30/07/2026
Kalaman Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan batun yunwa sun sake tayar da kura a faɗin Najeriya, inda 'yan ƙasa ke ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta kan halin tsadar rayuwa da wahalhalun tattalin arziki da ake fuskanta.
Yayin da wasu ke ganin bayanan shugaban sun yi daidai da halin da ake ciki, wasu kuma na bayyana cewa har yanzu jama'a na ci gaba da fuskantar matsin rayuwa, lamarin da ya sa batun ke ci gaba da zama abin muhawara a sassa daban-daban na ƙasar.