Masarautar Bununu

Masarautar Bununu Official Page Of HRH Alh. Jibrin Danlami Hassan, 1st Emir Of Bununu ASTAGFIRULLAH ALLAH

26/05/2026

Preparations for Eidul Adha are underway! 🎊💪🏻

We warmly welcome back His Royal Highness, Alhaji Jibrin Danlami Hassan, Emir of Bununu, as the emirate prepares to celebrate Eidul Adha in unity and joy.

May this blessed occasion bring peace, prosperity, and renewed strength to His Royal Highness, the royal family, and the people of Bununu.
Ibrahim Iliyasu Abubakar Lame Emirate Council, Bauchi State Umar Isa Bununu Babangida Y. Bununu Al Ameen Garba Sani Hussaini Bello Buskuri

MAIMARTABA SARKIN BUNUNU YA KARBI BAKUNCIN SEN. HALLIRU DAUDA JIKA A KAN TA’AZIYYAR RASHIN MATARSA.Maimartaba Sarkin Bun...
23/05/2026

MAIMARTABA SARKIN BUNUNU YA KARBI BAKUNCIN SEN. HALLIRU DAUDA JIKA A KAN TA’AZIYYAR RASHIN MATARSA.

Maimartaba Sarkin Bununu, Alhaji Jibrin Danlami Hassan, ya karbi bakuncin tsohon Sanatan Bauchi ta Tsakiya, Sanata Halliru Dauda Jika (Dokaji Bauchi), wanda ya kai ziyarar ta’aziyya a fadarsa bisa rasuwar matar mai martaba, marigayiya Hajiya Juwairiyya JD Hassan.

A yayin ziyarar, Sanata Jika ya nuna alhininsa mai girma dangane da wannan babban rashi, inda ya jajanta wa mai martaba da kuma daukacin iyalan gidan sarautar. Ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayiya Hajiya Juwairiyya, ya kuma ba mai martaba da iyalan hakurin jure wannan rashi.

Mai martaba Sarkin Bununu ya bayyana jin dadinsa ga wannan ziyara, inda ya gode wa Sanata Jika bisa jajircewa wajen nuna alhini da kuma kasancewa tare da su a wannan lokaci na bakin ciki.

Allah ya jikan Hajiya Juwairiyya, ya kuma sa aljanna ce makomarta.

✍🏻
Bununu Media Crew
23052026

23/05/2026
23/05/2026

KAI TSAYE DAGA fadan maimartaba sarkin bununu, yayin da yakarba bakuncin Federal road safety corps zone 12 headquaters (Bauchi, Borno & Yobe)

Karkashin Jogorancin Zonal Commanding Officer LEYE ADEGBOYEGA, fsi, FISPON, rss Assistant Corps Marshal.

SAKON GODIYA DAGA MASARAUTAR BUNUNU.A lokacin da mutuwa ta ziyarci fadar Maimartaba Sarkin Bununu, Alh. Jibrin Danlami H...
21/05/2026

SAKON GODIYA DAGA MASARAUTAR BUNUNU.

A lokacin da mutuwa ta ziyarci fadar Maimartaba Sarkin Bununu, Alh. Jibrin Danlami Hassan, ta hanyar karbar ran matarsa, Hajiya Juwairiyya JD Hassan, bakin ciki ya lullube masarautar baki daya. Amma a tsakiyar wannan yanayi na jimami, al'ummar Bununu da jihar Bauchi baki daya sun tabbatar da cewa dan adam dan uwan dan adam ne.

Maimartaba Sarkin Bununu ya mika godiyarsa ga mambobin Majalisar Sarakunan Jihar Bauchi bisa ziyarar jaje da s**a kai masa, inda ya bayyana ziyarar a matsayin wata alama ta daukaka zumunci da hadin kan masarautun jihar.

Wannan nuna kauna da kuka yi ya rage mana zafin rashin da muke ji. Mun ga yadda kuka dauki wannan rashi a matsayin naku, kuma hakan ya kara mana karfin gwiwa a cikin wannan lokaci na jarrabawa.

Sarkin ya kara da cewa, babu abin da zai iya saka musu daidai da girman abin da s**a aikata, sai dai addu'ar fatan alkhairi. Ya ce: Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya saka wa kowa da mafificin sakamako, Ya sanya wannan tafiya da kuka yi da lokacin da kuka bayar a matsayin abin da zai yi musu tanadi a ranar sakamako. Allah Ya kara hada kanmu, Ya kuma kare mana iyalai da masoyanmu baki daya.

Rashin Hajiya Juwairiyya JD Hassan babban rashi ne ga masarautar Bununu, amma soyayyar da al'umma s**a nuna ta kasance tamkar sanyin safiya ga zuciyar da take cikin zafi.

Maimartaba Sarkin Bununu, tare da iyalansa da dukkanin majalisarsa, sun bayyana irin matukar godiyarsu ga al'ummar da s**a tsaya dasu kafada da kafada a wannan lokaci na rashin masoyiyar su.

Muna addu'ar Allah Ya jikan marigayiya Hajiya Juwairiyya, Ya kuma ba Maimartaba Sarkin Bununu da dukkanin al'ummar masarautar hakurin jure wannan babban rashi.

✍🏻
Bununu Media Crew
21052026

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.Cikin jimami da mika lamari ga Allah Madaukakin Sarki, muke sanar da kammala addu'o'...
18/05/2026

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.

Cikin jimami da mika lamari ga Allah Madaukakin Sarki, muke sanar da kammala addu'o'in kwanaki uku na marigayiya Hajiya Juwairiyya JD Hassan, matan mai martaba Sarkin Bununu.

An gudanar da wadannan addu'o'in ne a gidan mai martaba dake cikin garin Bauchi, inda aka yi addu'ar Allah ya jikanta da rahama, ya kuma gafarta mata dukkan kurakuranta. Hakika rasuwarta babban rashin gaske ne ga iyalan gidan sarauta da ma dukkanin wadanda s**a santa da kyakkyawar dabi'a.

Muna rokon Allah ya ba iyalanta da dukkan masoyanta hakurin jure wannan rashin, ya kuma sa aljannar Firdausi ta kasance makomarta ta karshe. Amin.

✍🏻
Bununu Media Crew
18052026

17/05/2026

ADDU’AR RASUWA

Ana sanar da dukkanin al'umma cewa za a gudanar da addu’ar cika kwanaki uku (3) na rasuwar Matan Mai Martaba Sarkin Bununu.

Lokaci: Bayan Sallar La’asar
Wuri: Gidan Mai Martaba Sarkin Bununu, Bauchi.

Muna rokon dukkanin ‘yan uwa da abokan arziki da su halarta domin taya mu taya marigayiyar da addu’a.

Allah ya saka da alheri.

SARAKUNAN BAUCHI SUN KAI ZIYARAR TA’AZIYYA WA MAIMARTABA SARKIN BUNUNU BIYO BAYAN RASHIN MATARSA A wani yanayi na nuna a...
17/05/2026

SARAKUNAN BAUCHI SUN KAI ZIYARAR TA’AZIYYA WA MAIMARTABA SARKIN BUNUNU BIYO BAYAN RASHIN MATARSA

A wani yanayi na nuna alhini da juyayi, Maimartaba Sarkin Bununu, Alhaji Jibrin Danlami Hassan, ya karbi bakuncin tawagar wasu daga cikin sarakunan jihar Bauchi, wadanda s**a kawo ziyarar ta’aziyya a fadarsa bisa rasuwar abar kaunarsa, marigayiya Hajiya Juwairiyya JD Hassan.

Ziyarar wadda ta cika da yanayi na jimami, ta samu halartar wasu fitattun sarakunan jahar Bauchi, wadanda s**a hada da Maimartaba Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri; Sarkin Lame; Sarkin Jama’a; da kuma Za’ar Chief DOM.

Da yake jawabi a madadin sauran sarakunan da s**a halarci taron, Maimartaba Sarkin Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, ya bayyana cewa mutuwa gaskiya ce da kowa zai danka kansa gare ta, sannan ya kara da cewa rasuwar Hajiya Juwairiyya babban darasi ne ga kowane musulmi na cewa ranar komawa ga Allah ba ta da ranar fada. Ya kuma jagoranci addu’ar neman rahamar Allah ga rayuwar marigayiyar, inda ya roki Allah Ya kyautata makwancinta, Ya kuma ba iyali hakurin jure wannan babban rashi.

A lokacin da yake jawabi, Maimartaba Sarkin Bununu, Alhaji Jibrin Danlami Hassan, ya nuna jin dadinsa matuka ga wannan kyakkyawar al’ada ta hadin kai da sarakunan s**a nuna. Ya bayyana cewa ziyarar ta su ta ba shi babban kwarin gwiwa da kuma rage radadin zafin rashin da yake ciki.

"Hakan ya nuna cewa muna tare a kowane hali, kuma ina mika godiyata ta musamman ga takwarorina da s**a dauki lokacinsu, s**a bar fadojinsu domin zuwa su jajanta mini a wannan mawuyacin lokaci,"

Taron ya kammala ne da addu’o’i na musamman domin neman Allah Ya kare al’ummar jihar Bauchi da kasa baki daya daga dukkan sharrin da ke tattare da rayuwa, tare da fatan Allah Ya sanya Aljannah Firdausi ta zama makomar marigayiya Hajiya Juwairiyya.

✍🏻
Bununu Media Crew
17052026

16/05/2026

Kai tsaye Daga fadar Mai martaba sarkin bununu.. ya Karbi bakuncin sarakuna jahar Bauchi

Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!!Godiya ta musamman daga Masarautar Bununu. Allah ya sanya alheri a wannan sabuwar mota h...
16/05/2026

Alhmdllh! Alhmdllh!! Alhmdllh!!!

Godiya ta musamman daga Masarautar Bununu. Allah ya sanya alheri a wannan sabuwar mota hillux da Maigirma Gwamna ya bayar. Muna godiya ga Allah bisa wannan karramawa da aka yiwa masarautar.

✍🏻
Bununu Media Crew
16052026

Address

Bununu Emir Palace
Bununu

Telephone

+2349023476427

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masarautar Bununu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Masarautar Bununu:

Share