Personal Media

Personal Media Da Allah muka dogara

idan baka sauka ba yau gobe zaka sauka idan baka sauka gobe ba jibi zaka saukadomin rame na can najiran kawatara mune ab...
03/06/2026

idan baka sauka ba yau gobe zaka sauka idan baka sauka gobe ba jibi zaka sauka

domin rame na can najiran ka

watara mune abisa wannan kujera
bi'iznillah

yau ta Allah haka gobe ma tasa ce
Allah shike BADA Mulki ga Wanda yake so

Excellency
31/05/2026

Excellency

11/05/2026

SHAWARA ZUWA GA DUK WANI USTAZI
Da zarar ka tsinci kanka a harkar koyarwa, to ka saka ranka harkar Nan tadan wani lokaci zakiyita Komai gaskiya Aiki ne mai wahala, kuma mai buƙatar haƙuri. Saboda haka tun daga farko ka gyara niyyarka tsakaninka da Allah, ka haɗa aikinka da addu’ar Allah ya karɓa maka. Amma akwai wasu abubuwa da idan ka kula da su, za su taimaka maka sosai a rayuwar malunta.
1. Ka kare mutuncinka a ko da yaushe.
Mutuncin ustazi shi ne babban jarinsa. Da zarar ya zube, komai zai iya lalacewa. Ka yi taka-tsan-tsan a suturarka, hukuncinka, yadda kake zama da tashi, yadda kake magana da ɗalibai, da yadda kake mu’amala da iyaye. Ka rufe kowace ƙofa da za a samu hujja a kanka. Domin wasu iyayen yara ba neman gyara s**a zo ba, suna jiran ƙaramar kafa su samu su ci mutuncin malami. Wasu ma islamiyyar ba damuwarsu ba ce, kawai dai sun haifi yara ne. Saboda irin waɗannan mutane, ka ƙara haƙuri da kamewa.
2. Kada ka ɗora rai a taimakon iyayen ɗalibai. Wani lokacin zuciyar ustazi kan raya masa cewa “wannan ɗalibin ubansa mai kuɗi ne”, ko “wannan iyayen za su taimaka min”. Amma mafi yawan lokaci abin ba haka yake ba. Da ace iyayen ɗalibai suna bai wa malamai abin da ya dace, da yanzu tsofaffin malamai su ne s**a fi kowa walwala. Saboda haka ka yi aikinka saboda Allah, ka jira sakamako daga gare Shi, ba daga hannun mutane ba.
3. Kada ka yi tsananin saka ɗalibi a rai.
Kar ka nuna wa wani ɗalibi soyayya ko kulawa fiye da kima har ka fara jin kamar babu shi makaranta ba za ta tafi ba. Ka so su gaba ɗaya, amma ka san iyaka. Domin yaron da kake taƙama da shi yau, wata matsala kaɗan za ta sa a canja masa makaranta gobe. Wani lokaci ma iyaye kan sauya makaranta saboda ƙaramin hukunci ko rashin jituwa. Saboda haka ka maida hankali wajen yi wa kowa adalci.
4. Ka zama wayayye da sanin matsayinka. Kar ka yaudari kanka saboda kana koyarwa ka ji kamar ka fi kowa sani ko daraja. Ka yi iya abin da za ka iya cikin nutsuwa. Haka kuma ka kula da yawan sakewa da ɗalibai.

27/01/2026

may Allah help us and guide us

24/11/2025

A KOWACE RANA DAN ADAM YANA HADUWA DA JARABAWA GUDA UKU (3)

1. JARABAWA TA FARKO: Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka. Idan kudinsa ya ragu zai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.

2. JARABAWA TA BIYU: Kullum yana cin arzikin Allah, in halal yaci za'ah tambaye shi, in haram ne za'ah yi masa azaba akai, Bai san karshen Hisabin me zai kasance ba.

3. JARABAWA TA UKU: Kullum yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda ya damu da duniya. Bai san makomarsa ba, shin Aljanna ce ko wuta.

ITA FA WANNAN DUNIYA KWANA UKU CE KACAL (3)

1. JIYA (2) YAU DA KUMA (3) GOBE.

1. JIYA: Mun ganta ba zata dawo ba.

2. YAU: Muna cikinta ba zata dauwama ba zata wuce.

3. GOBE: Ba mu san ina zamu kasance ba.

Gaskiya babu abun da zai amfane ka/ki sai sallar Ka/ki da kuma kyawawan ayyukan mu na alkhairi.

Ka kyautatawa kowa, ka zauna da kowa lafiya, ka yawaita afuwa da sadaka domin ni da kai dasu duk matafiya ne.

Allah yasa muyi tafiya ta alkhairi da dacewa.dun Allah kayi share dun Yan uwa su anfana

24/11/2025

Wani aiki Sai Dan Adam
Yana Dan shekara 25 yayi soyayya da yar shekara 15 cikin rashin sa'a yayi Mata ciki
Ya gudu yabar gida akwana a tashi ta haihu
Ita bata son tayi abin kunya Sai ta doki diya ta'aje wani wuri
Hizba s**a gani s**a Kai gidan marayu
Bayan shekara Sha ukku Sai GA naka yadawo
Sai Allah yasa yasamu aiki gidan marayu din Yana karantar dasu
Cikin rashin sa'a Sai tsoho ya hadu da diyar sa baima San Itace bah
Abinka da fasiki
Sai yadora bibiyar diyar Nan tashi baisan diyar sace bah
Haka yasamu sa'ar ta, itama yayyi Mata ciki cikin rashin sa'a
Yarinyar ta doki ciki
Ashe tun lokacin da uwar Yarinyar ta ajeta Tana labe Tana kallon Wazai do diyar,
Haka ta dora bin Al amurran Yarinyar Nan Har ta girma duk tasan komi nata
Yanzu Dai Yarinyar tado ciki Kuma kowa yasa ni
Uwar ta Sani yansanda sun Sani
Aka matse Yarinyar wa yayyi miki ciki tace malamin su
Mamar Tana Nan kusa Har gidan marayu sun saba da ita
Yan sanda s**a kamo baban
Ana zowa dashi Sai mamar ta tambaya wannan ne malamin akace Eh Nan take ta suma
Har yanzu bata farbado bah bale aji yadda zata Kaya
ALLAH yasa mufi karfin zunciyar mu

20/11/2025

14/11/2025

Hukuncin fitsari a zaye

⤵️⤵️⤵️⤵️⤵️

11/11/2025

*✋𝙒𝘼𝙎𝙄𝙔𝙔𝘼𝙍 𝘽𝘼𝙉𝙆𝙒𝘼𝙉𝘼🤚*
_*"Duk Aikin Da Zakayi Kadunka Dauka Shine Aiki Na Karshe Annabi Muh'd ﷺ ; Ya Ce In Allah Na San Mutum Da Alkhairi Sai Ya Shirya Shi Akan Kyakkyawan Aiki Kafin Ya Karbe Shi , Wani Aikin Sa Na Karshe Aduniya Zinah Allah Ya Tsare Mu"*_

Address

Behind Old Prison Malam Mainasara Road
Birnin-Kebbi
TWO

Telephone

+2347066839493

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Personal Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Personal Media:

Share

Category