09/09/2026
Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 490 ga tsohon shugaban bankin NEXIM, Orya
Kotun Daukaka Kara da ke Abuja a ranar Talata ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin Nigeria Export-Import (NEXIM Bank), Robert Orya.
Kotun ta tabbatar da hukuncin da Babbar Kotun Taraiya ta Abuja ta yanke masa, inda aka same shi da aikata laifuka 49.
Daga nan ne kotun tayanke masa hukuncin shekaru 10 a gidan yari kan kowane laifi, wanda ya kai jimillar shekaru 490. Sai dai an tsara hukuncin daurin ya zama cewa shekarun za su tafi a lokaci guda da laifukan 49.
Orya ya kasance Manajan Daraktan NEXIM Bank daga 2009 zuwa 2016. Marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ne ya nada shi a ranar 14 ga Agusta 2009, sannan tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sake nada shi a ranar 18 ga Agusta 2014.
Bayan ya bar mukaminsa, Hukumar EFCC ta gurfanar da shi a shekarar 2021 kan tuhume-tuhume 49 da s**a shafi karɓar kuɗi ta hanyar yaudara, jabun takardu da damfarar kuɗin advance fee, wanda ya kai kimanin Naira biliyan 2.4.
A ranar 5 ga Fabrairu 2026, Kotun FCT High Court da ke Abuja ta same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin shekaru 490 a gidan yari.
Orya bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya garzaya Kotun Daukaka Kara yana neman a soke hukuncin da aka yanke masa.
Sai dai a hukuncin da s**a yanke baki ɗaya, alkalai uku na Kotun Daukaka Kara ƙarƙashin jagorancin Justice Muhammed Danjuma, tare da Justice Ntong Ntong da Justice Ele Enenche, sun ce kotun farko ta yi daidai.
Justice Danjuma ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin Orya ba tare da wata shakka mai ma'ana ba.
Kotun ta ce daukaka karar ba ta da wani tushe, don haka ta yi watsi da ita, tare da tabbatar da hukuncin Kotun FCT High Court na ranar 5 ga Fabrairu 2026.