Älhj Umar Soja

Älhj Umar Soja Alhmdllh

25/07/2025

Ashhadu Allah ila ha
illallah 💚
Ashhaadu Annah Muhammadu
Rasulullah ❤️

MENENE SALLAR DUHA?Sallar Duha (الضُّحى) wani nau'in sallar nafilah ce da ake yi a lokacin duhā, wato lokacin da rana ta...
24/07/2025

MENENE SALLAR DUHA?

Sallar Duha (الضُّحى) wani nau'in sallar nafilah ce da ake yi a lokacin duhā, wato lokacin da rana ta fara hayewa sosai bayan fitowarta. Ana kiranta da Sallar Ishraq idan an yi ta da wuri (nan da nan bayan rana ta fito).

🕰️ LOKACIN YINTA

Farko: Bayan fitowar rana da kusan mintuna 15-20.

Karshe: Kafin sallar Azahar da kusan mintuna 10-15.

Misali: Idan rana ta fito 6:30am, zaka iya fara sallar Duha daga 6:50am har zuwa kusan 11:30am (idan Azahar tana 11:45am).

🌟 MUHIMMANCINTA DA FADILARTA

1. Sunnah mai karfi ce (سنة مؤكدة) – Annabi ﷺ yana yinta akai-akai.

2. Lada mai girma – Manzon Allah ﷺ ya ce:

"Kowane ƙashi a jikinku yana da sadaka... Sallar Duha raka’a biyu suna isar da wannan sadaka."
(Sahih Muslim: Hadisi 720)

3. Sallar Masu tuba – Ana kiran ta "Sallat al-Awwābīn", sallar masu tuba da komawa ga Allah.

4. Suna janyo arziki da albarka – An ruwaito cewa Manzon Allah ﷺ ya ce

"Allah na isar wa bawansa duk bukatunsa idan ya ci gaba da yin sallar duha."
(Tirmidhi – Hasan)

🧎‍♂️ YADDA AKE YINTA

Ana yinta a raka'a biyu-biyu.

Mafi ƙanƙanta: raka'a 2.

Mafi yawa: raka'a 8 zuwa 12, kamar yadda Annabi ﷺ ya saba yi.

ALLAH yabamu iko
Älhj Umar Soja✍🏽✍🏽

Bayan kwanaki kaɗan da sakin matarsa, ya ɗauki waya ya kirata yace: -Ki yi haƙuri ki dawo, Tace masa cikin hali irin na ...
24/07/2025

Bayan kwanaki kaɗan da sakin matarsa, ya ɗauki waya ya kirata yace: -

Ki yi haƙuri ki dawo, Tace masa cikin hali irin na fushi: Akwai Kofi a kusa da kasai? Cikin mamaki ya ce Kofi kuma!? Tace: Eh. Yace: Babu. Tace: Jeka Kitchen ka ɗakko. Cikin yanayi na rashin fahimta yaje ya ɗakko.

Tace masa sake shi ya faɗi ƙasa. Yace: Na sake shi.

Tace: kamar yadda kofin ya tarwatse haka alaƙata da kai ta tarwatse, kamar yadda kofin ba zai gyaru ba, nima ba zan koma gidanka ba.

Yace Allah Sarki! Ai kofin na roba na yar, babu abin da ya same shi. 👌

Tace Kash! Maza ba zaku daina yaudara ba. Ai hikenan, sai kazo da Magriba ka ɗauke ni mu koma. 🤗🤣

Yan Uwana Ku taimakawa waɗanda Aurensu ya lalace da addu'a, Allah ya daidaita tsakaninsu.👋

24/07/2025
Wanda ya iya juyawa waɗannan 'yan sanda  su zama sojoji gaskiya na girmama fasaharsa. Dole mu haɗu muyi hoto tare! Kuma ...
23/07/2025

Wanda ya iya juyawa waɗannan 'yan sanda su zama sojoji gaskiya na girmama fasaharsa. Dole mu haɗu muyi hoto tare! Kuma yana da babbar kyauta mai tsoka Bismillah Bari muga Wa zai cinye wannan gasa

Mutane uku (3) ina kyautata zaton cewa; dasu Allah zayyi amfani wurin sauya wannan ƙasar daga zalunci da cin amana zuwa ...
23/07/2025

Mutane uku (3) ina kyautata zaton cewa; dasu Allah zayyi amfani wurin sauya wannan ƙasar daga zalunci da cin amana zuwa adalci da gaskiya

Kuyi musu biyayya, ku bisu sau-da-ƙafa, kuma kuyi musu uzuri idan sunyi kuskure 📌

Älhj Umar Soja

23/07/2025

SHEKARA 40 Da S**a Wuce kowa Yana Kwadayin Ya Tara 'Ya'ya. Amma Yanzu Mutane Tsoron Tara 'Ya'ya Sukeji..........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce 'Ya'ya ke Yiwa Iyaye Biyayya. Yanzu Iyaye Ke Yiwa 'Ya'ya Biyayya........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Aure Nada Sauki Sakin Mace Keda Wuya. Yanzu Aurene Da Wuya Sakin Macene Da Sauki........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Duk Munsan 'yan Unguwarmu. Yanzu Dan Unguwarku Kakewa Kallon Bako.........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Har Musun Fifikon Shekaru Mukeyi. Yanzu Kowa So Yake A Rage Masa Yawan Shekaru........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Har Gasar Fifikon Qiba Muke Yi. Yanzu Kowa Gudun Qiba Yake Saboda A Burge........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Attajirai ke Qoqarin Nuna Suma Talakawane. Yanzu Talakawa ke Qoqarin Nuna Suma Attajirai Ne..........................................
SHEKARA 40 Da S**a Wuce Mutum Daya ke Nema Kuma Ya Dauki Nauyin Gidan Gaba Daya. Yanzu Duk Gidan ke Aiki Dan Adauki Nauyi Yaro Daya........................................
SHEKARU 40 Da S**a Wuce Mutane ke Zaman Jiran Lokacin Sallah Yayi Sabida Isasshen Lokaci Da Son Yin Ibadar, Amma Yanzu Sallar Muke Tarawa Tana Jiran Muyi ta Sabida Muna Ganin Ba Laifi Idan Mun Hade Su Alokaci Guda.......................................
DAGA 1985 ZUWA YAU FA SUNE SHEKARA 40.
WANNAN SAUYIN ƘARARA YAKE KUMA MU MUKA CHANJA DUNIYA BA ITA TA CHANJAMU BA....................................

SHEKARA 40 Masu Zuwa Ya kuke Tunanin
Abubuwa Yadda Zasu Kara Chanjawa ?

Wai Me Duniyar Nan Ke Rudar Mu Dashi Ne ?

Abinda Kafi Karfi Kiri Kiri Kana Kallo Yana Neman Fin Karfin ka Koma Yafi Karfin Ka, Wallahi Abu Biyu kadai Idan Muka Gyara Ya l Ishe mu Mu Ga Chanji.

1- MUJI TSORON ALLAH A CIKIN DUKKAN LAMURAN MU.

ALLAH SA MUI KARSHE ME KYAU

Address

Rahama Bauchi
Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Älhj Umar Soja posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share