Daddy Ahmad ibn taimiyya

Daddy Ahmad ibn taimiyya Marubucin labari tare da wa'azantuwa, hadi da tallata hajar ku idan kuna so

DUNIYAR ALJANNU      KASHI NA FARKO                Babi na ukkuMai gari yasa aka k**a masu gadi ayi binciken su Ba'a gan...
02/08/2024

DUNIYAR ALJANNU
KASHI NA FARKO
Babi na ukku
Mai gari yasa aka k**a masu gadi ayi binciken su
Ba'a gane komi ba kwatsan wata rana mai gari k**ar ance tashi kaje ana kiran ka
Sai ya tashi sai gonar sa yana yawa tawa shi kadai can tsakiyar gona yaci karo da wani katon rame sai ya shiga ciki, yagga rame yaki karewa tafiya dai yakai naka ya bude baki yana mamaki tsoro ya k**ashi kada dai ace aljannu ne s**ayi ramen nan har yaso ya koma sai dai yacce duk abinda Zai faru ya faru sai yaga karshen ramen nan, ya cigaba da tafiya hadda zama yana hutawa can dai cikin ikon Allah gashi karshen rame kuma rame ya kare karshen gonar yaran nan su ukku
Mai gari babu abinda ya fara sai kuka gadin sa ya zama na banza
Abinka da yarannan kuma dadi na dasu suko idan s**ayi ma 6arna basu zuwa ko ina domin basu tsoron komi duk abinda zaka musu sai dai kayi musu
Amma da s**a san mai gari ne sai da s**ayi sati daya basu garin nan domin sun san yafisu iskanci

Follow us https://www.facebook.com/profile.php?id=100070768062324
Kuyi search din
Daddy Ahmad ibn taimiyya

A KOWACE RANA DAN ADAM YANA HADUWA DA JARABAWA GUDA UKU (3)1. JARABAWA TA FARKO: Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhuma...
25/07/2024

A KOWACE RANA DAN ADAM YANA HADUWA DA JARABAWA GUDA UKU (3)

1. JARABAWA TA FARKO: Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka. Idan kudinsa ya ragu zai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.

2. JARABAWA TA BIYU: Kullum yana cin arzikin Allah, in halal yaci za'ah tambaye shi, in haram ne za'ah yi masa azaba akai, Bai san karshen Hisabin me zai kasance ba.

3. JARABAWA TA UKU: Kullum yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira k**ar yadda ya damu da duniya. Bai san makomarsa ba, shin Aljanna ce ko wuta.

ITA FA WANNAN DUNIYA KWANA UKU CE KACAL (3)

1. JIYA (2) YAU DA KUMA (3) GOBE.

1. JIYA: Mun ganta ba zata dawo ba.

2. YAU: Muna cikinta ba zata dauwama ba zata wuce.

3. GOBE: Ba mu san ina zamu kasance ba.

Gaskiya babu abun da zai amfane ka/ki sai sallar Ka/ki da kuma kyawawan ayyukan mu na alkhairi.

Ka kyautatawa kowa, ka zauna da kowa lafiya, ka yawaita afuwa da sadaka domin ni da kai dasu duk matafiya ne.

Allah yasa muyi tafiya ta alkhairi da dacewa.dun Allah kayi share dun Yan uwa su anfana

Àllah kajikan mlm.

DUNIYAR ALJANNU      KASHI NA FARKO BABI NA BIYUkuyi following din mu domin samu update na sabbin bugu na labaraiDa mai ...
22/07/2024

DUNIYAR ALJANNU
KASHI NA FARKO BABI NA BIYU
kuyi following din mu domin samu update na sabbin bugu na labarai
Da mai bukata ana tura audio amma biya akeyi gaskiya
A cikin wannan gonar suke shiga su shawara yadda zasu shiga gonan mai gari
Kwasan shawara ta fadoma manu sarkin wayo cewa kai muyi gina daga gonar mu zuwa gonar mai gari mubi tanan mu shiga sai ko kowa yayyi amanna s**a yadda aka ko fara aiki babu yini babu dare koda s**a fara aiki saura kwana bakwai ayi ta6in gonar, acan gefe daya ko mai gari ya matsu lokaci baiyi ba domin yasan makircin yaran nan komi suna iyawa domin su cimma gurin su
A can gefe daya ko wayannan yara su dukufa babu dare babu rana kullum aiki s**ai cikin gari sai da aka azako sun bar gari domin anbar ganin su
Suna nan suna aiki kullum koda s**ai kai gonar bai gari da maracce safiya dai ake jiran ta waye aje ayi girbin gona a ta6e ta, masu gadi nacan suna gadin bakin gini, suko s**a shigo cikin gona s**ayi mata ayya ayya s**a kwashe komi s**a waske
Washe gari tunda subahin gari baima gama waye ba mai gari yasaka masu yi masa aiki suje suyi masa aikin wannan gonar
Koda s**aje ciyawa kawai s**a tarar anwa gona ayya ayya komi an kwashe sai ciyawa dai aka bari
S**a dawo s**a gayama mai gari, mai gari yacce karya ne muje in gani s**aje yaggani da idon sa komi babu ciyawa
Follow us https://www.facebook.com/profile.php?id=100070768062324
Kuyi search din
Daddy Ahmad ibn taimiyya

DUNIYAR ALJANNU KASHI NA FARKO            BABI NA DAYADaga bakin marubucin wannan labariDaddy Ahmad ibn taimiyyaIdan kun...
21/07/2024

DUNIYAR ALJANNU KASHI NA FARKO
BABI NA DAYA
Daga bakin marubucin wannan labari
Daddy Ahmad ibn taimiyya
Idan kuna bukatar audio na wannan labari zaku iya tuntubar mu domin mu tura muku shi
A wani gari da ake cema Daryon ganye anyi wasu matasa su ukku da ake cema manu mai wayo da da bala baka da dibara da basi dirtau ma'ana yafi kowa danbala
Suna zaune a garin su basuda abinda zasuyi kullum sai zaman banza basu wannan bishiya basu wannan gona kullum cikin jawo magana suke kullum anan gaban mai gari wurin kai karar su, babu sana'a babu aikin gona asalima idan kayyi aiki su kayyi ma domin zasu bi dare su kwashe amfanin noman ka,S**a ishe kowa agari,Kwasan wani lokaci mai gari yasa akayi masa aikin rani aka saka masa tumatur tumatur din yayi kyau yayi ja daga nesa abin ban sha'awa
Ashe wannan tumatur din ya tsonema mutanen nan ido🙄 suna nan suna jiran lokaci yayi subi dare su kwashe shi
Shi ko mai gari da yassan halin wayannan yara sai yasa aka gewaye masa gonar sannan aka saka yan banga kowane da karen sa da kayen gadinsa miyagu kayan da kai kasan idan mutum yashiga wannan gona yasan ya kira ma kansa ruwa
A can gefe daya ko mutan gari kowa ya wannan lokaci ba'a ta6a gonar sa ba kowa mamaki dai yakai ana fadin ai su manu sarkin wayo sunyi hankali wannan karo basu ta6a gonar kowa ba
Jama'a basu san wannan karo babban kamu akeson ayi domin gonar mai gari ake hari
Tau wannan lamari na yan banga ya shama yaran nan kai kowan su tunani dai yakai yaza'ayi kuma sun sha alwashi cewa basu ta6a gonar kowa wannan lokaci sai gonar mai gari, amma kuma abin yaci tira basu san yadda zasuyi ba
Akwai wata gona ta mangwaro wanda mai gonar yabarma yaran dan dolensa badan Allah ba akan sun addabesa, shi dakan sa yakira su yace kai wannan gonar na bar muku ita kuje kuyi duk abinda zakuyi nabaku akaje wurin mai gari aka sheda mai akayi sanarwa kowa yaji babu mai shiga wannan gonar sai su
To gonar tana kusa kusa da gonar mai gari nisan su yakai mita 2 da rabi
Babi na 2 next

Assalamu alaikum jama'aA wannan page muna da manufofi masu yawa da zamu fara zantardasu a wannan page in aha Allah nan b...
17/07/2024

Assalamu alaikum jama'a
A wannan page muna da manufofi masu yawa da zamu fara zantardasu a wannan page in aha Allah nan bada jimawa bah,
Daga cikin manufofinmu sune k**ar haka.q zamu kasan muna dora karance karance na malam mai masu albarka duk malami mai fadin gaskiya wurin karantarwassa zamu yi kokari in sha Allah mudora karatunsa
2 zamu fara baku labari na novels domin jindadin ku
Sannan nan bada jimawa ba zamu fara baku wani kayatacce labari namu da muka rubuta mai suna
DUNIYAR ALJANNU
Wanda zamu dora baku shi duk ranar monday da friday in sha Allah
Sannan ko bayan haka Muna da audio na wannan labri mai so zai iya tuntubarmu sai mu gaya nasa procedure yadda abin yake
Duniyar aljannu ku saurare nan zuwa Friday in sha Allah.ko bayan shi muna dasu da yawa

Highlighted

18/04/2024

BABBAN TASHIN HANKALI!!!

Hadisi ne zan karanta muku Amma ina neman alfarma guda awajenku kafin ku karanta Hadisin nan... Alfarmar da nake nema awajenku ita ce, ku tsayar da duk abinda kukeyi, ku nutsu ku karantashi da kyau.

Domin na tabbata sai ya girgiza zuciyar duk wani mai Imani.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.
Tsira da aminci su tabbata bisa Annabin Karshe, da dukkan Iyalansa da Sahabbai baki daya.

Yazeedur Raqqaashiy ya karbo Hadisin daga Anas bn Malik (R.A) yana cewa:
Watarana Mala'ika Jibreelu (A.S) yazo wajen Manzon Allah (S.A.W) awani lokacin da bai saba zuwa masa ba.

Yazo, gaba dayan launin fuskarsa
ya canza. Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "MAI YASA NAGA LAUNIN FUSKARKA DUK YA CANJA HAKA?".
Yace "Ya Muhammadu (S.A.W) nazo maka ne awannan lokacin da Allah yayi Umurni da Masu hura wuta suci gaba da Hura ta.

Duk wanda yasan cewa Jahannama gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Azabar Kabari gaskiya ce, kuma Azabar Allah ita ce mafi girma, to bai k**ata yayi wani farin ciki ba har sai ya tabbatar da cewa ya samu tsira daga wannan".

Sai Manzon Allah (S.A.W) yace masa "YA JUBREELU INA SO KA SIFFANTA MUN YADDA JAHANNAMA TAKE".

Sai yace "Na'am. Hakika Allah madau kakin Sarki yayin da ya halicci Jahannama, yasa an hurata tsawon Shekaru DUBU. Har sai da ta zama JA -JAWUR.

Sannan aka sake hurata tsawon Shekaru DUBU har sai da ta zama FARI - FAT!!
Sannan aka sake hurata tsawon shekaru DUBU har sai da ta zama BAKA - KIRIN!!!.
Tana nan har yanzu BAKA KIRIN ce, mai
tsananin duhu ce.Harshen Balbalinta basu mutuwa ballantana Garwashinta.

Na rantse da Girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a bude misalin kofar allura daga wutar Jahannama, Wallahi sai dukkan Ma'abotan doron duniyar nan sun kone baki dayansu saboda tsananin zafinta.
Na rantse da girman Ubangijin da ya aikoka da gaskiya, da ace za'a ratayo tufafi guda daya tufafin 'Yan Wutar Jahannama a makaloshi atsakanin Sararin Samaniya, da sai Dukkan Ma'abotan doron kasa sun Mutu baki dayansu saboda tsananin

08/04/2024

Domin masu tambaya Ga amsa Nan 👇
*_السلام عليكم ورحمة الله وبركا ته_*
➖➖➖➖➖➖➖➖
*_” بسم الله الرحمن الرحيم_
_*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA DAI SAURAN SU.*_
¤═════۩۞۩═════¤
_Wankan Janaba yana da *siffa guda biyu:*_
::
_*1- Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar),*_
_*2-Akwai kuma wacce ake kira 'siffatu k**al' (ta k**ala).*_
:
_*Wankan Janaba* a siffar sa ta k**ala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne:_
_zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka، a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa)_
_wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan، to daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba,_
:
_to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban,_
_bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka._
:
_To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina. To idan kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro._
_Wannan ita ce siffa ta k**ala a wankan janaba._
_In wankan *janaba* ne haka zakayi, in na *haila* ne haka za

Karfe nawa za a yi sallan idi a garinku??Duk wanda ya san lokacin da za a yi sallah a garin su, sanya mana sunan garin d...
07/04/2024

Karfe nawa za a yi sallan idi a garinku??

Duk wanda ya san lokacin da za a yi sallah a garin su, sanya mana sunan garin da lokaci domin jama'a su amfana.

Babban ni'ima ce Gare ka Wanda Allah yayyi ma Kana shan ruwa daKANKANA da TIARA Wani na can kunu Sai kunuShima ni'ima ce...
03/04/2024

Babban ni'ima ce Gare ka Wanda Allah yayyi ma Kana shan ruwa da
KANKANA da TIARA
Wani na can kunu Sai kunu
Shima ni'ima ce a Gare shi
Domin wani nacan daga ruwa Sai ruwa yake Buda baki
Shima ni'ima ce a Gare shi
Domin akwai Wanda baida lafiyar shan koda ruwan ne
Ashe Ko duk abinda muka ga ALLAH yayi mana lalle ni'ima ce agare mu
RAYUWA abar hankuri ce al'amarin duniya Mai wuce wa ne
Yau ne da gobe wataran Sai labari???
Yau ne da gobe wataran Sai labari???

Shedan baka da dakin kwana
03/04/2024

Shedan baka da dakin kwana

03/04/2024

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Rabi Abdulmumini, Last Borne, Sulaiman Turabu

????????
02/04/2024

????????

Address

Behind Old Prison Malam Mainasara Road
Birnin-Kebbi
TWO

Telephone

+2347066839493

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Daddy Ahmad ibn taimiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Daddy Ahmad ibn taimiyya:

Share

Category