Saye Online Reporters

Saye Online Reporters Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Saye Online Reporters, Media/News Company, Saye Bichi Local Government Area, Bichi.

An bude wannan gidan jaridane domin Kawo Maku labarai Akan Al'amuran Yau da Kullum har zuwa kasashen ketare, domin ji da Sanin Inda aka Kwana Da Kuma Inda Tashi ta Hanyar Kawo maku sahihan labarai

Founder/CEO
Hamza Danladi Saye

DEAR APPLICANT DA DUMI-DUMI: Za a Gudanar da Jarabawar CBT ga masu sha’awar shiga aikin Ɗan Sanda daga 28 Zuwa 30 ga Afr...
18/04/2026

DEAR APPLICANT
DA DUMI-DUMI: Za a Gudanar da Jarabawar CBT ga masu sha’awar shiga aikin Ɗan Sanda daga 28 Zuwa 30 ga Afrilu -inji PSC

Daga Saye Online Reporters

Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta kasa ta ayyana ranakun 28 zuwa 30 ga Afrilu, 2026 domin gudanar da jarabawar CBT ga masu neman shiga aikin ‘yan sanda a faɗin Najeriya.

Jarabawar na zuwa ne bayan tantance lafiyar jiki da takardu da za a kammala a ranar 18 ga Afrilu. Rundunar ‘yan sandan ta ce CBT muhimmin mataki ne domin zaɓen waɗanda s**a cancanta.

An bayyana cewa tsawon lokacin jarabawar zai bambanta daga jiha zuwa jiha, gwargwadon yawan ‘yan takara da cibiyoyin CBT da ake da su.

An buƙaci masu neman aikin su jira sanarwar wurare da jerin sunayen waɗanda s**a cancanta, tare da gujewa jita-jita, domin duk bayanai za su fito ne ta hanyoyin hukuma.

Wa kuke wa sha’awar samun aikin dan sanda a cikin abokanan ku

LIKE // SHARE & FOLLOW PLEASE

DAGA JIHAR NIGER AREWACIN NIGERIA'Yan ta'adda sun sa abin fashewa s**a tarwatsa wasu sassa na gadoji guda biyu da ke had...
24/03/2026

DAGA JIHAR NIGER AREWACIN NIGERIA

'Yan ta'adda sun sa abin fashewa s**a tarwatsa wasu sassa na gadoji guda biyu da ke hada Gundumar Wawa da Gundumar Luma a karamar hukumar Borgu Jihar Niger

Babban dalilin da ya sa 'yan ta'adda s**a karya gadojin shine domin su raunata aikin Sojojin Nigeria da suke sintiri a cikin dajin Kainji da sauran dazuka da sai an bi ta wadannan gadoji guda biyu

Gadojin suna da matukar muhimmaci ga aikin tsaro da yaki da ta'addaci, idan ba'a samu zirga-zirgan Sojoji da sauran hukumomin tsaro ba to wannan zai bawa 'yan ta'adda damar kaddamar da munanan hari na ta'addanci da garkuwa da mutane a jihar Niger

Muna rokon Allah Ya kare jihar Niger da Arewa gaba daya daga sharrin 'yan ta'adda....

Gurɓacewar Yanayi Na Neman Kawo Cikas Wajen Ganin Jinjirin Watan Ƙaramar Sallah A Saudiyya. Duba Da Yanayin Rashin Na Ra...
18/03/2026

Gurɓacewar Yanayi Na Neman Kawo Cikas Wajen Ganin Jinjirin Watan Ƙaramar Sallah A Saudiyya.
Duba Da Yanayin Rashin Na Rashin Kyawun Yanayi Na Sararin Samaniya A Kasar Ta Saudia Hakan Yana Zamo Wani Babban Kalubale Ga Hukumomin Kasar Saudia Wajen Lalubo Jinjirin Watan Duk Da Nagartattun Kayan Aikin Da Suke Amfani Dashi.

A DALILIN KULLE MASHIGAR RUWAN HORMUZKasar Sri Lanka anka ta sanar da duk ranar laraba a matsayin ranar hutu a kasar ind...
18/03/2026

A DALILIN KULLE MASHIGAR RUWAN HORMUZ

Kasar Sri Lanka anka ta sanar da duk ranar laraba a matsayin ranar hutu a kasar inda aka umarci makarantu su rufe, maaikatan gwamnati da private duk su zauna a gida sannan duk wasu zirga zirgar da bata shafi zuwa asibiti ba an bukaci da kada ayita a kasar saboda a rage yawan man fetur din da kasar ke bukata, sun ce zuwa nan gaba kadan hutun zai koma kwana uku a sati.

Kasar Thailand ta buƙaci al'ummar kasar da su fara yin tattaki akan tituna idan zasu tafi wajen aiki ko makaranta da kasuwa don hakan ya rage yawan bukatar man fetur da zasuyi a motocinsu.

A kasar Myanmar an kafa dokar sau uku zaka iya amfani da motar ka a kowanne sati inda aka buƙaci al'ummar su koma amfani da motocin haya idan zasu tafi harkokin su.

Bangladesh ta sanar da katse hasken lantarki na wasu awannni sak**akon rashin wadalar man fetur da Gas din da zaa zubawa injinan dake samar da hasken lantarki na kasar.

A kasar Vietnam hukumomin gwamnati da private sun nemi maaikata da su dinga aiki daga gida sau biyu a kowanne sati ta yadda hakan zai ragewa su maaikata yawan man fetur da zasu bukata domin zuwa aiki, wadanda aikinsu ya zama dole an nemi su koma amfani da kekuna wajen zuwa aiki.

Ana sa ran kasashe masu yawa musamman a Turai suma zasu fada irin wannan halin ko sama dashi idan har Mashigar ruwan Hormuz ta ci gaba da zama a kulle zuwa sati mai zuwa.

Zuwa yanzu Iran ta nunawa duniya cewa dakarunta a shirye suke wajen dakatar da harkokin tattalin arzikin duniya ta hanyar kulle mashigar ruwan Hormuz, tun da dama tun a farko tasha bayyana cewar kada a kuskura akai mata hari domin zata dauki mataki idan aka kai mata harin, amma Amurka tayi kunnen kashi ta janyowa duniya matsala.

Malam Alireza Tangsiri YaceYa rantse da Allah zasu kyale duk wani jirgin ruwan dakon man fetur ko iskar gas da ya samu n...
11/03/2026

Malam Alireza Tangsiri Yace
Ya rantse da Allah zasu kyale duk wani jirgin ruwan dakon man fetur ko iskar gas da ya samu nasarar shawo kan jirgin ruwan Amurka na USS Abraham Lincoln akan yayi masa rakiya ta Strait of Hormuz...

Duk jirgin ruwan da ya samu nasarar shawo kan Amurka ta turo jiragen ruwan yakinta domin suyi masa rakiya ta mashigar ruwan Hormuz to wannan jirgin zai shige lami lafiya kuma zasu cigaba da bashi damar shigewa kyauta har abada

A takaice ku kawo mana jiragen yaƙin Amurka zuwa mashigar ruwan Hormuz ku samu cikekken yancin shigewa

MU NA DA HANKALI BA MAHAUKATA BANE MU...Tsohon Prime Minister na Qatar Hamad bin Jassim bin Jaber Al Thani yace...Amurka...
09/03/2026

MU NA DA HANKALI BA MAHAUKATA BANE MU...

Tsohon Prime Minister na Qatar Hamad bin Jassim bin Jaber Al Thani yace...

Amurka tazo ace tashin farko kasar Qatar da sauran kasashen gabas ta tsakiya zasu shiga yaki da Iran sak**akon hare haren da Iran ke kaiwa a sansanin sojojin Amurka dake kasashen, wanda yin hakan zai bata damar da zata yi cinikin manyan mak**an da mu musulmi zamu halaka junanmu...

Bayan mun halaka kammu mu da Iran sai Amurka take goyawa Izra@ila baya wajen kafa Greater Izr@ael da suke burin kafawa...

Tabbas an samu saɓani tsakaninmu da Iran sak**akon hare haren da tayi a ƙasashen mu, amma fa laifin namu ne tunda mune muka sauke Amurka a kasashenmu sannan ita Amurka take amfani damu wajen kaiwa Iran hari...

Ba zamu taba shiga yaki da Iran ba insha Allah domin yan'uwanmu ne musulmai

PhotoNews: Today, 9th March 2026, the recruitment screening exercise of Police Constables begins at 0700hrs in Police Of...
09/03/2026

PhotoNews: Today, 9th March 2026, the recruitment screening exercise of Police Constables begins at 0700hrs in Police Officers' Mess Bompai Kano. The head of the Police recruitment team, DCP Habibu Rabiu alongside the head of the team from Police Service Commission (PSC) led by Alhaji Ibrahim Maikudi briefed the Officers scheduled for the screening, calling on them to exhibit a high level of professionalism by ensuring a credible and transparent process. Also, the Command's Public Relations Officer, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ANIPR, MNISMA, FNACSP addressed the candidates clearly stating that the exercise is free. The Physical and Credentials screening exercise is ongoing without any hitch.

Labari Cikin Hotuna: A yau, 9 ga Maris 2026, an fara aikin tantance masu neman shiga aikin 'yan sanda (Police Constables...
09/03/2026

Labari Cikin Hotuna: A yau, 9 ga Maris 2026, an fara aikin tantance masu neman shiga aikin 'yan sanda (Police Constables) da karfe 0700hrs a Police Officers' Mess Bompai Kano. Shugaban tawagar daukar ma’aikatan ‘yan sanda, DCP Habibu Rabiu, tare da shugaban tawagar daga Police Service Commission (PSC) wanda Alhaji Ibrahim Maikudi ke jagoranta, sun yi wa jami’an da aka tsara za su gudanar da tantancewar bayani, inda s**a bukace su da su nuna babban matakin kwarewa ta hanyar tabbatar da sahihin tsari mai gaskiya da bude ido. Haka kuma, jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ANIPR, MNISMA, FNACSP, ya yi jawabi ga ‘yan takarar inda ya bayyana a fili cewa wannan aikin kyauta ne. A halin yanzu ana ci gaba da tantance jiki da kuma takardu ba tare da wata matsala ba.

AMFANIN GWANDA!!!! Gwanda tana da abubuwan da jiki yake buqata da dama, ga dai amfaninta ga fata nan mun fada, masamman ...
09/03/2026

AMFANIN GWANDA!!!!

Gwanda tana da abubuwan da jiki yake buqata da dama, ga dai amfaninta ga fata nan mun fada, masamman ta wajen kiwon lafiya, yadda fatar za ta yi qarfi, lafiya da kyawun gani, gashin kai kuma ya yi santsi da qarfi, ba zai riqa kakkaba ba, namiji bai damu da sanqo k**ar yadda mace ta dauke shi ba, don in ma bai da shi yana iya yin tal-kwabo ya fita da kan a haka, ita kuwa abin kunya ne koda kuwa a wajen gyaran gashi ne, a irin wannan matsayin Gwanda tana da rawar da take takawa ba 'yar qarama ba.

1) Hawan jini daya ne daga cikin cututtukan da suke gallabar dan adam, to Gwanda tana da Potassium mai dama, wanda shi kuma yakan taimamaka wajen daidaita jinin mai cutar, tare da barin qwaqwalwa a farke kowani lokaci.

2) Gwanda kan kyautata ganin mutum, in mutum zai iya cin yanka biyu a kullum, ganinsa zai iya zama haka ba tare da ya ragu don girman shekaru ba, wannan sabo da yawan sinadarin ne da ake zaton zai iya yin wannan aikin, bawai don ita Gwanda ce an san dole ta yi haka ba.

3) Gwanda kan taimaka wajen kyautata qwayoyin garkuwar jiki, don tana dauke da sinadarinnan na Beta Carotene wanda wannan yana daya daga cikin aikinsa.

4) Kumburi wanda ya bayyana da boyayye duk cututtuka ne da suke cutar da jikin dan adam, to Gwanda takan taimaka wajen hana kumburin kunne na dindindin ko sanyi ko zazzabin influenza.

5) Cutar zuciya ma kan yi illa, to Gwanda tana da sinadaran da suke taimakawa, tana da Nutrients mai yawa wadan da suke maganin rubabben Cholesterol, da haka sai ta yi maganin yuwuwar kamuwa da rashin bugawar zuciya, ko tsayuwar qwaqwalwa.

6) Sai kuma raunuka irin na jiki, Gwanda kan taimaka ta yadda rauni zai yi saurin hadewa ya warke, in aka yanka gwandar sai a shafe raunin da shi, a nan muna ba da shawarar cewa duk raunin da mutum zai yi, ya yi qoqarin samun likita don karbar allurar Tetanus, wannan kuma wata cuta ce mai kisa, wace take saurin shiga jikin dan adam da zarar ya yanka, ko ya soke ko kuma ya yi wani rauni, in har ba a yi maganinta da gaggawa ba to akwai yuwuwar za ta yi kisa, Gwanda ba ta da amfani a nan.

7) Wani lokaci akan sami qurarraji ko maruru, wadan da s**an yi ta damun mutum na tsawon lokaci, to a nan sai mutum ya sami gwandarsa ya nuqe ta, ya hada ta da kindurmo ya shafa a wurin da marurun yake gallabarsa har sai ya bushe, in Allah ya so za a ga bambanci cikin gaggawa.

8) Akwai kuma ciwon s**ari, duk da cewa Gwanda tana da zaqi amma kuma tana taimakawa wajen sassauta matsalar, alal aqalla ba ta a cikin manyan 'ya'yan bishiyar da ake hana mai cutar ya ci ko ya sha.

9) Hanji masamman babban na qarshe wanda daga shi ba-haya yake fita waje, wanda ake kira a Turance Colon yakan kamu da cutar Cancer to Fibres din dake cikin Gwanda suna da qarfin da za su iya yin maganin wannan Cancer din kuma su ba hanjin kariya, banda wannan ita ma 'ya'yanta s**an taimaka wajen magance wasu matsalolin sabo da sinadaran dake cikinta, sai dai ita 'ya'yanta daci ne a su ba k**ar sauran 'ya'yan bishiyar da muka ambato a baya ba, 'ya'yan suna dauke da Vitamins da sauran sinadaran da za su taimaka mata wajen ida nufi.

Ga wadan da s**a yi shaye-shaye har ya wuce qima hantarsu ta lalace 'ya'yan Gwanda kan taimaka, in mutum yana shaye-shaye hantarsa kan tattare ne ta cure wuri guda, sai ta gaza yin aikinta k**ar yadda ya dace, to 'ya'yan Gwanda kan janye cutar matuqar za a dena dibar barasar, sai mutum ya sami 'ya'yan gwanda busassu ya niqe su, ya riqa sha a cikin lemon tsami, zai riqa sha ne a kullum da tazarar lokaci kafin ya ci abinci, haka zai yi har zuwa wata guda cur, don gurbacewar ba ta fita lokaci daya kacal, da haka in sha Allahu sai za a ci nasara, sai dai in mutum ya koma dibar barasar wata qila ba zai jima a duniya ba.

Kamar dai yadda muke fadi ne a kullum, matsalolimmu shi ne in aka sami dan bishiya guda to cin qoshi za a masa, wanda hakan kuwa matsala ce ga jikin dan adam, babu ko shakka rashin cin wadannan albarkatun gonar jikkunammu s**an shiga wani yanayi wanda cuta qarama in ta cafki mutum sai ta kwantar da shi, to amma in aka ci sama da yadda jikin yake buqata nan ma wata matsalar ce ta masamman, sai mutum ya yi qoqarin daidaita abincinsa don kaucewa da na sani a cikin rayuwa, Allah ya ba kowa lafiya amin, sai mu tara gobe in sha Allah don jin matsalolin gwanda, kusan ta fi duk wata dan bishiya matsala

Duk da cewa Gwanda tana da dumbin amfanin da muka ambata a baya, sai dai ba ta rasa nata matsalolin na masamman, galibin wadannan matsalolin ba a iya magance su in ba an nisanci ci gaba da dibanta ba

1) Abu mafi sauqin fadi shi ne Gwanda ga mace mai ciki hatsari ce, don za ta iya haifar da barin cikin, tun ba yau ba a baya can ma matan da ba sa son ciki, ko don sabo da hanyar da ya zo, ko ba a buqatarsa s**an zubar da shi ta wajen yin amfani da Gwanda, i tabbas nunanniyar Gwanda ta fi zama daidai ga mace sama da danya, don danyar takan haifar da matsalolin mahaifa sabo da sinadarinnan nan na Latex, shi wannan sinadarin zai iya haifar da bari ko haihuwar da ba a shirya ba, ba ma wannan kadai ba zai yuwu dan a haifo shi da tawaya ko ma ya fito a mace.

2) In da za a lura tun farkon darasin muna kwadaitarwa ne da cewa a riqa taqaita kowani dan bishiya ne da ake son ci, don mutum bai san wanda sinadarin cikinsa in ya hadu da na jikinsa qila ya wahalar da shi ba, in aka lura wani zai ce maka in ya ci kaza dole kaza zai same shi, ba camfi ba ne, tsarin jikinsa din ne akwai wasu abubuwan da ba sa haduwa da dan bishiyar shi bai sani ba, Gwanda in aka sha ta da yawa za ta iya haifar da Carotene a cikin jini, samun Beta Carotene a Gwanda zai iya haifar da canjawar launin fatar.

3) Haka kuma za ta iya kawo matsala ga mutum a wajen numfashi, sabo da samuwar Enzyme a cikinta, 'yan matsalolin za su shafi: Matsala a wurin numfashi, munshari, numfashin ya riqa samun cisgiya wajen shiga ko wurin fita, Asthma da kuma mura, koda yake ana iya magance mura da lemon tsami, ko citta, hatta kindirmo yana iya magance mura, sabo da sinadarin Magnesium dake cikinsa, qila ma shi ya sa fulani duk da zaman jeji, da rashin cikakken kariya daga sanyi, amma ba su ne s**a fi kowa kamuwa da muran ba.

4) Za ta iya haifar da tsakwankwanin qoda, domin Gwanda qwara daya tal tana da Vitamin C 60mg, wato sama da 300% na abin da malaman kiwon lafiya suke ba da shawara da shi a rana, shi kuwa Vitamin C yakan zama babbar garkuwa a jiki, ya ba da kariya daga cutar kansa, da hauhawar jini, ko ma jinin ya riqa gardama ta wurin nuna raguwa ko zamantuwa daidai, amma duk da haka yin overdose na Vitamin C zai iya zama Poising har ya qarisa zuwa tsakwankwanin qoda, dole mutum ya riqa sara yana duba bakin gatari.

5) Gwanda za ta iya wahalar da tumbi, wannan duk muna nufin ne in aka sha ta har ta wuce qima, wani in ya sa ta a gabansa sai ya ga iyakarta, tabbas tana haifar da matsala a tumbi, k**ar radadin tumbi, kumburin ciki, tashin zuciya da koke-koken ciki na ba gaira ba dalili, su galibin irin wadannan 'ya'yan bishiyar akan dan ci su ne daidai gwargwado a tsakanin abinci guda biyu, ba lokacin cin abinci ko nan take bayansa ba, duk da ka ji matsala to lallai an wuce gona da iri a ciki.

6) Ba wai ciki ba hatta ga mai shayarwa, yana da matuqar amfani ta san halin da take ciki, don malamai sun sami sabani a ciki, a gabashin Asia likitoci s**an ba masu shayarwa shawarar shan Gwanda don samun nono ga yaro, a wasu qasashen kuma akan gargade su sabo da samun Enzymes a ciki, a taqaice wannan babu wata matsaya qwaqqwara dake nuna cewa a guje ta din, a nan muna ba da shawarar cewa a kusanci malaman lafiya don samun cikakkiyar shawara.

7) In ya kasance mutum yana fama da mummunar cuta k**ar Asthma, ina ba da shawarar ya bi a hankali wajen dibar Gwanda, ni a ganina tunda akwai wasu 'ya'yan bishiyar ba ita ba gwara ma ya koma wata, wani lokacin akan sami wasu matsalolin ga wanda bai tafiya daidai da ita, k**ar kumburi a baki, a fuska, qaiqayi a cancan cikin baki da maqogwaro, a qasan harshe da baki, jiri, ciwon kai, kururuwan ciki, matsalar numfashi, zafi wurin hadiya da radadin ciki.

8) Idan mutum ya zarce gona da iri wajen yin amfani da ganyen Gwanda ko 'ya'yanta ko ma ita kanta zai iya samun matsala wurin yin numfashi da qyar, wannan kam in har yanayin bai canza ba, to ba shakka an k**a hanyar aukawa cikin matsala.
9) Ya zama dole ga wadan da suke fama da matsalolin zuciya sudan guji Gwanda, don za ta iya haifar musu da jinkiri wajen bugawar zuciya, ko tsarin bugawar kwata-kwata ya canza.

10) Wanda yake fama da zawo ya k**ata ya guji gwanda, k**ar yadda ya k**ata ya nisanci sauran 'ya'yan bishiya.

11) Haka yaron da bai kai shekara daya ba bai dace mamansa ta tura masa gwanda ba, don kashinsa yana iya yin kauri ya sha wahala a ciki, ko ma ya yi fama da atini, don haka ina ba wa mai shayarwa shawarar ganin likita kafin danta ya fara shan Gwanda

A matsayina na mai bincike kan tsaro da fasaha (Technology-Driven Security Analysis), kuma dalibin Cybersecurity akwai h...
08/03/2026

A matsayina na mai bincike kan tsaro da fasaha (Technology-Driven Security Analysis), kuma dalibin Cybersecurity akwai hanyoyi masu yawa da masana suke amfani da su wajen nazarin hoto ko bidiyo domin gano inda aka dauke shi, bawai kawai ta kallon hoton bane za'a gano inda aka dauke shi ba, bincike ne mai zurfi akeyi wanda ake kira Digital Forensics da Open-Source Intelligence (OSINT)...

Lokacin da aka samu hoto ko bidiyo k**ar wannan na matashin da ke rokon a taimaka masa, masana kan fara da abin da ake kira visual intelligence analysis, wato nazarin abubuwan da ake gani a cikin bidiyon.

Na farko akwai abin da ake kira Environmental Pattern Analysis, masana kan kalli irin yanayin dake cikin hoton tun daga nau’in bishiyoyi, yanayin kasa (soil texture), launin kasa, da irin tsirran da s**a bayyana a cikin bidiyon, wadannan abubuwa na iya nuna yankin da aka dauki hoton, domin kowace jiha ko yanki na da irin tsirran da s**a fi yawa a cikinsa.

Na biyu akwai Shadow and Sun Position Analysis, idan aka duba inuwa a hoton, masana zasu iya kimanta inda rana take a lokacin da aka dauki hoton ko video din, ta amfani da ilimin solar positioning algorithms, ana iya tantance ko bidiyon an dauke shi da safe ne, ko kuma da rana tsaka ne, ko kuma da yamma ne. Sannan akwai Vegetation and Terrain Mapping, akwai manyan satellite imagery databases k**ar wadanda ake samu a taswirar tauraron dan adam, masana kan kwatanta yanayin da ke cikin bidiyon da hotunan tauraron dan adam domin ganin ko akwai wuraren da s**a yi k**a da shi.

Wata muhimmiyar hanya ita ce Metadata Forensics, wato idan bidiyon ko hoton bai rasa bayanansa na asali ba, akwai bayanai da ake kira EXIF metadata da ke boye a cikin file. Wadannan bayanan zasu iya nuna lokacin da aka dauki hoton ko bidiyon, da irin na’urar da aka yi amfani da ita, wani lokaci ma har GPS coordinates da za'a iya samu kai tsaye. Idan aka samu wadannan bayanan, to tabbas binciken zai zama mai sauki sosai. Haka kuma akwai Audio Forensics, idan aka saurari sautin da ke cikin bidiyon, ana iya jin karar tsuntsaye na wani yanki a kasa, ko karar wani abu da zai ba da wata dama mai kyau wajen gano inda yake.

Akwai binciken da muke kira Network Intelligence Tracking, idan wanda aka sace ya saka account number k**ar yadda aka gani a wannan hoton nasa, jami’an tsaro za su iya bibiyar bayanan bankin domin gano wanda ya bude asusun, wurin da aka cire kudin, da kuma IP address ko na’urar da aka yi amfani da ita. A tsarin bincike irin na Technology, ana hada duk wadannan hanyoyi ne a cikin abinda ake kira Multi-Layer Digital Investigation Model, wato hada bayanan hoto, bidiyo, taswirar tauraron dan adam, da bayanan banki domin gano wuri ko mutanen da ke da hannu a lamarin.

Saboda haka, hoto ko bidiyo ba kawai abin da za mu kalla ba ne mu ji tausayinsa kawai. Kai tsaye, a wannan bidiyon ya bada signal mai kyau da gwamnati za ta iya amfani da shi wajen ceto rayuwarsa.

Wadannan informations din a wajen masana tsaro su kan zama digital evidence da zasu iya taimakawa wajen gano inda wanda aka sace yake ko kuma gano wadanda s**a aikata laifin.

Wannan shi ne dalilin da ya sa a yau Technology, Data Analysis, da Artificial Intelligence s**a zama manyan mak**ai a yaki da laifuka a duniya, k**ar laifin garkuwa da mutane da sauran ta’addanci a kasa.

NB: Babu abinda gwamnati bata sani ba a wannan bayanin nawa, nayi bayanin ne domin mu kara fahimtar Nigeria da kyau.

Allah ya sa mu dace.

© Hamza Danladi

‎Abinda na fahimta a yanzu shine, kusan over 90% na mutanen Africa har yanzu basu ma san menene makamin Nukiliya ba (Nuc...
08/03/2026

‎Abinda na fahimta a yanzu shine, kusan over 90% na mutanen Africa har yanzu basu ma san menene makamin Nukiliya ba (Nuclear Weapon). Mostly sun ɗauka kawai normal bomb 💣 ne ko wani barkonon tsohuwa da s**a saba ji. Oga kana ji?, duk ranar da makamin nukiliya ya fashe a garin ku ko?, billahillazi ƙiyamar kaf mutanen wannan garin naku ce baki ɗaya tazo ƙarshe. Ba mutuwa kaɗai za'a yi ba, ɓacewa ne zaku yi daga doron ƙasa a cikin ƙiftawar ido daga kai har dangin ka tar da maƙotan da suke yankin ku baki ɗaya. Kalmar Nuclear tana nufin makamin ƙare dangi. A cikin second na farko da fashewar sa za ku ga wani irin haske mai tsananin zafi wanda ya fi hasken ranar daka saba gani. Haske ne da zai narkar da idon duk wani wanda ya kalla kafin ma ya yi tunanin runtse idonsa. Bangon gine-gine zasu koma gari tamkar toka cikin second 4. Daga nan wata mahaukaciyar iska zata ta biyo baya, guguwar da za ta kakkaɓe duk wasu manyan benaye da gine-gine komin ƙwarin ginin kafin ƙiftawar ido. Ƙarfen service da manyan bishiyoyi zasu karye k**ar tamkar ashana sannan zasu rinka tashi sama k**ar takardu. Motoci zasu narke su zama gari sannan su haɗe da jinin mutane saboda zunzurutun masifa.

‎Duk wani abin da kuke alfahari da shi na ginin zamani zai zama tarkacen da bazai taɓa yin amfani ba in less than 1 minute. Duk da Haka fa wannan shi ne farkon masifar saboda bayan hayaƙi ya turnuƙe ko'ina, nan take wata irin baƙar ƙanƙara zata fara faɗowa daga sama, guba ce mai dauke da sinadarin radiation da zai gurɓata kowane ɗaki da kowane irin lungu dake kan radius na yankin. Ruwan fanfo zai koma sanadin mutuwa, ƙasar da kuke shuka abinci a kanta zata koma ƙabarin da babu damar binne kowa. Waɗanda s**a samu tsira da ransu za su rinka yawo idanunsu a makance, sannan fatar jikinsu zata ɗaɗɗago saboda ƙarfin radiation na Nuclear power. Ita kanta wannan Ranar da kake gani za ta ɓace ne a bayan wani baƙin gajimare na tsawon lokaci, damina za ta tsaya, iska za ta daskare, amfanin gona zai mutu sannan daga ƙarshe kuma yunwa za ta kwashe duk sauran mutanen da wutar ba ta gama cinyewa ba ɗaya bayan ɗaya. Daga wannan ranar har 'ya'yan da za'a haifa a wannan ƙasar ko wannan yankin zasu zo ne da nakasa da cututtukan da basu san asalinsu ba. Oga makamin nukiliya bawai iya a birni ko ƙasa yake rushewa ba, asalin jinin ɗan Adam yake lalatawa tun daga tsatson ka har illa masha Allah. Universal double standard ne da ba yadda ka isa dashi indai an sakar maka shi. Idan har yanzu kana tunanin makamin nukiliya ƙaramin ɗan iska ne, oga ka koma ka karanta tarihin nukiliyar da America ta jefawa Japan a yaƙin duniya na biyu.

Sudan has delivered a strong warning to the international community, saying it could join the conflict on Iran’s side if...
07/03/2026

Sudan has delivered a strong warning to the international community, saying it could join the conflict on Iran’s side if the United States and Israel launch a full ground invasion. This statement adds a new layer of tension, potentially expanding the war beyond the Middle East and introducing an African dimension to the crisis.

Sudan has historically balanced complex relationships with Western nations and regional powers, but this announcement suggests a shift toward closer alignment with Tehran. The warning comes shortly after reports that U.S. military aircraft arrived in Iraq carrying equipment meant for Kurdish forces, which could play a role in any potential advance toward Iranian territory.

If Sudan becomes directly involved, military strategists would need to consider a much wider battlefield. Key routes such as the Red Sea and nearby maritime corridors could face new security risks. At the same time, global opposition to the conflict continues to grow, with Spain’s Prime Minister Pedro Sánchez criticizing the war as “disastrous” and refusing to participate in military support.

For ordinary people around the world, Sudan’s possible entry raises serious concerns about trade routes, migration flows, and regional stability. A conflict involving multiple nations could significantly increase the already enormous financial and humanitarian costs, which analysts estimate at around $1 billion per day.

Sudan’s warning appears aimed at discouraging a ground invasion that U.S. officials reportedly believe could extend for months. As Washington continues to reaffirm its support for Israel, the possibility of new countries entering the conflict makes diplomatic solutions far more difficult to achieve.

Address

Saye Bichi Local Government Area
Bichi
703101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Saye Online Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share