26/10/2025
Labari me rikitarwa copy dinsa nayo muku
Darasin Rayuwa: Abinda ya Faru da ni.
Suna na Paul, ni mutum ne mai son zumunci. Bayan na kammala bautar ƙasa a Jahar Enugu, munyi waya da wani abokina wanda muka gama karatu tare. Na shaida mashi cewa zan tsaya wurinshi mu gaisa, kafin in karasa zuwa garinmu, tunda motar da zan hau iyakarta Abuja.
Ai kuwa haka akai. Bayan mun taso daga Enugu, kira shi a waya na shaida mashi tasowarmu. Haka muka cigaba da yin waya dashi lokaci zuwa lokaci har Allah ya sa mu ka isa Abuja. Bayan na kira shi, sai yace da ni naya garejin ma yana jirana. Na fada mishi daidai inda nake tsaye, ba da jimawa ba sai gashi gabana. Muka rungume juna sak**akon kewa da murnar andade ba a hadu ba.
Kai tsaye muka hau Taxi zuwa gidansu. Sai dai kuma ba a cikin Abuja ba ne. Irin kauyukan gefen Abuja din nan ne. Dan ni har yanzu ban san sunan wurin ba. Sun dai shirya da drivern kuma mu kadai ya dauka har kofar gidansu.
Munsha hira, mun raba dare muna tuno da muka sha gwagwarmar rayuwar makaranta, labarin bautar ƙasa, labarin ƴanmata dasauransu. Ahaka dai ban san lokacinda Barco ya kwasheni ba. Dama jiki da jini, abinka da wanda ya sha doguwar tafiya.
Gari ya waye bayan mun gaisa da iyayenhi, mun karya sai ya haɗani da ƙanin shi ya ce zai wuce wurin aiki, duk abinda nake bukata, ƙanin ya yi min. Na raka shi ya wuce, sai na dawo muka fara hira da ƙanin har zuwa wani lokaci. Kanin daukeni muka fita zagaya unguwar da suke muka dan yawata, har kai ni wani club muka huta.
Da maraicen ranarda bazan mance ba, abokina ya dawo aiki, munyi wanka mun fita waje. Sai nake bashi labarin yawonda mukayi, sai yake cewa ashe na zagaya gari. Nace mashi sosai kuwa, domin duk inda muka je, zan iya gane wurin. Ya yi dariya, ya ce toh bazai ce komi ba yanzu mu tafi zuwa club in shiga gaba.
Na shiga gaba kuwa har muka isa wurin. Ya ce gaskiya kana da riƙe wuri a zuciyarka. Nan muka bata lokaci har dare ya yi mana sosai. Muka yi shaye shayenmu da raye raye. Abokina ya barni nan tare da wasu mutane wanda ni ban san su ba, kuma jikina bai bani ba. Sai na kira shi a waya ya zo mu wuce. Sai ya ce min yana gida, uzurine ya k**a shi gashinan dawowa. Kawai sai naji ban iya jiranshi nan take. Na ce mashi ya bari kawai zan wuto.
Ya ce dani a'a dare ne, in bari ya dawo mu wuto tare. Abinka da kaddar, kawai sai na k**a hanya ba tare da bata lokaci ba. Ina tafiya ina waige ko wasu sun biyoni. Tsorona dai bai wuce wayata sabuwa da na siya bada jimawa.
Ina cikin tafiya, sai na ji fitsari ya k**a ni. Ko ina ya yi tsit, shiru kawai kake ji. Daga iskar damina mai kadawa, sai kukan tsuntsaye. Na dan kai zuwa wani fili haka wanda babu itatuwa sosai, ya danyi fili haka a bakin hanya. Na kebe gefe, na zage zip nai fitsari. Ina kammalawa naji tsigar jikina ta tashi, lokaci daya sai tsoro ya k**ani. Sai naji tamkar wani yana tsaye a bayana. Na juya da sauri amma banga kowa ba. Lokaci guda zufa ta karyo min duk da cewar iskar damina na kadawa k**ar za ai ruwa.
Da sauri na k**a tafiya ina addu'a, na matsu inkai gidansu abokina. Ina isa kofargidansu ana kawo wuta, sai nai ajiyar zuciya, naji hankalina ya dawo jikina. Kafin in shiga, sai ga abokina ya fito da niyyar komawa mu taho tare. Ya ce min meyasa ban jira shi ba, ranshi ya baci. Na bashi hakuri, muka shige ciki.
Daren nan banyi bacci ba kuwa. Tsigar jikina kawai ke tsahi, jikna kuma sai ya k**a rawa. Da zarar na rufe ido, sai in janni na koma wajen da nayi fitsarin nan, sai in maza in bude. Haka dai na ciro wayata nata dannawa har sai da gari ya fara waye sannan bacci ya daukeni. Sak**akon banyi bacci da wuri ba, abokina har ya wuce wurin aiki ban tashi ba. Ko da na tashi ya tafi aiki, kuma da ni ranar na so in wuce garinmu domin kusan shekara daya kena banga mahaifiyata ba. Ita ma ta matsu ta ganni. Na kira shi a waya yace dole sai na sake kwana, tunda shi bai san zan wuce yau ba. Haka dai na yanke wayar, nai zaune ina nazarin abinda ya faru da ni a daren jiya.
Bayan na karya ne sai wata zuciya ta ce min in koma wurin da nai fitsarin nan. Haka kuwa akai. Na fito na k**a hanya, ina nazartar wuraren ahankali. Sai gashi na isa wurin filin. Fili ne matsakaici haka, irin k**ar na sabuwar unguwa wanda ba a gina ba. Na ci gaba da matsawa, koda na zo dai dai inda na kebe nai fitsari, sai gabana ya fadi. Domin abinda nagani ya razanani sosai. Nan take naji kafafuna k**ar baza su iya daukata ba. Jikina yai nauyi, miyon bakina yana neman ƙafewa, juwa kuma na neman daukata.
Inda nai fitsarin ashe akan kabari ne, tashin hankali wanda ba a sa maka rana!
Mu hadu a Part 2 a comment section idan kuna so mu cigaba.