Bulaliya Hausa News

Website

Bulaliya Hausa News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Bulaliya Hausa News, News & Media Website, G R A Bauchi, Bauchi.

BARKA DA ZUWA TASHAR BULALIYA HAUSA NEWS

TASHA CE WACE AKA SAMAR DA ITA DOMIN KAWO MUKU INGATATTUN LABARAI NA YAU DA KULLUM

DOMIN CIGABAN NIGERIA BAKI DAYA MUNGODE

TIRKASHI: Ba Mu Son Musulmi Ya Jagoranci Makarantar Mu, Ɗan Uwanmu Kirista Muke So — Masu Zanga-zanga a JosDaga Rabiu Us...
13/08/2026

TIRKASHI: Ba Mu Son Musulmi Ya Jagoranci Makarantar Mu, Ɗan Uwanmu Kirista Muke So — Masu Zanga-zanga a Jos

Daga Rabiu Usman

Wasu mutane na iya tunanin cewa lamarin da ya jawo zanga-zangar da ake yi a yankin Jos South na Jihar Plateau yana da alaƙa da kashe yara ko wani babban bala’i da ya afku a yankin.

Sai dai, a cewar marubucin wannan rahoto, abin da ya jawo zanga-zangar shi ne naɗin wani Musulmi a matsayin shugaban wata makarantar gwamnatin tarayya da ke yankin.

Makarantar da ake magana a kai ita ce National Veterinary Research Institute (NVRI) da ke Vom, Jos South, wadda aka kafa tun shekarar 1924.

Rahoton ya bayyana cewa tun bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Abdullahi Ahmad, ɗan asalin Jihar Gombe kuma Musulmi, a matsayin shugaban makarantar, wasu daga cikin al’ummar yankin s**a fara gudanar da zanga-zanga suna neman a cire shi daga mukamin.

A cewar rahoton, Farfesa Abdullahi Ahmad ya kwashe sama da shekaru 20 yana aiki a makarantar, inda ake zargin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa cibiyar a tsawon shekarun da ya yi yana aiki a can.

Haka kuma, rahoton ya ce ba a naɗa shi kai tsaye ba tare da an bi ƙa’ida ba, domin an buɗe damar neman aikin, aka tantance masu neman mukamin, sannan aka gudanar da hira kafin kwamitin zaɓe ya bayyana wanda ya fi cancanta.

Sai dai, duk da wannan tsari, masu zanga-zangar na neman a cire Farfesa Abdullahi Ahmad tare da buƙatar a naɗa ɗan asalin yankin a matsayin shugaban makarantar.

Marubucin rahoton ya bayyana cewa irin wannan mataki na iya haifar da tambayoyi kan yadda ya kamata a gudanar da naɗe-naɗe a hukumomin gwamnati, musamman idan aka mayar da asalin mutum ko addininsa a matsayin babban dalilin ƙin amincewa da shi.

Ya ce idan aka amince da irin wannan tsarin, akwai yiwuwar hakan ya zama al’ada inda duk wata hukuma ko ma’aikata da ke wani yanki za ta riƙa fuskantar matsin lamba domin a naɗa ɗan yankin, maimakon a yi la’akari da cancanta da ƙwarewa.

Musulmai da Kiristocin Najeriya sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya.Ƙarin bayaniShugabannin addinin Musulunci da Kir...
13/08/2026

Musulmai da Kiristocin Najeriya sun sanya hannu kan sabuwar yarjejeniya.

Ƙarin bayani

Shugabannin addinin Musulunci da Kiristoci fiye da 50 ne s**a rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinan biyu a Najeriya,

An ƙaddamar da wata sabuwar ƙungiya da za ta mayar da hankali wajen inganta fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin addinai, a taron da ƙungiyar Musulmi ta Duniya da ke da hedikwata a Saudiyya ta shirya a Abuja.

Yarjejeniyar ta zo ne watanni bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Najeriya da gaza kare Kiristoci daga hare-haren ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, tare da yin barazanar daukar matakin soji kan ƙasar.

Sai dai ba a yi magana kan kalaman Trump ba a taron da aka sanya hannu kan yarjejeniyar.

Sakatare Janar na ƙungiyar Musulmi ta Duniya, Mohammad Al-Issa, yana cewa dukkanin mabiya addinan biyu na maraba da wannan tsari da ya ce ya "buɗe sabon shafi".

Shugabannin Musulmi da Kiristocin da s**a halarci taron sun ce yarjejeniyar za ta iya taimakawa wajen rage kalaman ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu wajen bikin, ya ce gwamnati ta kuduri aniyar ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa dunƙulalliyar ƙasa duk da bambance-bambancen da ke tsakaninta.

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Donald Trump ya yi musayar jiragen sama a asirce yayin da yake barin tar...
11/08/2026

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Donald Trump ya yi musayar jiragen sama a asirce yayin da yake barin taron ƙungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya a watan da ya gabata, a matsayin matakin kariya ga barazanar da zai iya fuskanta daga Iran.

Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Donald Trump ya yi musayar jiragen sama a asirce yayin da yake barin taron ƙungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya a watan da ya gabata, a matsayin matakin kariya ga barazanar da zai iya fuskanta daga Iran.

Shugaban Amurka ya hau jirgin Air Force One a bainar jama'a kafin a yi a shigar da shi cikin wata babbar motar abinci a filin jirgin sama sannan a kai shi jirgin sama na soja, ba tare da 'yan jarida da wasu ma'aikatan Fadar White House sun sani ba, in ji jaridar Washington Post.

Jami'ai sun shaida wa abokiyar hulɗar BBC ta Amurka CBS News cewa Amurka ta gano wata barazana ta gaskiya da Iran ke yi na harba makami mai linzami a kan jirgin. Fadar White House ba ta tabbatar da wannan sirrin ba

Mece ce shawara kan wanda ya dace a tsayar?A karkashin kungiyar G100, shugabannin manyan jam’iyyun adawar Njeriya sun ko...
11/08/2026

Mece ce shawara kan wanda ya dace a tsayar?

A karkashin kungiyar G100, shugabannin manyan jam’iyyun adawar Njeriya sun koma teburin tattaunawa da nufin samar da kawancen siyasa mai karfi, wanda zai iya kalubalantar dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a matakin shugaban kasa.

An yi wasu dabaru an sauya jirgin da Donald Trump ya yi amfani da shi yayin dawowa daga Turkiyya saboda barazanar kai ma...
11/08/2026

An yi wasu dabaru an sauya jirgin da Donald Trump ya yi amfani da shi yayin dawowa daga Turkiyya saboda barazanar kai masa hari. Karanta cikakken rahoton a sashen sharhi.

11/08/2026

Ga wata sabuwa Kuma; Ra'ayin Yan kannywood ya rabu gida biyu, bisa samun wasu bangaren da sun ki marawa Tinubu baya, dukda cewa Dauda Kahutu Rarara da shi da tawagarsa Sun fito Sun nuna cikakken goyon bayansu ga Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Meye naku Ra'ayin?

An ji matashin a cikin gajeren bidiyon mai tsawon daƙiƙa 26 yana cewa: "Kamar yadda kuke gani, sarki aka ba carry over, ...
10/08/2026

An ji matashin a cikin gajeren bidiyon mai tsawon daƙiƙa 26 yana cewa: "Kamar yadda kuke gani, sarki aka ba carry over, shi ne ya zo da ƴan kombarsa, za a zo a sulhunta... Hattara lecturers."

Ƙarin bayani -

Wani faifan bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka ga wani matashi na iƙirarin cewa tawagar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ta isa harabar jami'ar da sarkin ke karatu domin a "sulhuntawa" saboda an ba Sarkin "Carry Over".

An yaɗa bidiyon sosai a shafukan sada zumunta da dama, inda aka yi ta muhawara kan dalilin da zai sa Sarkin ya faɗi darasi cikin darussan da yake ɗauka.

An ji matashin a cikin gajeren bidiyon mai tsawon daƙiƙa 26 yana cewa: "Kamar yadda kuke gani, sarki aka ba carry over, shi ne ya zo da ƴan kombarsa, za a zo a sulhunta... Hattara lecturers."

Mai martaban dai ya koma Jami'ar Northwest da ke Kano domin karantar ilimin shari'a, inda ya fara karatunsa a farkon shekarar nan daga aji na biyu.

10/08/2026

Kun san bambanci tsakanin biranen Istanbul da Ankara da ke ƙasar Turkiyya? Mutane da dama suna zaton Istanbul ne babban birnin ƙasar. Wataƙila suna wannan zato ne saboda birni ne da ake hada-hada. Amma a haƙiƙanin gaskiya Ankara shi ne babban birnin ƙasar. Ga ƙarin bayani game da waɗannan muhimman birane na duniya.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta shiga zango na ƙarshe amma har yanzu ''ba a cimma mats...
09/08/2026

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta shiga zango na ƙarshe amma har yanzu ''ba a cimma matsaya kan buɗe mashigar Hormuz'' ba.

Ƙarin bayani -

Oman ta ce tattaunawa na gudana tsakanin ta da Iran a kan ƙulla yarjejeniyar tabbatar da tsaro ga jiragen ruwa masu wucewa ta mashigar Hormux, yayin da Tehran ta yi gargaɗin cewa ba za ta gaggauta buɗe hanyar tekun mai matuƙar muhimmanci ba.

A ranar Asabar dukkan ɓangarorin s**a bayyana cewa tattaunawar tasu na samun armashi, amma babu wani tabbaci kan lokacin da za a ƙulla yarejejeniya. Ma'aikatar harkokin wajen Oman ta yi gargaɗin cewa duk wani hari a kan jiragen ruwan zai iya kawo cikas ga tattaunawar da ke gudana.

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce tattaunawar ta shiga zango na ƙarshe amma har yanzu ''ba a cimma matsaya kan buɗe mashigar Hormuz'' ba.

Tun bayan harin da Amurka da Isra'ila s**a ƙaddamar kan Iran a watan Faburairu, Tehran ta rufe mashigar wadda ta kanta ake jigilar aƙalla kashi biyar cikin ɗari na mai da iskar gas da ake amfani da su a sassan duniya'

Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗi a Najeriya ta Tracka ce ta wallafa bayanan da ke zargin cewa gwamnatin ta...
06/08/2026

Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗi a Najeriya ta Tracka ce ta wallafa bayanan da ke zargin cewa gwamnatin ta Kano ta ware miliyoyin kudaɗe a kasafin kuɗin 2025 amma ba a ga ayyukan ba.

Karin bayani -

Wani batu da yake ta waɗari a kafar sada zumunta shi ne zarge-zarge da rahotanni da ke nuna cewa an ware ko an biya kuɗaɗe ga wasu ayyuka a jihar Kano da ake cewa ba a same su a wurin da aka ce an aiwatar da su ba.

Ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗi a Najeriya ta Tracka ce ta wallafa bayanan da ke zargin cewa gwamnatin ta Kano ta ware miliyoyin kudaɗe a kasafin kudin 2025 amma ba a ga ayyukan ba.

A ranar 5 ga Agusta 2026, ƙungiyar da ke bibiyar aiwatar da kasafin kuɗin a Najeriya ta yi zargin cewa an fitar da fiye da naira biliyan ɗaya domin gyaran azuzuwa 100 a faɗin jihar ta Kano amma kuma ba a gano wurin da makarantun suke ba.

Har wa yau, Tracka ta kuma yi batun ƙarin wasu naira miliyan 235 da aka ware domin gina wata makaranta a ƙaramar hukumar Sumaila amma kuma babu ita babu labarinta.

Address

G R A Bauchi
Bauchi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bulaliya Hausa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share