Mikiya Page

Mikiya Page Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mikiya Page, News & Media Website, Bulangu.

Muna kawo muku sabbin labarai daga Najeriya da ƙasashen waje 🌍, da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa.
👉 Ku biyo mu, ku danna Follow domin kada ku rasa wani sabon labari! 🔔
MIKIYA PAGE — Labari cikin sauri, bayani cikin sauƙi.

Ministan Abuja Nyeson Wike, ya sake kai ziyara  hanyar Apo-Karshi da yake ginawa, inda yace  watan Nuwanba ne za'a kamma...
24/09/2026

Ministan Abuja Nyeson Wike, ya sake kai ziyara hanyar Apo-Karshi da yake ginawa, inda yace watan Nuwanba ne za'a kammala aikin baki daya.

Tun a shekarar 2010 ne aka bada aikin gina wannan hanya amma ba'a tabuka komai ba sai zuwan wannan ministan wanda a cikin shekara biyu zai gama aikin wanda zai taimaka wajen rage cunkoson ababen hawa a waccan hanya ta Nyanya-Maraba.

Allah Sarki Ummi Gayu ta haɗu da ɓata gari...
24/09/2026

Allah Sarki Ummi Gayu ta haɗu da ɓata gari...

Yan Nigeria ya kamata hankalinku ya dawo nana !Domin Najeriya da Amurka Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Ƙarfafa Zuba Ja...
24/09/2026

Yan Nigeria ya kamata hankalinku ya dawo nana !

Domin Najeriya da Amurka Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Ƙarfafa Zuba Jari a Bangaren Ma’adinai

Najeriya da Amurka sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da nufin ƙara zurfafa zuba jarin Amurka a fannin ma’adinai na Najeriya.

Ministan Ma’adinan Ƙasa, Dele Alake, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Alake ya ce an sanya hannu kan yarjejeniyar ne a ranar Laraba a Gidan Jakadancin Najeriya da ke New York, inda shi da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, s**a sanya hannu kan tsarin yarjejeniyar.

A cewar ministan, yarjejeniyar na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu wajen bunƙasa albarkatun ma’adinan Najeriya, waɗanda ya ce ƙimarsu ta kai kusan dala biliyan 700.

Ya ce tsarin yarjejeniyar ya shafi bayanan ƙasa da binciken ma’adinai, bunƙasa da sarrafa ma’adinai, ababen more rayuwa, da kuma haɓaka ƙwarewar fasaha.

Alake ya ce: “Wannan muhimmin mataki ne wajen ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Amurka a kan albarkatun ma’adinanmu, waɗanda ƙimarsu ta kai kusan dala biliyan 700.”

An wallafa wannan rahoto ne kimanin sa’o’i biyu da s**a gabata.

Atiku Ya Sanya Elrufai Cikin Ƴan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Duk Da Cewa Yana Tsare fans
24/09/2026

Atiku Ya Sanya Elrufai Cikin Ƴan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓensa Duk Da Cewa Yana Tsare

fans

"Tabbas kamar yadda kukaji a baya na gama idda, fatana shine Allah ya sa na cinye jarabawar dana shiga.Shi kuma tsohon m...
24/09/2026

"Tabbas kamar yadda kukaji a baya na gama idda, fatana shine Allah ya sa na cinye jarabawar dana shiga.

Shi kuma tsohon mijina ina yimasa fatan alkairi

Inji Meenat Preety

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gana da yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin taron Majalisar Ɗinkin Duni...
24/09/2026

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya gana da yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya dake gudana a birnin New York na Amurka

Muhimman Abubuwan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Gabatar a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Wanda Mataimakinsa Kashim Sh...
24/09/2026

Muhimman Abubuwan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Ya Gabatar a Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, Wanda Mataimakinsa Kashim Shettima Ya Karanta

1. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatar da ƙudurin Najeriya na ci gaba da amfani da diflomasiyya, haɗin gwiwa da dokokin ƙasa da ƙasa, maimakon tilastawa, ware ƙasashe ko amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba.

2. Ya yi kira da a gaggauta gyara Majalisar Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNSC), yana mai cewa tsarin rarraba iko na shekarar 1945 bai dace da yanayin duniya na shekarar 2026 ba.

3. Najeriya ta buƙaci Afirka ta samu aƙalla kujeru biyu na dindindin a Majalisar Tsaro, tare da cikakken haƙƙi da nauyin da ke tattare da kasancewa mamba na dindindin, ciki har da ikon amfani da veto, matuƙar ana ci gaba da amfani da wannan tsarin, da kuma kujeru biyar marasa dindindin.

4. Tinubu ya bayyana shirye-shiryen Najeriya na ƙara taka rawa a harkokin duniya, bisa dogon tarihin ƙasar wajen wanzar da zaman lafiya, sasanci da ayyukan tsaro a Afirka.

5. Ya danganta manufofin harkokin wajen Najeriya da gyare-gyaren tattalin arzikin cikin gida, yana mai jaddada muhimmancin ingantaccen tsarin tafiyar da tattalin arziki, ƙarfafa hukumomi, saka hannun jari da bunƙasa kamfanoni masu zaman kansu.

6. Najeriya ta yi watsi da ra’ayin cewa dole ƙasashe masu tasowa su zaɓi tsakanin ci gaban tattalin arziki da yaƙi da sauyin yanayi. Ta ce ya kamata ƙasashe masu tasowa su samu damar bunƙasa masana’antu, rage talauci da faɗaɗa samar da makamashi ta hanyoyin da s**a dace.

7. Tinubu ya yi kira da a samar da tallafin kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, fasaha da ƙwarewa, bisa adalci da kuma la’akari da nauyin da ya rataya kan kowa.

8. Najeriya ta sake jaddada Energy Transition Plan da burinta na cimma net-zero nan da shekarar 2060, ta hanyar amfani da makamashi mai sabuntawa, tsaftataccen girki, iskar gas a matsayin makamashin miƙa mulki, noma mai la’akari da sauyin yanayi da kuma hanyoyin kare muhalli.

9. Tinubu ya yi kira ga duniya da kada ta bari tsor

Kotu Ta Soke Tikitin Tsohon Minista Pantami Na PDP, Ta Umarci A Yi Sabuwar Zaben Fitar Da Gwani Na Gwamnan GombeKotun Ta...
24/09/2026

Kotu Ta Soke Tikitin Tsohon Minista Pantami Na PDP, Ta Umarci A Yi Sabuwar Zaben Fitar Da Gwani Na Gwamnan Gombe

Kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta soke fitowar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na neman kujerar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen 2027, tare da umartar jam’iyyar da ta gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani.

Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da wannan umarni a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da wani ɗan takarar neman tikitin PDP na gwamnan Gombe, Usman Aliyu Garry, ya shigar. Ya ƙalubalanci tsarin da aka bi wajen fitar da Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.

24/09/2026

dambe daga Mikiya page

DA ƊUMI-ƊUMI: El-Rufa'i Ya Koka Kan Yadda Mutanensa S**a Juya Masa Baya A Mawuyacin Halin Da Yake Ciki YanzuTsohon Gwamn...
24/09/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: El-Rufa'i Ya Koka Kan Yadda Mutanensa S**a Juya Masa Baya A Mawuyacin Halin Da Yake Ciki Yanzu

Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya koka kan yadda wasu daga cikin mutanen da ya taɓa goya wa baya s**a yi shiru tare da juya masa baya a lokacin da yake fuskantar mawuyacin hali.

El-Rufai ya ce a baya ya tsaya wa mutane ba tare da neman yabo, godiya ko ramuwa ba, domin ya yi imanin hakan shi ne daidai, kamar yadda Mikiya page ta ruwaito a saƙonsa na Facebook.

Ya ce abubuwan da ya fuskanta a ƴan watannin nan sun sa ya sake duba wasu daga cikin dangantakarsa, musamman yadda wasu da yake tsammanin za su kasance tare da shi s**a zaɓi yin shiru.

Duk da haka, ya jaddada cewa ba ya nadamar taimaka wa mutane, kuma ba ya neman ɗaukar fansa kan waɗanda s**a kasa tsayawa tare da shi, yana mai barin hukuncin ƙarshe ga Allah.

Address

Bulangu
NIGERIA

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mikiya Page posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mikiya Page:

Shortcuts

Share