة): SHARAƘA NA FARKO KAFIN SALLAH

A. ALWALA (الوضوء)

Ayah:

> يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى ٱلصَّلَوٰةِ فَٱغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ...
(Surat Al-Mā’idah: 6)

Hadisi:

> "La tuqbalu ṣalātu aḥadikum idhā aḥdata ḥattā yatawaḍḍa."
"Ba a karɓar Sallarku idan kuna da najasa har sai kun yi alwala." (Bukhari & Muslim)

Abubuwan da ake Wankewa:

1. Fuska

2. Hannaye har gwiwar hannu

3. Shafe kai

4. Wanke ƙafafu zuwa idon sawu

✔️ Wanda ya rasa ruwa, sai yayi Tayammam da ƙasa mai tsarki:

> فَلَمْ تَجِدُوا مَآءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا... (An-Nisā’: 43)

---

🔹 3. NIYYA (النِّيَّةُ) — ZUCIYA CE KE AYYANA IBADA

Hadisi:

> "Innamal-aʿmālu bin-niyyāt..."
"Ayyuka sun danganta da niyya." (Bukhari & Muslim)

🧠 Niyya na nufin: “Ina yin wannan Sallah ne saboda Allah, lokacin kaza.”
Babu buƙatar ka furta da baki, zuciyarka kawai ake buƙata.

---

🔹 4. TSAIWA A SALLAH DA LADABI (القيام والخشوع)

Ayah:

> قَدْ أَفْلَحَ ٱلْمُؤْمِنُونَ ٱلَّذِينَ هُمْ فِي صَلَاتِهِمْ خَاشِعُونَ
(Al-Mu’minūn: 1-2)
Fassara: Lallai muminai sun ci nasara, waɗanda ke yin Sallarsu da ladabi da nutsuwa.

🧍 Tsayuwa da nutsuwa alama ce ta tsoron Allah. Ka kiyayi yawan yawo da ido, tunani da motsi cikin Sallah.

---

Sauran Bayani a comment section👇
Copied

Alqur'ani Zeyi Ceto A Gobe Qiyāmah Allah Yasa mu A Ceton Alqur'ani.🤲🤲🤲 zaharaddeen adam
23/07/2025

Alqur'ani Zeyi Ceto A Gobe Qiyāmah
Allah Yasa mu A Ceton Alqur'ani.
🤲🤲🤲 zaharaddeen adam

ABUBUWA 5 DA SUKE JANYO BALA'I ACIKIN AL'UMMAHadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)Yace Wa...
21/07/2025

ABUBUWA 5 DA SUKE JANYO BALA'I ACIKIN AL'UMMA

Hadisi Ya Tabbata daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya ƙara masa yarda)

Yace Watarana muna zaune sai ga Manzon Allah (S.A.W) yazo wucewa, Yace " ya ku taron muhajirai! Akwai wasu abubuwa guda 5 idan al'umma s**a Jarabtu dasu!

Ina Roƙon Allah kada ku riske wannan Lokaci.

1⃣ Duk Al'ummar da s**a bayyana Alfasha! Tabbas zasu samu kansu cikin Annoba da yaduwar sabbin cututtukan da ba'a taɓa ganin su ba!

2⃣ Duk Al'ummar da suke tauye modu da sikeli! Tabbas zasu samu kansu cikin yanayi na fari (rashin ruwan sama), Tsadar Rayuwa da cutarwa daga azzaluman Shuwagabanni.

3⃣ Duk Al'ummar da s**a hana zakkar dukiyoyinsu! Tabbas Allah zai hanasu ruwan sama! Idan kaga Ruwa, an yine kawai saboda yara da dabbobi da suke rayuwa a cikinsu.

4⃣ Duk Al'ummar da s**a saɓa alkawarin Allah da Manzon sa! Tabbas Allah zai ƙasƙantar dasu a gaban abokan gabansu.

5⃣ Duk Al'ummar da Shuwagabaninsu basu hukunci da Littafin Allah, kuma suke chanza Abinda Allah ya sauƙar! Tabbas Allah zai sanya gaba, yaƙi da ganin Aibin Junansu a tsakaninsu.

Ibn Majah ne ya Rawaito Wannan Hadisin.

Dan Girman Allah acikin Waɗannan Abubuwa 5 wanne ne ba'a aikatawa a Nigeria? A hakan kuma muke jiran ganin dai dai

Allah kashiryemu ka gyara mana zukatanmu

~ Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum HAFIZAHULLAH

Address

Miri Along Jos Road Bauchi
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jamil Idris posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share