22/08/2026
Lūda/Yamrat–Ɗan Dango: Ƙarfi da Akidar Siyasa
Mutanen Gundumar Yamrat/Ɗan Dango na ci gaba da tabbatar da matsayinsu a siyasance, tare da ƙara shirya tarurrukan neman goyon baya da ƙarfafa haɗin kan jama'a.
Wannan ba wai taro kawai ba ne; alama ce ta wayewa, kishin al’umma da kuma cikakkiyar akida ta siyasa. Mutanen Lūda sun tabbatar da cewa suna da ra’ayinsu, kuma ba za a iya juya su daga abin da s**a yi imani da shi ba.
A wannan tafiya ta neman kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya ta Bauchi LGA a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, suna ƙara tabbatar da muhimmancinsu wajen tabbatar da nasarar Hon. Dr. Alhaji Adamu Sa’idu.
Lūda ta yanke shawara. Lūda ta san abin da take so. Lūda na tafiya da NNPP!