B.G.N hausa news

B.G.N hausa news We'll come to .BG.N hausa news
Mun bude wannan pagene saboda yada labari a Nigeria da sauran kasashe

21/02/2023

Ina gaisuwa

Send a message to learn more

18/02/2023

Shugabannin kasashen Afirka a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, za su soma taron kolin kungiyar tarayyar Afrika AU, domin tattauna batutuwan da s**a jibanci tashe-tashen hankula a yankin Sahel da…

B.G.N hausa news yana nan tareda ku Dan kawo muku labarai masu inganci
18/02/2023

B.G.N hausa news yana nan tareda ku Dan kawo muku labarai masu inganci

18/02/2023

Alhamdulillah ala kulli halin

18/02/2023

Shugaba Buhari ya ja kunnen masu 'yaɗa jita-jitar' kafa gwamnatin riƙon kwarya a Najeriya
https://bbc.in/3S761dO

17/02/2023
17/02/2023
17/02/2023
16/02/2023
16/02/2023

Amurka ta nanata cewa babu wani dan takara da ke samun goyon bayanta a Najeriya, inda ta bukaci tabbatar da ganin an gudanar da zabukan kasar masu karatowa cikin nasara.

16/02/2023
16/02/2023
16/02/2023

Kotu a Kano ta sake tura Murja Ibrahim Kunya gida yari, bayan sake zaman ci gaba da shari'ar da ake mata.

16/02/2023

An ceto matashiya a ɓuraguzai bayan kwana 10 da girgizar ƙasa a Turkiyya
Ƙarin bayani - https://bbc.in/3k0NaVd

Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki sakamakon canjin ƙudi.
16/02/2023

Shugaba Buhari ya bai wa 'yan Najeriya haƙuri kan halin da ake ciki sakamakon canjin ƙudi.

YANZÚ-YANZÚ: Kotú ta saké tura Múrja Kúnya Da Réal Idris Mai Wushirya, Aminu BBC Da Sadiq Mai Waƙar A Daidai Ta Nàn Zúwa...
16/02/2023

YANZÚ-YANZÚ: Kotú ta saké tura Múrja Kúnya Da Réal Idris Mai Wushirya, Aminu BBC Da Sadiq Mai Waƙar A Daidai Ta Nàn Zúwa Gídan Yari

Kotu ta sake aike wa da fitacciyar mai amfani da dandalin TikTok ɗin nan Murja Ibrahim Kunya da ƙarin wasu mutum uku zuwa gidan yari.

Mutanen sun haɗa da Babban abokin Murjan wato Ashir Idris da aka fi sani da Mai Wushirya sai kuma Aminu BBC da Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi waƙar nan mai taken "A daidai ta nan".

Zauren Malaman Kano ne ya yi ƙarar matasan bisa zargin wallafa bidiyoyin baɗala a dandalin TikTok.

Ana tuhumar Murja da Real Ashir Idris da yin bidiyon batsa a TikTok, inda ya amsa laifinsa yayin da ita kuma ta musanta.

An kuma tuhumi Aminu BBC da yin bidiyon batsa a dandalin TikTok wanda ya musanta.

Sai kuma Sadiq Shehu Shariff mai waƙar "A daidai ta nan" wanda aka zarga da yin waƙar batsa zargin da ya musanta.

A nan ne lauyoyinsu s**a nemi a basu belinsu, sai dai lauyan Gwamnati ya yi s**a, inda ya nemi a basu mako guda domin su yi martani.

Kotun ta tura su zuwa gidan yari har zuwa 23 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Dangane da tuhumar da aka soma yiwa Murja a zaman da ya gabata kuwa, Murja ta rubuto takardar cewa ta tuba, inda Kotun ta ce za ta yi nazari a zama na gaba.

- Freedom Radio

Tsohuwar Takardar Kuɗi Ta Naira 200 Ce Kaɗai Za A Cigaba Da Amfani Da Ita Na Tsawon Watanni Biyu, Cewar Shugaba Buhari“D...
16/02/2023

Tsohuwar Takardar Kuɗi Ta Naira 200 Ce Kaɗai Za A Cigaba Da Amfani Da Ita Na Tsawon Watanni Biyu, Cewar Shugaba Buhari

“Don ƙara sauƙaƙa wa ƴan ƙasarmu matsaloli da suke fuskanta wajen samun kuɗi, na bai wa CBN umarni da cewa a sake fitar da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 kuma a bar su su riƙa yawo a hannun mutane da sabbin takardun kuɗi na 200, 500 da kuma 1,000 na tsawon kwanaki 60, daga ranar 10 ga watan Fabarairun 2023 zuwa 10 ga Afrilu, lokacin da tsohuwar takardar kudi ta N200 za ta daina aiki.” Inji shugaba Buhari

16/02/2023

Assalamualaikum barkada Rana fatan zaku bamu hadinkai wajen Gina wannan page

Address

Yerwa
Borno

Telephone

+2348068441588

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when B.G.N hausa news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to B.G.N hausa news:

Share