Hannat TV

Hannat TV This page is basically created in order to inculcate and to remind the good teachings of Islamic reli

Cikin Hotuna: Yadda Aka gudanar da Zagayen Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W) a FuntuaAn fara gudanar da Zagayen Maulidin ...
22/08/2026

Cikin Hotuna: Yadda Aka gudanar da Zagayen Maulidin Annabi Muhammad (S.A.W) a Funtua

An fara gudanar da Zagayen Maulidin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam a garin Funtua, Jihar Katsina, inda dubban al’ummar Musulmi s**a fito domin halartar wannan gagarumin taro na tunawa da fiyayyen halitta.

Mahalarta taron sun fito cikin farin ciki da annashuwa, suna bayyana ƙauna da girmamawa ga Manzon Allah (S.A.W), tare da yin salati da yabo gare shi.

Zagayen ya kasance cikin yanayi na haɗin kai da zumunci, inda mutane daga sassa daban-daban s**a taru domin gudanar da bukukuwan Maulidi tare da tunawa da kyawawan halaye, koyarwa da tarihin rayuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Haka kuma, an gudanar da zagayen ne cikin yanayi na nishaɗi da farin ciki, yayin da mahalarta ke ɗauke da tutoci da alamomin Maulidi, suna bayyana farin cikinsu da kuma ƙaunar da suke yi wa fiyayyen Halitta.

Wannan zagaye ya kuma kasance wata dama ga al’umma wajen sabunta tunani kan koyarwar Manzon Allah (S.A.W), da ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummar Musulmi.

22/08/2026
Bayan sallah la'asar, Maulana Sheikh Imam Prof. Ibrahim Maqari (H) tareda ƴan'uwa a masallacin madinar sayyiduna Rasulul...
22/08/2026

Bayan sallah la'asar, Maulana Sheikh Imam Prof. Ibrahim Maqari (H) tareda ƴan'uwa a masallacin madinar sayyiduna RasululLahi (S.a.w)

Muna fatan Allah Ubangiji yasa suyi ibadah cikin aminci yaƙara yarda da dukkanin al'amuran su yaƙara mana adduo'insu baki ɗaya 🤲🤍🙏

Hannat TV

Zaɓi ya Rage Naka
22/08/2026

Zaɓi ya Rage Naka

21/08/2026

Addu'ar Neman Arziki

21/08/2026

Maulana Sheikh Pro. Abba Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini

21/08/2026

Gidan Shaidan a jikin ɗan Adam,

21/08/2026

Tambaya da Amsa, daga Bakin Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini

An Yi Jana'izar Khalifa Malam Ghali Na Shehu Yahuza Zaria Da Ya Rasu Tare Da Ƴaƴansa A yau juma'a  21 gawatan Ogusta 202...
21/08/2026

An Yi Jana'izar Khalifa Malam Ghali Na Shehu Yahuza Zaria Da Ya Rasu Tare Da Ƴaƴansa

A yau juma'a 21 gawatan Ogusta 2026, bayan kammala sallar Juma'a a Babban Masallacin Juma'a dake Fadar Zazzau aka gabatar da sallar jana'izar Khalifa Sheikh Muhammad Ghali ɗan Shehu Yahuza Zariya, wanda Allah Ya yi wa rasuwa jiya sanadin haɗarin mota shida ƴan uwan sa biyu da kuma ɗansa.

Babban Limamin Zazzau Malam Ɗalhatu Ƙasim Imam ne ya jagoranci ɗunbin al'umma wajen jana'izar, wanda s**a halarta daga sassa daban-daban.

Bayan su Khalifa da suke huɗu, akwai ƙarin mutune mutane hudu da suma Allah Ya yi masu rasuwa daga unguwanni aka hada aka yi jana'izar.

Daga Aqil Abdulkadir

Address

Birnin-Kebbi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hannat TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share