Kautal Pulaaku Bauchi

Kautal Pulaaku Bauchi Kautal fulaaku fulbe associationof Nigeria reshen jahar bauchi state

LABARI DA DUMI DUMINKAUTAL PULAAKUƘUNGIYAR FULBE TA NAJERIYASANARWA GA AL'UMMAAn jawo hankalinmu kan labarin ƙarya da ak...
17/10/2025

LABARI DA DUMI DUMIN

KAUTAL PULAAKU
ƘUNGIYAR FULBE TA NAJERIYA

SANARWA GA AL'UMMA

An jawo hankalinmu kan labarin ƙarya da ake yadawa cewa tsoffin shugabannin Miyetti Allah Kautal H**e na jihohin Bauchi, Taraba da Adamawa an kore su daga mukamansu ta hannun shugaban ƙasa na Miyetti Allah Kautal H**e Bello Bodejo.

Wannan labarin na bogi ne, an shirya shi ne domin bata sunan waɗannan shugabanni da tuni sun yi murabus da kansu sun bar Kautal H**e, kuma sanarwar murabus ɗin nasu an wallafa ta a shafukan sada zumunta na ƙungiyar Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria.

Shugabannin uku da s**a sauka daga mukamansu sun kuma shiga Kautal Pulaaku Fulbe Association nan da nan, yanzu suna mai da hankali ne kan sabbin shirye-shiryensu na ƙungiyar domin inganta tattalin arziki, zamantakewa, siyasa da tsaron Fulani marasa galihu da masu rauni a yankunansu, don ganin an ingantawa makiyaya rayuwarsu sun amfana da romon dimokoradiyya ta fannin samar masu Ruwan Sha nasu, Dana dabbobin su, inganta ilimin yayan su, koya musu kiwon Zamani da sauran su a fadin ƙasa baki ɗaya.

Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria ba ta fito don yin gaba ko yaƙi da wata ƙungiya ba. Maimakon haka, ƙungiyar za ta mai da hankali wajen haɗa kai da sauran ƙungiyoyin Fulbe da waɗanda ba Fulbe ba domin inganta rayuwar makiyaya a fadin ƙasar nan.

Sai dai, ƙungiyar ba za ta lamunci farautar mutanenta , nuna wariya, barazana ko kai hari ga membobin ta, ko mutuncin ƙungiyar ba.

Muna kira ga shugabannin Miyetti Allah Kautal H**e da su mai da hankalisu kan shirye-shiryen ƙungiyarsu maimakon shiga rikici da ƙungiyoyin Fulbe masu son zaman lafiya da cigaban makiyaya, domin irin waɗannan abubuwa na iya lalata martabar ƙungiyar da shugabancinta.

Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria na kira ga dukkan mambobinta da su ci gaba da mai da hankali, kada su bari wani mutum ko ƙungiya su karkatar da su daga hanyar da ƙungiyar ta bi don gina martaba da mutuncin Fulbe.

Haruna Idris Bayero,
P.R.O

Suleiman Dungal
Director Media

Nura shehu
Director media na bauchi state 

Kautal Pulaaku Fulbe Association of Nigeria.

16/10/2025

Nasma nam gi gujjo kusel #

15/10/2025

Wannan gsky duk wa'ennan Mutanen banzan daka lissafo wlh bama tare da su Kai hasalima sunfi chutar da mu akan kowa a kasar Nan 👌 muna fatan Allah ya kawo mana karshen su










Aslm ina mika godiyata  wa allah subahanahu wata alah da kuma yan’ uwana fulani baki daya, ina mai muku al bishir nam ba...
15/10/2025

Aslm ina mika godiyata wa allah subahanahu wata alah da kuma yan’ uwana fulani baki daya, ina mai muku al bishir nam badajumawaba wani abu mai dadi zayriskeku anam jahar bauchi dama kasar nam baki daya da yardar allah nan gaba kadan damu samu shuwagabanni nagartattu masu ilimin addini dana zamani kuma masu sanin yakamata akan al’ummansu.

14/10/2025

Mubajahi laibane wallahi

14/10/2025

Fulani bajahilaiba fulani mutane da suke da hakuri kawayci nutsuwa kamalah da sanim yakamata amman wasu jahilan kasan nam dukkan nim abin da ya taso saisuce ai fulani komai ajinginamusa haba sai kace mu ba muslmaibane dan allah day na irin haka allah ya samuda ce 🙏🙏 阿木爷爷Grandpa Amu Adamu Ahmad Gidado Gimbiyar Hausa

13/10/2025

13/10/2025

Mu alfahari da wannam yar 阿木爷爷Grandpa Amu

13/10/2025

Gimbiyar Hausa Maryam Aliyu Matawalle Aliyu Abubakar

13/10/2025

Allah wallu pulaaku fulbe associate
of Nigeria

Address

Yelwan Tudu Market
Bauchi
740102

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kautal Pulaaku Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share