10/06/2025
Sabuwar Duniya - Karfin Jama'a
Wannan rubutun na yara ne. Ku yi tunanin akwai mutane 469 a makarantar ku. Mu kira su Manyan Mutane.
Kowanne Babban Mutum yana karɓar albashin ₦40 miliyan a kowane wata.
Mu lissafa…
₦40,000,000 × 469 = ₦18,760,000,000 a kowane wata
Wannan yana nufin ₦18.7 biliyan naira — duk bayan kwana 30 — Abunda ake baiwa wadannan Manyan Mutane kennan.
Yanzu mu dan yi lissafi da waɗannan kuɗade kamar muna koyon lissafi…
1. Gina Asibiti?
• Asibiti guda daya a kauye = ₦200 miliyan
• Da ₦18.7 biliyan, za ka iya gina:
Asibitoci 93 a kowane wata!
2. Gina Makaranta?
• Makaranta guda a kauye = ₦150 miliyan
• Da ₦18.7 biliyan, za ka iya gina:
Makarantu 124 a kowane wata!
3. Biyan Albashin Malamai?
• Malami na karɓar ₦70,000 a wata
• Da ₦18.7 biliyan, za ka iya biyan:
Malamai 267,000 a wata!
(Wannan ya fi yawan malamai a Arewacin Najeriya.)
Amma Maimakon Haka…
• Yara na zaune a kasa.
• Rufin makarantu sun lalace.
• Babu Malamai, kuma kadan da ake da su na roƙon albashi.
• Asibitoci babu magani.
• Kuma mutum ɗaya yana karɓar fiye da abin da malamai 500 suke samu a kowane wata.
To, Ka Tambayi Kanka, Yaron Kirki:
Idan mutane 469 na zaune a kan ₦18.7 biliyan a kowane wata —
Amma ajinka babu kujera…
Ina kujerarka ta tafi?
Mu ‘Yan Gaskiya na kira a mayar da albashin duka ‘yan majalisu iri daya da malaman makarantar firamari.
Mu ‘Yan Gaskiya na kira a cire duka kujerun da ke cikin majalisun kasa - ‘yan majalisa su koma zama a kasa ko tsayawa a tsaye har sai kowani yaro ya samu wajen zama a makarantun gwamnatin Najeriya.
Dan Bello yace:
Idan yaro daya na zaune a kasa — babu wanda ya cancanci zama a ofis.
Karfin Jama’a - Sabuwar Duniya