JAHAR KEBBI A YAU

JAHAR KEBBI A YAU A page dedicated for news update in kebbi state and Nigeria at large

02/02/2026

“Ina kira ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Kauran Gwandu, da ya tsayar mana da Hon. Shehu Na Tsoffi, Jarman Shanga, a matsayin ɗan takarar kujerar ɗan majalisa ko kuma shugabancin ƙaramar hukumar Shanga.”
Inji Ibrahim Muhammad Tfana. Malikiyya Tfana

02/02/2026

Sakon Gwamnan jahar kebbi zuwa ga 'yan siyasar jahar.

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar, ta hany...
28/01/2026

Gwamnatin Jihar Kebbi ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar, ta hanyar karfafa tsaro a matakin al’umma.

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dakta Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya bayyana hakan yayin da yake duba jami’an sa-kai da mafarauta 500 da s**a kammala horaswar sabunta kwarewa da dabarun yaki a sansanin horaswa da ke Kalgo, karamar hukumar Kalgo.

An shirya horaswar ne domin su rika taimakawa hukumomin tsaro na gwamnati wajen fuskantar kalubalen tsaro a Jihar Kebbi.

Da yake jawabi a wurin, Gwamna Nasir Idris ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa nasarar shirin, inda ya bayyana horaswar a matsayin mataki da aka dade ana jira domin bai wa jami’an tsaro na al’umma sabbin dabaru na zamani.

“Allah ne yasa na zama Gwamna, Kano ce a kan gaba, ba biyayya ga mutum ba” Inji Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.Gwamna Yus...
25/01/2026

“Allah ne yasa na zama Gwamna, Kano ce a kan gaba, ba biyayya ga mutum ba” Inji Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake rabon babura ga hadimansa masu kula da shafukan sa na kafafen sada zumunta, a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce dangane da rahotannin da ke yawo cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

“A shekara ta 2023, Allah ne Ya bani mulki, ba wani mutum ba, kuma har yanzu ina gode Masa tare da yabonsa, domin Shi kaɗai ne zai ba ni damar ci gaba da jagoranci a shekarar 2027,” in ji gwamnan.

Shin Abba ya fadi gaskiya ko kuma Yayi butulci.

Ku bayyana mana Ra'ayoyinku a comment section.

Tsohon Ministan shari’a kuma babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke cewa an gano maka...
23/01/2026

Tsohon Ministan shari’a kuma babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya musanta rahotannin da ke cewa an gano makamai a wasu gidaje da ake zargin mallakinsa ne.

A cikin wata sanarwa da hadiminsa kan yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar a ranar Laraba, Malami ya ce labaran ba gaskiya ba ne.

Ya ce babu wata hukuma da ta sanar da shi, iyalansa ko lauyoyinsa cewa an samu makamai a gidansa.

Sanarwar ta zargi wasu kafafen yaɗa labarai da yaɗa jita-jita ba tare da yin bincike na gaskiya ba.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf  ya raba gari da jam’iyyar NNPP ta uban gidansa Kwankwaso.
23/01/2026

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya raba gari da jam’iyyar NNPP ta uban gidansa Kwankwaso.

DA DUMI DUMI: Sa’o’i kaɗan bayan sanarwa, fadar shugaban ƙasa ta janye naɗin Dakingari a matsayin jakadan Turkiyya.Fadar...
23/01/2026

DA DUMI DUMI: Sa’o’i kaɗan bayan sanarwa, fadar shugaban ƙasa ta janye naɗin Dakingari a matsayin jakadan Turkiyya.

Fadar shugaban ƙasa ta janye naɗin Usman Dakingari, tsohon gwamnan jihar Kebbi, a matsayin jakadan Najeriya zuwa ƙasar Turkiyya, kasa da awanni 24 bayan sanar da jerin naɗaɗɗun jakadu.

Bayo Onanuga, kakakin shugaban ƙasa, ya fitar da wata sanarwa a daren jiya Alhamis inda ya tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin jakadu huɗu kacal daga cikin sama da mutum 60 da Majalisar Dattawa ta tantance tare da amincewa da su a watan Disambar da ya gabata.

SOURCE: The cable.

Address

Ahmadu Bello Way Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JAHAR KEBBI A YAU posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share