19/11/2025
*ALJANA*
*CE*
*ko*
*MUTUM*
*BY* *Nusnim*
*Assalamu* *Alaikum* *ina* *mika* *sakon* *gaisuwata* *ga* *dukkan* *yan* *uwana* *musulmai*, *dafatan* *zaku* *kasance* *dani* *acikin* *sabon* *novel* *ɗina* *mai* *suna* *ALJANA* *CE KO* *MUTUM ?* *Wanda* *nida* *kaina* *na ƙir* *ƙira* *labarin* _Allah_ _yabani_ _ikon_ _Isar_ _da_ _sakon_ _dake_ _ciki_.
1⃣
kwance yake saman makeken katifarsa dataji lallausar zanin gado' sai juyi yake ya kasa bacci, tunani yake ina zai sake ganinta? ina zai sake tozali da wannan kyakkyawar fuskar dake hana zuciyarsa sukuni dare da rana? wani irin haske yaziyarci idanuwansa, wanda yayi sanadiyyar saurin runtse idanun don hasken yayi yawa, jiyayi ance bude idanunka mosoyina, gani nazo gareka don insanyaya maka zuciya tareda sanyata nishadi" saurin bude idanunsa yayi s**ayi ido hudu da kyakkyawar fuskarta, yayi saurin tashi zaune cikeda jindad'in ganinta' don Allah kada kisake tafiya kibarni, ina matukar sonki, inason kasancewa tare dake' inason mukasance a inuwa guda (aure)
tace" kayi hakuri mosoyina inasonka, amman banajin zamu iyayin aure yanxu kusa' saboda wasu dalilai' na farko baka sanni ba' baka san koni wacece ba, akwai babban hatsarin dake tattare da arayuwata' banason wani mummunar abu yafaru da rayuwarka' hawaye yaji ya siraro a idanunsa, ya dafe saitin zuciyarsa dake baraxanar faso kirjinsa sbd tsabar sonta dayakeji' wani irin had'arine? wani irin had'arine arayuwarki dazai hana mana mana kasancewa da juna?
jiyayi ance cikin tsawa ina ruwanka da rayuwarta, inaso kafita hanyar wannan yarinya' inba haka ba rayuwarka zata salwanta, ke kuma yau saikin d'and'ani azaban da baki taba sha ba arayuwarki, ba an hanaki zuwa wajan wannan mutumin ba? afusace matar ta fizgo hannunta 6at s**a 6ace'
wani irin zazzafan hawaye ya gangaro a kuncinsa" meyasa zuciyata zatamin haka? meyasa zata fad'a soyayya da wacce ba jinsinmu guda ba? meyasa zata