17/02/2026
ABIN MAMAKI BAYA KAREWAđ„±
DATTI ASSALAFIY âđ»
Wadannan wasu gungun âyan bindiga ne da ke boye a cikin gari, suna gayyatar fulanin daji âyan bindiga a kan su zo su sayi mak**an ta'addanci a gurinsu
Har ma suna tallata wa cewa ga bindiga kirar AA (makamin harbo jirgin sama) da alburusai, sannan kuma ga bindiga kirar AK-47 samfurin Rasha, a cikin dakin da suke sayar da mak**an har da fankoki suna kadawa suna basu iska
Subhanallah, wani irin abu ne wannan? Lallai wadannan mutanen dole suna da masu daukar nauyi da ke mara musu baya
Na ga k**ar hasken rana ya shiga cikin wannan bidiyo da 'yan ta'adda s**ayi, idan bincike za'ayi ta sanadin hasken rana da ya shiga bidiyon za'a gano inda wannan gini yake ta hanyar amfani da digital forensics gadgets
âYan bindiga na amfani da manyan bindigogi irinsu AA da AK a lokaci guda wasu daga cikin jami'an tsaron mu na amfani da kananun bindigogi wanda da zaran an fara musayen wuta sun dau zafi sun dena aiki sai sun huce
Akwai bindigogi da tankokin yakin da akayi amfani da su tun lokacin yakin Biafra har zuwa yanzu ba'a canzasu daga hannun jami'an tsaron Gwamnati ba, a lokacin da wani dan siyasa shi kadai ya saci kudin da sun haura Naira biliyon dari kuma yana yawon kamfe ba abinda za'a masa
Batun tsaro ya koma siyasa da kasuwanci, Allah Ka dai ne zai iya ceto yankin mu na Arewa
Ubangiji Allah Ka mana maganin abinda ya fi karfin mu