08/04/2024
Domin masu tambaya Ga amsa Nan 👇
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_
_*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU.*_
¤═════۩۞۩═════¤
_Wankan Janaba yana da *siffa guda biyu:*_
::
_*1- Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar),*_
_*2-Akwai kuma wacce ake kira 'siffatu k**al' (ta k**ala).*_
:
_*Wankan Janaba* a siffar sa ta k**ala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:_
_zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa)_
_wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba,_
:
_to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban,_
_bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka._
:
_To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro._
_Wannan ita ce siffa ta k**ala a wankan janaba._
_In wankan *janaba* ne haka zakayi, in na *haila* ne haka za