30/01/2026
“A yau Sen.Bala Muhammad ya kaddamar da tambarin cikar Jihar Bauchi shekaru 50 ( 50) a Fadar Gwamnati da ke Bauchi, wanda hakan ke nuna fara ayyukan bukukuwan cikar jihar shekaru 50 a hukumance.
Wannan kaddamarwa ta gabaci jerin manyan bukukuwa da aka tanada a fadin jihar, ciki har da shirye-shiryen al’adu, bukukuwan gargajiya, Durbar na gargajiya, da sauran ayyukan tunawa da wannan muhimmiyar shekara.
Kamar yadda ya bayyana a wajen taron, wannan bikin cikar shekaru hamsin (Golden Jubilee) babban mataki ne a tarihin Jihar Bauchi. Lokaci ne na tunani da sabuntawa, kuma yana jaddada alhakin da muke da shi ga zamanin yanzu da na gaba.
Saboda haka, yyi kira ga dukkan al’ummar jihar da su sake tabbatar da jajircewarsu ga hadin kai, zaman lafiya da ci gaba, domin mu yi aiki tare wajen gina Jihar Bauchi mai karfi da wadata ga al’ummomi masu zuwa.”