Comr. Ammar Bichi

Comr. Ammar Bichi Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Comr. Ammar Bichi, Digital creator, Gandun Alhaji Kabiru Abubakar Titin FCE Bichi, Bichi.

06/12/2023

Zamu Rika shiga giveaway Don samun na data, Don Alfarmar Annabi (S.A.W) 💖, zamu raba Kati in mun samu nasara

A gobe jumma'a kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan jihar Kano. Wa kuke yiwa fatan Nasara a tsakanin...
16/11/2023

A gobe jumma'a kotun daukaka kara za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan jihar Kano. Wa kuke yiwa fatan Nasara a tsakanin su?

Yafa sha she-gen bugun tsiya, dole kungiyar kwadago ta fantsama yajin aiki, domin a kwato mishi 'yanci 🙂 A rayuwar Gwagw...
15/11/2023

Yafa sha she-gen bugun tsiya, dole kungiyar kwadago ta fantsama yajin aiki, domin a kwato mishi 'yanci 🙂

A rayuwar Gwagwarmayarka, sau nawa jami'an tsaro s**a taba yi maka dukan tsiya 💁‍♂️

14/11/2023

Kungiyar ma'aikatan lafiya ma, ta fantsama cikin yajin aikin sai baba-ta-gani.

YANZU-YANZU :An Gudanar da Adduo'in domin Nasarar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a Shari'ar da za'a gabatar daga Karamar Hukuma...
13/11/2023

YANZU-YANZU :An Gudanar da Adduo'in domin Nasarar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna a Shari'ar da za'a gabatar daga Karamar Hukumar Karaye.

13/11/2023
Yadda magoya bayan Gawuna s**a gabatar da Sallah tare da Addu'ar Neman a nasara a Kotun daukaka kara. A Karamar hukumar ...
13/11/2023

Yadda magoya bayan Gawuna s**a gabatar da Sallah tare da Addu'ar Neman a nasara a Kotun daukaka kara. A Karamar hukumar Gwale dake birnin Kano.

YANZU-YANZU. :Kotu Ta Umarci A Liƙawa Rarara Sammaci A Dukkannin Gidajen SaBabbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke La...
13/11/2023

YANZU-YANZU. :Kotu Ta Umarci A Liƙawa Rarara Sammaci A Dukkannin Gidajen Sa

Babbar Kotun Majistiri, mai lamba 1, da ke Lafia, a jihar Nasarawa, ta umarci a liƙawa Fitaccen Mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara, takardar sammacin kiran Kotun, a dukkannin gidajensa, da ke faɗin Najeriya.

Kotun ta bada wannan umarni ne, sakamakon gaza samunsa fuska-fuska domin miƙa masa takardar sammacin da Kotun ta aike masa, kan ƙarar da Fitaccen Ɗan Jaridar nan (Mamallakin Jaridar Rariya Online), Alhaji Sani Ahmad Zangina, ya shigar da shi a gabanta, ya na neman Kotun ta sanya a tsare shi, bisa wasu kalamai da ya furta da Alhaji Sani Zanginan ke musu kallon kalaman tunzuri.

Lauyan mai ƙara, Barista M.A Barde, shi ne ya tabbatar da wannan umarni da Kotun ta bayar, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, jim kaɗan bayan fitowa daga zaman Kotun, a yau (Litinin).

Kotun ta kuma sanya, ranar 4 ga watan gobe na Disamba, a matsayin ranar komawa Kotun, domin cigaba da sauraron shari’ar.

Sai dai, a wata tattaunawar wayar tarho da Jaridar ATP Hausa ta yi da Mawaƙin, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya bayyana cewar, takardar Kotu bata riske shi ba. Amma zai sanar da Lauyansa, domin ya bincika.

Idan za a iya tunawa, Mawaƙi Rarara, ya furta wasu kalamai da ake ganin cin zarafi ne, ga muhibbar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ya yin wani taron Manema Labarai da ya gudanar, a jihar Kano, tun a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata. Inda me ƙara (Sani Ahmad Zangina) ya kasance daga jerin mutanen da ke kallon kalaman na Rarara a matsayin kalaman tunzura al’umma.

YANZU - YANZU: Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’i...
13/11/2023

YANZU - YANZU: Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta dakatar da Jarumi Abdul Saheer da aka fi sani da Malam Ali Kwana Casa’in daga Finafinan Hausa har tsahon Shekaru biyu.

Hukumar tace hakan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da aka yi a kansa na cewa yana yaɗa bidiyon batsa a kafafen sada zumunta.

Hukumar ta ce ta gayyace shi amma ya bijirewa amsa gayyatar ta.

KU JI RABO: Musulunci Ya Samu Karuwa Shararriyar ‘Yar TikTok  A Kasar Amurka Mai Suna  Megan Rice Ta Musùlùmai Ta Karbi ...
13/11/2023

KU JI RABO: Musulunci Ya Samu Karuwa Shararriyar ‘Yar TikTok A Kasar Amurka Mai Suna Megan Rice Ta Musùlùmai Ta Karbi Addinin Musùlúnci, Jim Kadan Bayan Duba Inda Allah Yake Magana Akan Isra*'ila A Cikin Al'qur*ani Mai Tsarki.

Wane Fata Ku Yiwa Megan Rice.?

13/11/2023

MTN sun Dawowa da kowa bashin shi, kowa ya duba Balance din shi.

WATA SABUWA: Mafiya yawan masu shirya Finafinan Hausa su na Promoting ɗin abubuwa uku ne, wasu káruwańci, wasu kawalci, ...
13/11/2023

WATA SABUWA: Mafiya yawan masu shirya Finafinan Hausa su na Promoting ɗin abubuwa uku ne, wasu káruwańci, wasu kawalci, wasu kuma ɗaukaka.

Jarumi kuma mawaƙi, Abdullahi Amdaz, ya bayyana haka ne ranar Litinin ya yin wata ganawa ta musamman da hukumar Hisbah tayi da ƴan Kannywood.

Me zaku ce ?

12/11/2023

Ance yau MTN sun fara dawowa da mutane bashukan da suke bin su. Kuyi checking balance ku tabbatar mana, shin gaskiya ne ko karya?

Kasar Saudiyya ta karrama shugaban kasa Bola Tinubu.
11/11/2023

Kasar Saudiyya ta karrama shugaban kasa Bola Tinubu.

11/11/2023

A jihar Kogi dai APC ce kan gaba wajen samun kuri'u, duk da "Yan takarar sauran jam'iyyu suna ta korafi akan kogi ta tsakiya🤔

Dole ne INEC ta soke zaben a kananan hukumomi 5 na Kogi ta tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da...
11/11/2023

Dole ne INEC ta soke zaben a kananan hukumomi 5 na Kogi ta tsakiya. Zaben da aka yi a Okene, Okehi, Ajaoukuta, Adavi, da Ogori/Mangogo wata zamba ce da aka hada daga babban mataki na INEC – Dino Maleye.

11/11/2023

An harbe Barawon akwatin za6e har lahira, a garin ayingba na jihar kogi
Allah Ya kyauta

Address

Gandun Alhaji Kabiru Abubakar Titin FCE Bichi
Bichi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Comr. Ammar Bichi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share