Radio Nigeria Equity FM Kebbi

Radio Nigeria Equity FM Kebbi Educate, inform and enlighten the public.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo d...
20/08/2026

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur a Najeriya idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wani zaman Facebook Live, inda yake amsa tambayoyi kan cire tallafin man fetur da kuma tasirin matakin ga al’ummar ƙasar.

Ya ce da farko bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma daga baya ya sauya matsayinsa, yana mai tambayar yadda aka yi amfani da kuɗin da aka samu sakamakon cire tallafin.

Ya ce: “Da farko ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba. Amma yanzu da aka cire shi, ina kuɗin yake? Ina aka kashe kuɗin tallafin? Shin an yi amfani da shi wajen inganta kiwon lafiya, ilimi ko tsaro?”

Atiku ya ƙara da cewa, “Idan na lashe zaɓen shugaban ƙasa, zan dawo da tallafin man fetur. Kuma duk wanda ya sace kuɗaɗen tallafin Najeriya, dole ne ya dawo da su.”

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar 29 ga Mayu, 2023, a lokacin rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.

Matakin ya haifar da ƙarin farashin man fetur, wanda kuma ya jawo tashin farashin sufuri, abinci da sauran kayayyaki da ayyuka.

Shugaba Tinubu ya kare matakin, yana mai cewa tallafin ya yi tsada sosai ga ƙasar, kuma gwamnati ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyinsa ba.

20/08/2026

Shugaba Tinubu ya nada Abel Enitan a matsayin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Mista Abel Olumuyiwa Enitan a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Wata sanarwa da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, ta ce nadin zai fara aiki daga ranar 27 ga watan Agustan 2026.

Enitan, wanda ya fito daga Jihar Osun, zai maye gurbin Madam Didi Esther Walson-Jack, wadda za ta yi ritaya daga aikin gwamnati bayan ta kai shekarun ritaya na doka, wato 60.

A halin yanzu, Mista Enitan shi ne Babban Sakatare na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, kuma shi ne mafi dadewa a cikin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Ya shafe shekaru bakwai da watanni bakwai yana rike da mukamin Babban Sakatare, inda ya yi aiki a Ma’aikatar Harkokin ’Yan Sanda, Ma’aikatar Jin Kai da Agaji, da kuma Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

Sanarwar ta ce Shugaba Tinubu ya bukaci sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya da ya karfafa sauye-sauyen da ake gudanarwa, ya zurfafa kwarewa da ingancin aiki, tare da gina ma’aikatan gwamnati masu nagarta da saurin amsa bukatun al’umma.

Shugaba Tinubu ya kuma nuna godiyarsa ga Madam Walson-Jack bisa irin hidimar da ta yi wa ƙasa, musamman gudunmawarta wajen kawo sauye-sauye da sabbin dabaru a ma’aikatan gwamnati.

An haifi Mista Abel Enitan ne a ranar 12 ga Disamba, 1966. Ya yi karatun sakandare a Ajibode Grammar School da ke Ibadan da kuma College of Arts and Science da ke Ile-Ife.

Daga bisani ya halarci Jami’ar Legas, inda ya kammala karatun digiri a fannin Finance and Banking a shekarar 1988. A shekarar 2015 kuma ya samu digiri na biyu a fannin Public Policy Analysis daga Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Lafia.

20/08/2026
Gwamna Nasir Idris Ya Ƙirƙiri Ofisoshin Mataimakan Gwamna Kan Magungunan GargajiyaGwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris...
20/08/2026

Gwamna Nasir Idris Ya Ƙirƙiri Ofisoshin Mataimakan Gwamna Kan Magungunan Gargajiya

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya amince da ƙirƙirar ofisoshin Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Magungunan Gargajiya a masarautun Gwandu, Argungu, Yauri da Zuru.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar Ƙungiyar Masu Sana’ar Magungunan Gargajiya ta Najeriya, reshen Jihar Kebbi, a fadan Gwamnati.

Gwamna Nasir Idris ya umarci shugaban ƙungiyar da ya gabatar da sunayen mambobi huɗu da za su riƙe waɗannan mukamai.

Ya kuma umarci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya samar wa ƙungiyar ofishin sakatariya da gonar da za a shuka tsirran da ake amfani da su wajen sarrafa magungunan gargajiya.

Gwamnan ya ƙara amincewa da shirya tarukan horaswa ga mambobin ƙungiyar domin inganta iliminsu kan hanyoyin zamani na sarrafa magungunan gargajiya da na tsirrai, tare da samar da motocin aiki guda biyu.

Dakta Nasir Idris ya gode wa mambobin ƙungiyar bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatinsa.

Tun da farko, shugaban ƙungiyar, Rilwanu Muhammad Wasagu, ya ce sun kai ziyarar ne domin sake tabbatar da amincinsu da goyon bayansu ga gwamnatin Gwamna Nasir Idris.

Ya yaba wa gwamnatin bisa ayyukan raya ƙasa da take aiwatarwa a fannoni daban-daban, da s**a haɗa da lafiya, tituna, ilimi, noma, tsaro da shirye-shiryen tallafa wa al’umma.

Ƙungiyar ta kuma nemi gwamnatin ta samar mata da fili domin noman tsirran magunguna, sakatariya, shirya tarukan horaswa, da kuma ƙirƙirar ofishin Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Magungunan Gargajiya.

A wani labarin kuma, tawagar kungiyar, masu sana'an hannu, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na jihar, Malami Ado, ta kai wa Gwamnan ziyarar nuna goyon baya.

Gwamna Nasir Idris ya nuna godiya kan ziyarar da kuma goyon bayan, yana mai jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da kyakkyawan yanayi da zai ba ’yan kasuwa damar gudanar da harkokinsu cikin sauƙi.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.07 domin bunkasa harkokin ilimin manyan makarantu a jih...
18/08/2026

Gwamnatin Jihar Kebbi ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.07 domin bunkasa harkokin ilimin manyan makarantu a jihar.

Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Kebbi, Isah Abubakar Tunga, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema 𝙻𝚊𝚋𝚊𝚛𝚝𝚎 𝚊, 𝚘𝚏𝚒𝚜𝚑𝚒𝚗 𝚜𝚊, inda ya yi bayani kan sabbin matakan da gwamnatin jihar ke dauka wajen inganta fannin ilimi.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir Idris ya amince da sayen tare da rabawa manyan makarantu mallakar jihar motocin Coaster guda bakwai, mai kujeru 32 kuma dauke da na’urar sanyaya iska, kan kudi Naira biliyan daya da miliyan 750.

Makarantun da s**a amfana da motocin sun hada da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodiyo, Aliero; Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie, Argungu; Kwalejin Kimiyyar Jinya ta Jihar Kebbi, Birnin Kebbi; Kwalejin Jinya da Ungozoma ta Kauran Gwandu, Ambursa; Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha, Jega; Kwalejin Fasaha ta Jihar Kebbi, Dakingari; da Kwalejin Manyan Karatu da Nazarin Shari’a, Yauri.

Ya ce Gwamna Nasir Idris ya kuma amince da sakin sama da Naira miliyan 172 domin biyan alawus-alawus na kayan aikin koyarwa na ma’aikatan ilimi, wato CATA, da kuma na ma’aikatan da ba malamai ba, wato CONTTA, karkashin tsarin albashin kungiyoyin ASUU, SSANU, NASU da NAAT na Jami’ar Abdullahi Fodiyo da ke Aliero.

Kwamishinan ya kara da cewa an shigar da tsarin albashin CATA da CONTTA cikin tallafin wata-wata da jami’ar ke samu daga gwamnati, wanda zai ci wa gwamnatin jihar sama da Naira biliyan 2.065 a duk shekara.

Ya ce an kuma amince da sakin sama da Naira miliyan 151.5 domin biyan bashin karin albashin shekara-shekara da ya rataya a wuyan ma’aikatan Jami’ar Abdullahi Fodiyo.

A cewarsa, wadannan kudade da sauran amincewar da gwamnatin jihar ta yi sun kai jimillar kudaden da aka ware wa Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi a watan Agustan 2026 zuwa sama da Naira biliyan 2.073.

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa Gwamna Nasir Idris ya amince da nada Dr. Zayyanu Umar a matsayin Shugaban Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie da ke Argungu.

Ya ce wadannan matakai na nuna yadda gwamnatin jihar Kebbi ke kokarin bunkasa ilimin manyan makarantu da kuma samar da yanayin da zai taimaka wajen kai cibiyoyin ilimi na jihar matsayin da ya dace da tsarin duniya.

Cikakken Shirin zai zo da mislin karfe 6:30 na yammacin Laraba 19/08/2026Dafatan zaku Kasance tare damu.  fm
18/08/2026

Cikakken Shirin zai zo da mislin karfe 6:30 na yammacin Laraba 19/08/2026

Dafatan zaku Kasance tare damu.

fm

17/08/2026

Shugaban matasan jamiyyar ADC Hon. Muhammad Al'Amin yayi fashin baki game da Zaben jihar Osun da Shirin hadin giwar Jamiyyar ADC da sauran jamiyyu G100.

FM ayi sauraro lapia 👇

Gwamna Nasir Idris Ya Sake Jaddada Goyon Bayansa Ga Ayyukan Addini a KebbiGwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya sak...
16/08/2026

Gwamna Nasir Idris Ya Sake Jaddada Goyon Bayansa Ga Ayyukan Addini a Kebbi

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa harkokin addini a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi dubban mambobin TIGMEN a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi.

Gwamna Nasir Idris ya gode wa kungiyar bisa goyon baya da addu’o’in da take yi wa gwamnatinsa, da kuma zuwansu gidan gwamnati domin nuna goyon baya da hadin kai.

Ya kuma bukaci kungiyar da ta ci gaba da yin addu’a domin zaman lafiya a Jihar Kebbi da kasa baki daya.

Tun da farko, shugaban kungiyar, Dakta Nazifi Inyas Gwadangaji, ya ce sun zo gidan gwamnati ne domin sake tabbatar da biyayyarsu ga gwamnatin da ake ciki, bayan gudanar da tattaki domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

Dakta Nazifi ya bayyana cewa an kafa kungiyar ne domin wayar da kan jama’a da kuma ilmantar da su kan hakkokinsu, 'yancin su da kuma nauyin da ya rataya a wuyansu na kasa.

Ya nuna godiya ga Gwamna Nasir Idris bisa irin goyon bayan da yake bai wa addini da harkokin addini a fadin jihar, inda ya bukaci gwamnan da ya ci gaba da wannan kokari.

Shi ma Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kebbi kan Harkokin Addini, Faruk Umar Ambursa, ya ce tawagar ta kunshi shugabannin da ke wakiltar mambobin kungiyar daga kananan hukumomi 21 na jihar.

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya zabi Alhaji Ibrahim Muhammad Augie a matsayin mataimakinsa a zaben gwamnan ji...
16/08/2026

Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya zabi Alhaji Ibrahim Muhammad Augie a matsayin mataimakinsa a zaben gwamnan jihar na shekarar 2027.

Alhaji Ibrahim Muhammad Augie zai maye gurbin Mataimakin Gwamnan jihar mai ci, Sanata Umar Abubakar Tafida Arugungu.

An bayyana hakan ne a ranar Lahadi aBirnin Kebbi, yayin wata ziyara ta godiya da wasu masu ruwa da tsaki daga Masarautar Argungu s**a kai wa Gwamna Nasir Idris.

Sakataren Shirya Ayyuka na Jam’iyyar APC na Kasa, Alhaji Suleiman Muhammad Argungu, ya ce an dauki matakin sauya mataimakin gwamnan ne bisa shawarar kwararrun lauyoyi dangane da cancantar mataimakin gwamnan mai ci.

Ya ce, saboda haka, an zabi Alhaji Ibrahim Muhammad Augie a matsayin sabon abokin takarar Gwamna Nasir Idris a zaben shekarar 2027.

Alhaji Suleiman Argungu ya jaddada cewa an dauki matakin ne bisa fahimta da amincewar Sanata Umar Abubakar Tafida, yana mai cewa babu wata rashin jituwa tsakanin gwamna da mataimakinsa.

Ya yi kira ga ‘yan siyasa, ‘yan jam’iyya da magoya bayan APC a fadin jihar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da yin aiki domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaben shekarar 2027.

A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris ya gode wa al’ummar Masarautar Argungu bisa ci gaba da ba gwamnatinsa goyon baya da hadin kai.

Gwamnan ya sake jaddada cewa babu wata rashin jituwa tsakaninsa da Mataimakin Gwamna Sanata Umar Abubakar Tafida, yana mai bayyana cewa sauyin ya samo asali ne daga wasu dalilai na shari’a.

Ya kuma bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, musamman a yankunan Masarautar Argungu, tare da neman ci gaba da samun goyon baya da addu’o’in al’umma domin samun nasarar ayyukan gwamnati.

Address

Kalgo Road, Opposite NTA
Birnin-Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Radio Nigeria Equity FM Kebbi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share