Kitabu Wassunnah

Kitabu Wassunnah Disussion about islamic view using Quran and hadith

_🌹🌹An kar6o daga Ibn Abbas R.A yace : Manzon Allah S.A.W ya kasance yana nemawa Hasan da Husaini tsari yana cewa : U'IZU...
11/07/2025

_🌹🌹An kar6o daga Ibn Abbas R.A yace : Manzon Allah S.A.W ya kasance yana nemawa Hasan da Husaini tsari yana cewa : U'IZUKUMA BIKALIMATILLAHITTAAMMAH, MIN KULLI SHAIDANIN WA HAAMMAH, WA MIN KULLI AININ LAAMMAAH.🌹🌹_

*▶️Yakan ce : Babanku Annabi Ibrahim Ya Kasance Yana 'Ya'Yensa Isma'il da Ishaq A.S Tsarin Allah Da Wannan Addu'a.*

Abu Dawud

_🌹🌹An kar6o daga Abu Zarr R.A, haqiqa Annabi S.A.W yace masa : Ya kai Aba Zarr, idan ka dafa miya, ka qara ruwanta, sai ...
11/07/2025

_🌹🌹An kar6o daga Abu Zarr R.A, haqiqa Annabi S.A.W yace masa : Ya kai Aba Zarr, idan ka dafa miya, ka qara ruwanta, sai ka rabawa maqobtanka.🌹🌹_

Muslim

*🕋HUKUNCIN AZUMTAR RANAR ASHURA KADAI🕋*  _♦️Ya halatta mutum ya azumci iya ranar Ashura, ammadai an fi so ya hada da azu...
05/07/2025

*🕋HUKUNCIN AZUMTAR RANAR ASHURA KADAI🕋*

_♦️Ya halatta mutum ya azumci iya ranar Ashura, ammadai an fi so ya hada da azumtar ranar kafinta ko bayanta, domim hakan tabbatacciyar sunnace daga Annabi S.A.W inda yace : Idan Allah ya kaini badi, to zan azumci tara ga wata.♦️_

Muslim.

*▶️Ibn Abbas R.A yace : Yana nufin tare da goma ga wata.*

*🛑DAGA CIKIN MANYAN ZUNUBAI AKWAI YANKE ZUMUNTA🛑*  _🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Mai yanke zumunta ba zai shiga aljannah ...
05/07/2025

*🛑DAGA CIKIN MANYAN ZUNUBAI AKWAI YANKE ZUMUNTA🛑*

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Mai yanke zumunta ba zai shiga aljannah ba.🌹🌹_

Bukhari da Muslim

05/07/2025
*🕋AZUMIN ASHURA🕋*  _🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Azumin ashura,ina sa rai daga Allah cewa zai kankare zunubin shekarar da...
30/06/2025

*🕋AZUMIN ASHURA🕋*

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W yace : Azumin ashura,ina sa rai daga Allah cewa zai kankare zunubin shekarar da tazo kafinsa.🌹🌹_

Muslim.

*▶️Kar kayi sakaci wajan qin azumtarsa, ka tunawa abokanka da masoyanka, a cikin azumtarsa akwai alkhairi mai girma.*

30/06/2025

*🕋AZUMIN RANAR ASHURA🕋*

_🌹🌹An kar6o daga Ibn Abbas R.A yace : Ma'aiki S.A.W ya zo madina, sai ya samu yahudawa suna azumtar ranar Ashura , sai yace : Me kenan wannan ? Sai s**a ce : Wannan ranace mai kyau, itace ranar da Allah ya tserar da banu isra'il daga maqiyinsu, don haka Annabi Musa ya azumci ranar, sai yace S.A.W : Ai na fiku cancantar Annabi Musa, sai shi ma ya azumce shi, yayi umarni da a azumce shi.🌹🌹_

Bukhari

*☘️Ya Ubangiji Ina Roqonka Tabbatuwa Cikin Lamura, Da Qulla Niyya Akan Shiriya.🤲*  _🌹🌹An kar6o daga Irbaab Bn Saariyah R...
18/06/2025

*☘️Ya Ubangiji Ina Roqonka Tabbatuwa Cikin Lamura, Da Qulla Niyya Akan Shiriya.🤲*

_🌹🌹An kar6o daga Irbaab Bn Saariyah R.A, haqiqa Annabi S.A.W yace : ...Yadda lamarin yake, duk wanda ya rayu a cikinku, to zai ga sa6ani mai yawa, amma na haneku da biyewa qirqirarrun abubuwa, domin su din 6ata ne, duk wanda ya riske su a cikinku, to yayi ruqo da sunnata, da kuma sunninin halifofina shiryayyu masu shiryarwa, ku riqesu da turamenku.🌹🌹_

Abu Dawud da Tirmizy

Address

Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kitabu Wassunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kitabu Wassunnah:

Share